❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*THE BLOOD VOW*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 14*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**THE TRAGEDY*
*Not edited please 😕*....................... Ta jefar da wayan a gefenta tana fad'in d'an banzan yaro, ni bansan me yarinyar nan tayi masa da har yake neman ruining rayuwarsa akanta ba.
Sumayya ta kuma cuno baki gaba ranta na suya, tace ay Hajiya ba sai kin tambayi mai tayi masa bama, wannan yarinyar da idanunta a bushe meye ba zatayi ba, kina ganin yanda da maida Bro NAJEEB wani bawanta sai yanda taga dama tayi dashi, baya jin maganar kowa sai nata.
Kuma ki duba bawai tafini da wani abu bane, amma haka bro ya wanke ido ya rufe, ya nuna shi sam baya sona, bro da ko kallon banza bai tab'a min ba, amma saboda ita ya mareni, ya zazzageni ranar a gidanta har da korata wai karna k'ara zuwa, Mummy ay wallahi ba a banza ta barshi haka ba.
Sanata BINTA tayi ajiyar zuciya tace duk nasan hakan Sumayya amma ya zanyi tunda baby boy d'ina ya nace sai ita, a sanadin haka kinga ya gudu ya bar k'asan yak'i dawowa, wai sai na nemeta ya dawo.
What! yanzu Mummy sai ki nemeta kuma? Sanata BINTA ta harareta, of course kuwa, zan nemeta amma bawai don baby boy na ya bukaci hakan ba, sai don na kalli idonta ta fito ta fad'a min black magic d'in datayi wa boy na yake neman kuncewa.
Sumayya ta kada kai cikeda jin dad'i, tace to Mummy after that, kuma idan bro yace saita dawo fa, Sanata BINTA tayi murmushi to ke Sumayya waya fad'a miki akwai aure a tsakaninsu, idan ma akwai wallahi badai wannan yarinyar ba, ta kuma yin dariya indai yarinyar nan ne, na kusa shafe babinta, muzuba mu gani.
Sumayya tayi fito cikeda da jin dad'i tayi dariya ta tafa, yes! Yes! ta rumgumeta, shiyasa nake sonki Mummy.
Naji! mik'o min wayar nan ki gani, ke kuma kije ki duba Amal ko ta tashi daga bacci.
Saida ta bari Sumayya ta fita ta dialing wani number, yawwa DANJA kuna ina? kuyi maza kuzo akwai aiki....
*************
Saukowarsa kenan daga jirgin Turkish airlines data dawo daga k'asar India, a inda suke je wani important aiki na wata hud'u, sai yau yasamu dawowa.
Akai akai yake duba agogon hannunsa yana jan tsaki bayan ya gama dubawa babu driver sa daya kira yazo, ganin tsayuwar na neman damunsa ya sanya shi ya fito daga airport d'in ya nufi main road yana k'ok'arin tsaida taxi.
Hey man! badai har ka gaji da jira na bane ka fito titi kana bubbud'e hanci tamkar bututun mai.
Doctor MANSUR daya gama k'uluwa ya juyo ya hararesa, baice masa komai ba ya sanyawa taxi d'in datazo wucewa ta gabansa hannu.
Har mai motar ya tsaya, doctor ishaq ya fito da sauri ya sallami mai motar, ya juyo kan Dr mansur yace haba mutumina me yayi zafi kake ta fushi haka, ko bakason dawowa Nigeria ne, mu maida ka jirgin garin da ka fito
Dr mansur ya shafa sumar kansa dake kwance bak'i luf luf dashi tamkar wanda yayi dyeing dinsa.
Ya bugi ishaq da a guiwa da tsinin bakin takalminsa kafin ya bud'e motar ya shige.
Dr ishaq ya d'angale k'afa d'aya yana fadin kaifa Mansur ba karamin mugu bane. yanzu daka dokeni a k'afa naga ba d'aga ni zaka iyayi ba.
Har sukayi nisa a mota Dr mansur bai furta ko kalma d'aya ba, yayinda Dr ishaq keta zuba zance tamkar ya had'iyi radio, har suka iso k'ofar apartment d'in Dr mansur inda ya saba zama idan ya shigo garin Adamawa.
Yana shiga dakin ya zage ya shiga wanka, harya fito yayi sallah ishaq bai shigo ba, saboda tsayawa da yayi da wata yarinyar da suna shigowa ya taras da ita tana jiran shi.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama