•... 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
sʜᴇ ᴡᴀs ᴀ ɢɪʀʟ ᴡɪᴛʜ ᴀ ᴍᴏᴜɴᴛᴀɪɴ ᴛᴏ ᴄʟɪᴍʙ!!!BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Don't Forget To Follow My Both Accounts;
Nainarhkd3 @Wattpad.
Nkds @Arewabooks.
..Copy is not allowed.¡!
Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!
_Na sadaukar da wannan Labarin kacokan ɗin sa gare ki ƴar uwa marubuciya kuma abokiyar shawara ƙawata kuma Takwarata Khadija M Abdulwahab A.k.a Queen Kainaat. Haƙiƙa keɗin ta musamman ce a wurina ba zan manta da Alkhairan ki a gareni ba, sai dai na ƙara da yi miki fatan Alkhairi a Rayuwa Allah kuma ya bar zumunci Tsakanin Mu💯... Daɗi da ƙari wannan labari ƙarin sadaukarwa ne ga duk wata ɗiya mace da ta sha gwagwarmaya a Rayuwa.💋_
.. ..
Nainarh KD...✍️
MARUBUCIYAR:1. SARAUNIYAR KYAU
2. TSANTSAR SO
3. ANEESERH ( The Innocent Girl.)
4. KIN CUCENI
5. RANAR BIYAN BUƘATA
6. BA TABBAS
7. CAPTAIN AYUSHERH!.
+234 808 112 9487.
Perfectly Pen's 🖊️
Lafazi Writer's Association...
بسم الله الرحمن الرحيم
Episode 1.
BABUR TRIBE PEOPLE;
Babur Har ila yau ana kiran sunan ƙabilar da Babar ko Baber.
Wannan wata ƙabila ce ta wasu mutane da suka kasance asalin mazauna daji. Asalin da yawa na mutanen ƙabilar sun fito ne daga Yankin tafkin Chadi.
YAWANSU; (POPULATION.)
A ƙiyasi adadin mutanen ƙabilar zasu kai kimanin dubu ɗari biyu zuwa dubu ɗari uku. (200,000-300,000.) A faɗin Duniya.
YANKI; (LOCATION.)
Mutanen ƙabilar sun kasu kashi uku, mafiya rinjaye nasu suna a ƙasar Cameroon yayin da wasu suke a ƙasar Chadi. Har ila yau kuma wasu suna a ƙasar Nigeria. A Nigeria an fi samun su a yankin Arewacin ƙasar a wurare kamar irinsu; Borno da kuma Yobe State da sauransu. As well a ƙasar Cameroon kuma yawancin su, sun fi ne a Far North na Yankin ƙasar Cameroon.
HARSHE; (LANGUAGE.)
Ƙabilar Babur yawancinsu suna magana ne da harshen Bura. Da yake daga cikin reshe dake iyakan Nigeria Da Chadi da kuma Cameroon. (Biu-Mandara.)
ADDINI; (RELIGION.)
Mafi rinjaye na mutanen ƙabilar Babur sun kasance suna Bautar gumaka (Idolatry.) ne, yayin da wasunsu suka canja zuwa adddinin Musulunci (Islam.) kaɗan daga cikinsu kuma sun kasance Kiristoci ne (Christianity.)
AL'ADA; (CULTURE.)
Yawanci na Mutanen ƙabilar Babur sun kasance manoma ne, suna girban amfanin gona kamar irinsu; Gero. Dawa. Da kuma Gujjiya. Da sauransu. Sannan kuma akwai mafarauta a cikinsu sosai.
Abubuwa da yawa nasu na al'ada yana Kamance da na Kanuri da kuma mutanen Shuwa Arab.
WANNAN KE NAN!.
**
*Mayo-Danay. Far North Region. Cameroon.*
Mayo-Danay wani yanki ne ko nace sansani ko ƙauye da wasu daga cikin mutanen ƙabilar Babur dake a ƙasar Cameroon suke zaune a wurin shekara da shekaru.
Mutanen ƙauyen Mayo-Danay sun kasance suna zaune lafiya ƙarƙashin jagorancin Arɗon garin komai yana tafiya dai dai. A wasu shekarun baya. Arɗo ya kasance mabiyin addini ne na al'ada dama sauran mutanen ƙauyen sun kasance akwai wuri da suka ware suna bautar gumaka kuma suna biki irin nasu na addini da kuma al'ada, lokaci bayan lokaci. Arɗo yana da Mata guda biyar rass, bisa adadin yadda addininsu ya umarta, yana kuma da yaran da bazasu ƙirgu ba.
Babban yaron Arɗo a maza sunansa Babankaka ya kasance na daban cikin yaran Arɗo dama sauran mutanen ƙauyen gaba ɗaya domin ya taso ne da wata iriyar halayya da kuma ɗabi'a da ta yi daban da na mutanen ƙabilar. Sam bai yarda da bautan gumaka da Mutanen ƙauyen ke yi ba tun yana ƙaramin sa duk kuwa da yadda a ke so da shi amma yaƙi sam ko zuwa wurin bautansu bayayi. Ba irin azabtar war da Arɗo bai saka an yi ma sa ba wai duk dan ya koma ya zama kamarsu ya dinga bauta irin nasu amma sam yaƙi, haka dole suka saka masa ido, tare kuma da nazarin mummunar mataki da zasu ɗauka a kansa muddun bai canza aƙidar nasa ba. Domin ba kyalesa zasuyi ba. Akwai wani abin burgewa ga kowa da Babankaka yake da, domin shi ɗin ya kasance Gwarzo ne ta fannin farauta tun yana ƙaraminsa kuwa, domin lokaci da dama a daji yake ƙare Rana guda kuma a haka ya taso a daji yake gudanar da rabin Rayuwarsa shi ya sa ya kasance daban da saura yana da shekaru goma sha tara a ka naɗa sa a matsayin Sarkin Samari masu farauta na ƙauyen gaba ɗaya da hakan ya sa a ke kiransa da Jakadi.
Rayuwa ta ci gaba bayan shuɗewar wasu ƴan shekaru wani gagarumin al'amari ya faru a tsakanin Jakadi (Babankaka.) da kuma mutanen ƙauyen su, lamarin dai shi ne a kan yaƙi ya yi bauta irin nasu kuma daga bisani suka sama labari a kan ya shiga wani addini daban ba tare da ya sanar dasu ba kuma hakan ya yi matuƙar fusatasu sosai da hakan kuma ya sa suka haɗa taro da gaba ɗaya mutanen ƙauyen a ka taru sannan suka bawa Jakadi zaɓi biyu a kan ko dai ya bar Addinin da ya shiga sannan ya shiga nasu ko kuma ya bar ƙauyen gaba ɗaya in kuma ba haka ba za su ɗauki mummunar mataki a kan sa. Kowa ya nutsu a lokacin a na jiran a ji amsar da Jakadi zai bada. Hatta shi kansa Arɗo sai da cikin shi ya ɗuri ruwa domin ba zai so Jakadi ya yi nesa da shi ba ko ya ya kuwa. Sai dai ga mamakinsu gaba ɗaya shi ne Jakadi ya zaɓa a kan ya bar ƙauyen da dai a ce ya bar Addinin da yake ciki a yanzu Addinin Rahma Addinin Musulunci.
Wannan lamari ya matuƙar bawa kowa mamaki kuma ya fusata su kwarai, haka suna ji suna gani Jakadi ya bar ƙauyen ba kuma tare da ya ɗauki komai nasa ba kuma tun da ya bar ƙauyen bai dawo ba tsawon shekaru masu ɗan yawa domin an shafe sama da shekaru goma, kuma wannan shi ne ya zama dalilin da Arɗo ya kamu da mummunar ciwo a kan rashin Jakadi tun suna saka rai da dawowarsa har suka haƙura, sai dai zuwa lokacin Arɗo tsufa ya ƙaru sosai baya iya taɓuka komai haka dole Mulkin ƙauyen ya koma Hannun ƙaninsa domin yaronsa da ya kamata a bawa Mulkin bayanan.
Al'amurra sun ci gaba da gudana mutanen ƙauyen suna gabatar da al'amurran su kamar yadda suka saba kwatsam a wani dare suka sama baƙon cin babban al'amari a tattare da su domin kuwa Jakadi wato Babankaka shi ne ya dawo musu garin a cikin wani irin yanayi jikinsa jina-jina da jini ga kuma sara da a ka yi masa ƙarin abin mamaki da ruɗani shi ne a tare yake da jaririya da ikon Allah ita kuma babu abin da ya sameta domin goya ta ya yi tam ta gaba kuma ya kakkareta daga duk wani farmaki, wannan dalilin ya sa babu abin da ya sameta. A wannan dare kowa da ka gani daga kan mutanen gari da suka yi cincirindo a ƙofar gidan Arɗo da su kansu iyalan Arɗon har ma da shi kansa Arɗon gaba ɗayansu mamaki ne a tare da su na ganin Jakadi a wannan dare cikin wannan hali a irin wannan lokaci ga kuma jaririya, mamaki, ruɗani, tashin hankali shi ne abin da ke tare da kowannen su kuma bakinsu ɗauke yake da tarin tambayoyi a garesa.
