16

6 0 0
                                        

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)

                                   https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5

        BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.


*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 16.

     
AYUSHERH!
Fitowa suka yi daga motar lokacin suka ƙari so Anguwan ta faka motar a saitin inda motar Jasmine ke fa ke, yayin da Jasmine ɗin take zaune saman motar tana latsa waya. Ƙari sowarsu Ayusherh shi ne ya sa ta sauko tare da ƙari sawa inda suke tsaye jikin Jeep ɗin da suka zo a ciki, tana murmushi ta ce.
“Da alama aiki na musamman ne ya kawo Captain wannan area da kanta.”
Ta faɗa a yayin da ta ƙari sa wurin tana fuskantarsu.
Miƙa ma Lieutenant Hammad iPad ɗin dake hannunta Ayusherh ta yi tare da cire Farin Glass dake idanunta tana kallon Jasmine fuskarta ba walwala ta ce.
“Ya a ka yi naga Anguwan ya lashe ne kamar ba masu rayuwa a ciki?.”
Ta tambaya tana ɗan duban yanayin Anguwan da tafi kama da na masu ƙaramin ƙarfi.
Ita ko Jasmine lura da yanayin da Ayusherh take ciki ne ya sa ta ce.
“Nima dai haka nazo na tarar sai dai na sama wasu mutane da na tambaye su dangane da hakan sai cewa suka yi kowa yana gida ne a sakamakon abin da ya faru wai har shima Sa'idu wanda ya yi kisan yana gida Mahaifiyarsa ta ɓoye sa. So I was very confused saboda ban san mene ne yake faruwa ba.”
Jasmine ta ƙare maganar tare da ɗa ga kafaɗa.
Jinjina kai Ayusherh ta yi domin zuwa yanzu ta fahimci ainihin daga ina matsalar ta samo Asali.
“Yanzu ya kake ganin za'ayi?.”
Ta faɗa tana duban Lieutenant Hammad domin jin ra'ayinsa.
“A gaskiya Captain bani da abin faɗa saboda lamarin yafi ƙarfin kaina na rasa ta yadda zan lissafi al'amarin.”
“a, ah kai nifa kun ƙara sakani a ruɗani wai mene ne yake faruwa ne wanene shi Sa'idu yake ko wa?.”
Cewar Jasmine tana kallonsu su duka.
“Karki damu zan miki bayani.”
Ayusherh ta faɗa tare da buɗe Jeep ɗin da suka zo a cikinta ta ciro wata madaidaiciyar loud speaker.
“Ina ga wannan hanyar ce mafi sauƙi a garemu.”
Ta faɗa tare da ɗan bubbuga hannunta a kan loud speaker ɗin sannan ta kai saitin bakinta ta ɗan yi gyaran murya tare da fara magana kamar haka.
“Assalamu Alaikum Jama'a!. Ga waɗan da basu san ni ba, sunana AYUSHERH jami'ar soja muƙamin Captain. Nazo ne tare da abokan aikina Lieutenant Hammad da kuma Second Lieutenant Jasmine a domin tafiya da Sa'idu domin yanke masa hukunci dai dai da abin da ya aikata. Ku daure ku bamu haɗin kai ku fito a yi abin nan a gaban kowa, ku sani yanzu ba lokacin da jahiliyya ba ne da kuna da sani a kan komai amma kuke takewa kuma kuke ƙoƙarin kare masu laifi. Shi wannan matashi Sa'idu tun farkon fari abin da ya yi ya cancanci mummunar hukunci a kai ta fuskar addini da na hukuma amma ba'a yi komai ba, ban sani ba su Malaman Addinin bacci suke ne har haka ke faruwa ko ya ya ko kuwa su Jami'an hukumar basu sama horon da ya da ce ba ne har haka ke faruwa, abin takaici wai a ce har jami'an ƴan sanda ne za'a sama gama garin mutum ya fasa kansu da kwalba kawai dan sun zo tafiya da shi a kan laifi da ya yi. Hummp a ajiye duk waɗan nan a gefe kuyi wa Allah ku fito sannan ku bani amsar tambaya ɗaya tal da zan yi muku a kan wannan bawan Allah Sa'idu, daga nan ni da kuma ku sai a tattauna yadda ya kamata a yi masa.”
