RANTSUWAR JINI(THE BLOOD VOW) 39

8 0 0
                                    

❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 39*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*THE GIFT*
*NOT EDITED PLEASE*

_____________  Shekara goma kenan daya fara ganinta da yamma, lokacin tana y'ar shekara sha biyar zuwa sha shida. wata ranar laraba sun taso daga makarantar islamiyya itada UMMI. duk da cewa suna da driver dayake kaisu ya d'auko su, to ranar sai akayi rashin sa'a baya jin dad'i.

Umma kuma tayi tayi dasu su zauna a gida suka k'i. HUMAIRA uwar naciya ita ta matsa sai sunje wai batason rasa hadda. so sai UMMA ta basu kud'in keke dasu hau. kasancewar akwai d'an rata tsakanin gidansu da makarantar nasu.

Saidai koda suka tafi, bayan sun tashi HUMAIRA tak'i yarda su hau keke, wai ga yara dayawa na tafiya da k'afa suma yau su tafi, tafiyan zuga yafi dad'i. UMMI kam sarkin son jiki tace atafau bata yarda ba, suje su hau mota.

HUMAIRA tace saidai ta kwana awajen amma ita kam da k'afa zata tafi. saidai suna kan tafiya sai ji tayi UMMI tana taran motoci wai su taimaka musu da lift.

HUMAIRA taja ta tsaya tana mamakin abinda UMMIN keyi. taja hannunta tana fad'in ke bakida hankali ne? waya fad'a miki ana tare mota haka kawai a hanya, kika sani ko y'an yankan kai ne?

Ummi ta fincike hannunta cikeda masifa tana fad'in to sai me? ay komai ya faru damu ke kika jawo, an bamu kud'in mota amma kin kama kin rik'e kinyi kane kane, to ni bazan iya takawa ba, kuma motane saina tara.

Haka tacigaba da tsaida motoci a hanya, amma duk babu mai tsayawa. sai wata farar mota kiran Honda accord ce ta tsaya. Ummi ta daka tsalle tareda yiwa HUMAIRA gwalo, tayi gudu ta isa jikin motar.

HUMAIRA ta dafe goshi tana fad'in oh my GOD UMMI what have you done? sai kuma tabi bayan ta da gudu itama har izuwa jikin motar. tace haba UMMI yazaki zo kinayiwa stranger magana, ko ban fad'a miki masu irin wad'annan motar sune masu yanka kan mutane ba?

Ummi ta murgud'a baki tace to nidai sai na shiga, baki isa ki tsorata ni ba, tunda duk ke kika jawo.

Ta kuma komawa jikin motar tana k'ok'arin budewa, saidai inaaa HUMAIRA bata bar mata wannan damar ba, ta soma janta tana cewa ay kuwa kema badai ki shiga motar masu yankan kai ba.

Saidai ko taku uku mai kyau batayi ba, taji an rik'e hannunta, ta tsaya cak tareda juyowa cikeda mamaki.

Kyakkyawa ne? kamar yanda ta fad'a a rana, duk da cewa bata wani ga fuskarsa ba, shigar farin coat ne a jikinsa da surgical nose mask a fuskarsa, sai kuma bak'in space daya rufe k'wayan idanunsa.

Saidai duk da cewa fuskar nasa a lullub'e take, hakan bazai hana ka gano kyakkyawan glowing and yellowish skin d'insa. one of the thing dayake dad'a jan attention d'in mutane a kansa shine lallusa, kuma kwantacciyar sumarsa dake shan gyara.

A hankali ya taso cikeda izza irin nasa har inda suke, dukkaninsu suka saki baki suna kallonsa. baiyi magana ba, kamar yanda sukayi tsammani, sai ma kama hannun UMMI dayayi suka juya.

Aikuwa HUMAIRA tayi tsalle ta raba hannun tana fad'in saketa kai b'arawon mutane. ya juyo tareda kafeta da idanu sai k'ifi k'ifi take da idanu tana yiwa UMMI masifa.

Tsawon mintuna kafin, ya juya zai tafi, still baice komai ba, ay kuwa UMMI uwar naciya ta faki HUMAIRA taje ta shige motar tun kafin shi. sai yaja ya tsaya yana kallonta kafin ya juyo ga HUMAIRA datayi tsaye kamar gunki ta had'e rai tamkar wacce akayiwa mutuwa.

Yayi murmushin daya sanya ta saki baki tana kallon sa, don bak'aramin kyau tayi masa ba. bata ankare ba kawai taji jiniyar motarsa a kusa da ita, wato harya juyo da kan motar daidai inda take.

RANSTUWAR JINI (The blood vow) Where stories live. Discover now