Gaba ɗaya idanunsu suna a kan Jakadi ne dake zaune saman wani Marmara gaban wuta dake ci ranga-ranga kuma ta zama haske a wurin gaba ɗaya, zuwa yanzu ya kwance wannan Jaririyar daga goyan da ya yi ma ta, a halin yanzu tana riƙe ne a hannunsa ya zuba mata idanu yayin da ita ma Jaririyar take ɗan gif-gifta nata kyawawan Meadow Green Eyes ɗin tamkar tasan abin da ke faruwa.
Arɗon yanzu, wato Sarkin da a ka naɗa a ƙauyen shi ne ya sake maimaita tambayar da ya yi ma Jakadi a karo na biyu da cewa cikin harshensu na Babur.
"Tsawon lokaci kana ina, mene ya faru ka dawo mana a haka, wannan Jaririyar ta wacece, kuma daga ina ka samo ta?."
Sai dai a ka shafe kusan sakanni talatin da yi masa tambayar a karo na biyu. Kamar ba zai magana ba. Sai suka ji wannan murya tasa a yadda take wata kalar kakkaura mai daɗin saurare ya fara magana cikin harshen nasu da bada amsa kamar haka.
"Nigeria ita ce ƙasar da na koma nake Rayuwa tsawon waɗan nan shekaru, wannan Jaririyar kuma Ɗiyata ce."
Abin da ya faɗa ke nan, ya yi shiru daga haka.
Surutu ne sama sama ya fara tashi a wurin kowa yana faɗar albarkacin bakinsa ba abin da kake ji sai ƙus-ƙus dake tashi. Shi kuwa Jakadi har yanzu idanunsa a kan wannan kyakkyawar Jaririyar suke babu abin da yake tunawa sai maganganun Mahaifiyarta a garesa a sa'ilin da take dab da barin Duniyar. _Cikin Wata kalar wahalalliyar Muryar da ta gama galaɓaita da wahala ta ci gaba da faɗin. _"Jakadi! Na yarda da kai! Shi ya sa a wannan taƙin da nake tsakanin Rayuwa da Mutuwa, na bar maka Ɗiyata Halak, ina mai roƙonka a kan ka kulamin da ita sannan ka saka ma ta sunana wato AYUSHERH! sannan kayi min wata alfarma, kayi iya iyawarka wurin ganin Ayusherh ta zama Soja bayan ta girma domin ta hakan ne nake saka ran komai zai dai dai ta, duk wata ɓarna da a ka yi zata gyaru, azzalumai za su fuskanci mummunar sakamako daga zunubansu."_ Daga haka kuma ta yi shiru ta ɗan rumtse ido sakamakon zugi da bayanta yake yi a dalilin wuƙar da mutanen da suka biyo ta, suna farautar Rayuwarta domin su halaka ɗaya daga cikinsu ya yi nasarar caka ma ta wuƙar ta baya!_"Baka bamu amsar tambayar mu ba. Garin ya ya haka jikinka duk jini da kuma sara ta ko'ina sannan ina ita Mahaifiyar Jaririyar take?."
Arɗo ya ƙara yi masa wannan tambayar.
"Ta mutu."
Cewar Jakadi a taƙaice.
"Garin ya ya, kuma su waye suka kashe ta?."
Zuwa yanzu Jakadi ya fara gundura da waɗan nan tambayoyi.
"Farmakin mu a ka yi a hanyar mu na zuwa nan kawo muku ziyara. Sanadin hakan ta mutu ni da wasu daga cikin mutanen ƙauyen da wannan al'amari ya faru da su mun yi ma ta sutura an rufe ta a can."
Jikinsu ne ya ɗan yi sanyi jin abin da ya ce, haƙiƙa wasu daga cikinsu sun tausaya masa, jin cewar ya rasa Matarsa duk a dalilin ya zo ya duba su.
Wasu kam ko'a jikinsu sai ma cewa da suke tsinuwa ce take bibiyarsa a dalilin bijire musu da ya yi.
"Har yanzu kana a wancan Addinin?."
Arɗo ya sake yi masa wata tambayar Again, domin kaf cikinsu shi ne mai zarrar da zai iya yi ma Jakadi waɗan nan tambayoyi ya zauna lafiya, don kuwa Jakadi ya amsa sunan nasa ta ko'ina.
Wani irin ɗa go manyan idanunsa Jakadi ya yi tare da watsatsu a kan Arɗo ƙanin Mahaifinsa. Ba tare da ya yi magana ba ya miƙe tsaye riƙe da Yarinyar sannan ne ya basa amsa da faɗin.
"Har gobe ina nan a cikin Addinina kuma babu abin da zai saka na canza har Abada. Ku ma ina yi muku fatan shiriya ku gane hanya madaidaiciya wata rana tun kafin lokaci ya ƙure muku."