Ayusherh ta yi shiru bayan ta kawo nan a zancen ta sannan ta a je loud speaker ɗin a saman Jeep ɗin.
Tana mayar da Farin Glass ɗin da ya kasance a wasu lokutan yana taimaka ma ta wurin gani a dalilin wasu lokutan da take da matsalar gani hakan ya samo asali ne shekarun baya da suka gabata.
“Hump bana tunanin mutanen nan za su bamu haɗin kai da ya kamata..”
Cewar Lieutenant Hammad sai dai kafin ya rufe baki a hankali kuma cikin sanyin jiki mutane maza da mata yara da manya na Anguwan suka fara fitowa daga gidajensu kan ka ce kabo duk sun fifito tare da kafa layi a jere daga yanayin duban da suke ma su Ayusherh kamar a ce ƙyat su arce zaka fahimci a ɗan tsorace suke.
Lura da haka ya sa Ayusherh ta yi wa Lieutenant Hammad alama da ya ɗauki loud speaker ɗin ya yi musu magana.
Hakan kuwa ya yi, ya ɗauki loud speakern tare da fara magana kamar haka;
“Ku saki jikinku domin mu ba mun zo nan ne domin cutar daku ba sai dan kare ku da kuma kama Mutum mai laifi daga cikinku amma sai da haɗin kanku.”
Dai dai ya ƙare maganar idanunsa suka sauka a kan wata dattijuwa dake zaune gefe ta rafka uban tagumi ta yi jigum hankalinta ma ba'a kansu yake ba.
Miƙa ma Ayusherh loud speaker ɗin ya yi sannan da ido ya yi ma ta alama da Matar.
“Kafin nace wani abu zan so sanin wacece wancan Matar?.”
Ayusherh ta faɗa muryarta raɗau ta loud speakern tanayi musu nuni da dattijuwar. Sai dai kaf cikin mutanen wurin an rasa mai zarrar da zai yi bayani har sai da ta maimaita amma shiru. Ganin haka ya sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fara taka wa ta isa ga matar tare da ɗan tsugunna wa tana duban Matar ta ce.
“Madam lafiya kuwa? Zamu iya sanin ko meke faruwa?.”
Ta faɗa cike da kulawa. Sai dai shiru ba amsa daga matar. Ayusherh zata maimaita abin da ta faɗa taji murya daga bayanta ana faɗin.
“Mama tsohuwa ce ita ce Kaka a Wurin Malam wanda Sa'idu Azzalumi ya kashe.”
Ayusherh ta yi saurin juyawa tana duban yaron da bai haure shekaru goma ba ya yi maganar yayin da bai ƙari sa ba Mahaifiyarsa ta yi saurin toshe masa baki.
“uhump ina sauraren ka mene ne ya faru ta kasance a haka?.”
Cewar Ayusherh bayan ta ƙari sa wurin tanayiwa Mahaifiyar nasa wani irin duba, ganin uwar taƙi sakin ɗan ne ya sa Ayusherh ta ce.
“Ci gaba ki ci gaba da hanasa faɗan gaskiya har har zuwa yadda ya yi miki, ina mai tabbatar miki daga samun uwa irin ku ne da ba za su ƙara ma yara kwarin gwiwa ba sai dai su hana su faɗar gaskiya to daga haka ne a ke samun al'umma a jirkice saboda tun farkon fari ba'a nuna musu faɗar gaskiya shi ne ba.”
Girgiza kai Matar ta hau yi yadda kasan ƙadangare na neman manja, sai kuma ta yi saurin sakin bakin yaron da ta rufe da hannunta ai kuwa yaro kamar jira yake ya ci gaba da faɗin.
“Ta ce ba zata ƙara magana ba muddun adalci bai samu ba daga kashe ma ta jika da Sa'idu Azzalumi ya yi.”
“Wanene shi jikan nata kuma me ya sa a  ke kiransa da malam sannan mene ne ya sa shi wannan bawan Allah Sa'idu ya kashesa?.”
Ayusherh ta jero ma yaron tambaya. Ai kuwa ya wage baki tare da fara bata amsa dalla dalla.
“Saboda Sa'idu ya kasance yana abin da ba dai dai ba kuma addini bai koyar ba shi ya sa Malam wato jikan Mama tsohuwa ya yi ƙoƙarin ganin ya ganar da shi gaskiya shi kuma Sa'idu ya fusata a cewarsa ya mayar da shi jahili shi ya sa ya zo masa da maganar, wannan abu ne ya kai su ga faɗa kuma laifin azzalumi Sa'idu ne kuma shi ne ya kashe mana Malamin mu na islamiyya a tsakiyar Anguwan a gaban mutane kuma ba wanda ya ɗauki mataki shi ne Mama tsohuwa ta shiga damuwa a kan haka Likita ma ya ce tana da hawan jini da ciwon zuciya.”
Yaro ya ƙare maganar yana sheshsheƙa.
Da sauri Ayusherh ta ciro Handkerchief ɗin daga aljihu ta ɗan goge ma hawaye sannan ta ce. “Yaro mene ne sunanka?.”
“Sunana Muhammad Khabir.”
Yaron ya bata amsa.
“Ma sha Allah, zaka iya nuna min gidan su Sa'idun?.”
Jinjina ma ta kai yaron ya yi alamar e.
Ayusherh ta kamo hannunsa sannan ta duba mutanen tana ɗan girgiza kai ta ce. “Kuna da buƙatar canji a kankin kanku kafin na sama daku su gyara.”
Ta faɗa tare da yin gaba abin ta tare da yaron suka nufa gidan, yayin da Jasmine da Lieutenant Hammad suka mara ma ta baya. Suma mutane masu son ganin kwakwaf da waɗan da jikinsu ya yi sanyi suka mara musu Baya.
Ƙaton gida ne da alama irin gidan yawan nan ne?.
Tsayawa suka yi a tsakiyar gidan Jasmine ta miƙa ma Ayusherh loud speakern sannan Ayusherh ta ɗan yi gyaran murya batace komai ba. Sai mutanen gidan kowa ya fara fitowa daga ɗaki suna yo waje. Daga ƙarshe wata ƴar duma-dumar mace ta fito hannunta janye da wani matashin saurayi da tana jansa yana boƙarewa shi ga ɗan banza. Tsayawa matar ta yi ƙerere gaban Ayusherh riƙe da ƙugu sannan ta nuna matashin saurayin ta ce.
“Ga Sa'idun nan kuma naga mara kunya da kishin addinin da ya isa ya taɓa min ɗa, arnan banza kawai!.”
Ta ƙare maganar da jan dogon tsuka, a fusace Lieutenant da Jasmine suka yi kanta, amma Ayusherh ta dakatar da su, sannan ta yi ma matar duban tsanaki kafin ya ɗan taka kaɗan ta isa ga matar ta ce.
“Baiwar Allah ba hayaniya ne ya kawo mu ba, sannan ba mun zo ne mu tafi da Sa'idu ta ƙarfin tuwo ba, a tsanaki zamuyi komai. Baiwar Allah ki saurareni magana fa a ke ta addini shin wai ke da kunnen ki kika taɓa ji ko karantawa a Alkur'ani mai girma ko kuma a sauran littafai a inda a ka halasta musulmi na kwarai ya yi abin da ɗan ki ya aikata?. Laifukan nasa da yawa kuma masu tsauri ne duka na farko tsakaninsa da Ubangiji ne mahalicci da ya haɗa sa da wani bayanshi bayan kuma ya san hakan mummunar saɓo ne koda yake a wannan zamanin mutane da yawa basu ɗauki hakan a komai ba domin a zahiri Akwai masu yin irin abin da yake yi wai kuma da sunan su Musulmai ne, ni dai kam a'iya sanina babu wani littafi na addini ko kuma wata sura ko Annabi da a ka aiko a kan mutane irin ɗan ki suyi abin da suke aikatawa. Musulunci bai koyar damu haka ba, to amma son zuciya irin namu na ɗan Adam yana sakawa ana ganin gaskiya amma a take ta, sai kuma laifi na biyu da ɗan ki yayi shi ne kisan kai, a musulunci kisan kai Babban laifi ne da kai tsaye zai kai mutum zuwa wuta, gashi ɗan ki ya aikata ke kuma kin goya masa baya, har kike kiran mu da arna bayan kuma a addini kafirta musulmi shima Babban laifi ne, amma duk kin take wannan, to wai a hakan ne har kike gadara da kinason ɗan ki bayan sanin kanki ne a yanzu da zai mutum duk da bana da sani a kan gaibu amma da wuya ba wuta zai shiga ba, kiji tsoron Allah Baiwar Allah ki tuna ke musulma ce kuma uwa, yanzu abin da kika yi kinyiwa wannan Baiwar Allah mahaifiyar Malam adalci inda a ce baƙin cikin abin da ɗan ki ya yi, zai saka a mutu a yanzu to fa alhakin rayuka biyu a kan ɗan ki zasu kasance kuma har da ke kanki saboda ke kika mara masa baya.”