Yana gama faɗar hakan ya juya tare da shiga cikin makeken gidan Arɗo ƙaton gaske da yake ginin yaɓe haɗe da bukka, kaf ƙauyen shi ne gida mai ginin yaɓe na jar ƙasar dake bakin tekun garin dake dab da wani ƙaton dutse.
Bai ankara ba yaji yaci karo da Mutum daga yanayin kuma ya san Mace ce. Ya ɗa ga tsayayyun idanunsa yana dubanta. Kana ganin fuskarta tsoro ne zalla sai gif-gifta Manyan idanunta take yi yayin da take cukurkuɗa curkurkuɗaɗɗen gashin ta mai tsayi da hannunta guda, yayin da ɗayan ta kama bakinta dake rawa, idanunta a zare cike take da tsoron da ya fahimce na ganinsa ne. Raɓa ta ya yi ya wuce ciki, ta bisa da ido sai kuma ta daka tsalle tare da rugawa da gudu ta fita.
Babaya ke nan sarkin shiririta da shirme kuma Ɗiya wurin Arɗon yanzu, Mahaifiyarta ta rasu tun tana tsumma, a Hannun kwarin Arɗo, ta taso kuma ta girma wato a hannun Mahaifiyar Jakadi ke nan.
Wani ɗan ƙurmin ɗaki ya shiga tare da zama a saman gadon ƙasa dake ciki. Bayan ya rufe ƙofar ɗakin da take na kara. Ya tattara nutsuwarsa gaba ɗaya yana tuna abin da ya kasance ya afku a daren jiya. Shi kansa bai yi tsammanin zai tsira ba. Kuma yana da tabbacin Mahaifiyar wannan Jaririyar dake hannunsa a yanzu ta mutu. Domin kuwa a gaban idon sa komai ya faru.
Ya sauke ajiyar zuciya a nutse. Yana tuna kalamanta a gare sa. Tabbas komai da ya faru cikin sauri ya kasance ya faru da haɗu wa da ita da ya yi a ƙurmin daji tana zabga gudu da tsohon ciki ga wasu muggan mutane dake bin ta. Da taimaka ma ta da ya yi har zuwa haihuwa da ta yi zuwa wayewar gari da kuma gano maɓoyarsu da waɗan nan mutane suka yi da wasiyyar da ta bar masa a kan Jaririyar da ta haifa, kafin nan domin ta san ita kam da wuya ta rayu. Sake gudun tsira da suka yi tare yana riƙe da Jaririyar tun farar safiya, gudu suke a dajin Allah ba hutu sai in idan ta ce ta gaji ne sannan su samu su tsaya hutu, kuma a wannan taƙin ne ta basa gaba ɗaya labarin ta da dalilin ta na son ɗiyarta da ta zaɓa ya saka ma ta suna Ayusherh da ta zama Soja, har ma da irin mummunar cin amana da a ka yi ma ta ita da mijinta da hakan ya zama sila na Rayuwarsa. Sai yammaci suka isa wani ƙauye, nan ne da kyar suka samu Mutanen ƙauyen suka taimaka musu har suka basu masauki. Da sharaɗin safiya nayi zasu ƙara gaba. Jaririyar da Mahaifiyarta suka sama kulawa da ta dace.
A cikin dare kuma suka sama baƙon cin waɗan nan gawurtattun ƴan ta'adda da suka farma ƙauyen da mutanen cikinsa. Ƙauyen yana a dab da Iyakar Nigeria da kuma Cameroon ne.__
TOFA!
Reader's kun dai ji ta yadda Labarin ya soma da salonsa.
Wai shin wacece mahaifiyar wannan Jaririyar ce da ta zaɓi a sakama Ɗiyarta sunanta kuma take so bayan Ɗiyar nata ta girma da ta shiga aikin SOJA?. Mene ne ainihin labarin ta?. Shin ya ya Rayuwar Ayusherh zai kasance a wannan ƙauye cikin waɗan nan ƙabila da ba nata ba?. Wai ma mutanen gari za su bari Jakadi ya ci gaba da zama a cikinsu bayan ba addininsu yake yi ba?. Su waye muggan mutane da suka biyo Mahaifiyar Ayusherh domin su kasheta?, shin su ne waɗan da suka farmaki wannan ƙauye da har hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta? Idan su ne, mene ne dalilin su, waye ne yake da alhakin duk waɗan nan????.
Hummp muje zuwa domin yanzu a ka fara kafta wasar kuma da alama da zafi Zafinsa ya taho.
Alƙamin Nainarh KD...✍️
𝓐.𝓴.𝓐~𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡

YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romantizm# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...