Zuwa yanzu jikin Matar ya yi mugun sanyi da har maganganun Ayusherh suka saka taji bata kyauta wasu ma daga mutanen dake tsai-tsaye sai da suka zubar da hawaye.
“Kuyi haƙuri Dan Allah nasan ban kyauta ba amma sharrin shaidan ne da kuma mahaukaciyar ƙaunar da nake ma ɗana da ya kasance shi ɗaya ne ɗana namiji kuma daɗi da ƙari da bakinsa ya ce min wai a mafarki yaga Ma'aiki Sallallahu Alaihi Wasallama, to nima kuma naga ai idan mutum yaga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama a mafarki ana masa kyakkyawan zato da samun aljanna shi ya sa naƙi yarda ɗana ya aikata abin da a ka ce ya yi kuma naƙi yarda a yanke masa hukunci na ƙeƙashe idanuna ina zuba rashin mutunci ga kowa amma Dan Allah kuyi haƙuri.”
Matar ta ƙare maganar tana durƙusa gwiwowinta ƙasa cikin zubda hawaye.
Girgiza kai Ayusherh ta yi, kana ta ce. “bamu ne zaki bawa haƙuri ba, da fari ki fara neman yafiyar Allah sannan ita ma mahaifiyar Malam ki nema yafiyarta. Shi kuma Malam Allah yaji ƙan sa da rahama.”
Gaba ɗaya Jama'an wurin ne suka amsa da Ameen!!!
Sannan Ayusherh ta dubi Matashi Sa'idu, da ya yi tsuru a wurin.
“Ba zan ce maka komai ba, sai dai na tuna maka da kaji tsoron Allah.”
Ta faɗa kana ta yi shiru.
Sa'idu bai ce komai ba ya duƙƙar da kansa ƙasa haƙiƙa ya yi danasani na abubuwan da ya aikata sai dai danasanin ya kasance mara amfani saboda lokaci ya riga ya ƙure. Hannu biyu ya miƙa, alamar ya yi surrender.
Ganin haka ya sa Lieutenant Hammad ya ciro handcuffs sannan ya saka masa.
Darewa mutane suka yi suka basu hanyar fita. Waje suka fito Ayusherh ta ƙari sa gaban Matar da ta miƙe tsaye ganin an fito da Sa'idu.
“My condolence about your Grandchild. In sha Allah za'a yanke ma Sa'idu hukunci dai dai da abin da ya aikata.”
Ayusherh ta faɗa cikin sanyin murya bayan ta dafa kafaɗar Matar.
Rasa abin faɗa ya sa Matar ta rungumo Ayusherh tana hawaye.
Wani irin yanayi Ayusherh ta tsinci kanta domin tun da take a rayuwarta wannan shi ne karo na farko da wata mata uwa ta rungume ta har haka, kuma cike da ƙauna, sai ta tsinci kanta a yanayi mara misaltawa, soyayyar Mahaifiya tabbas daban yake da komai.
Murmushi Ayusherh ta sakarwa Matar sannan ta ƙari sa wurin Yaro Muhammad Khabir ta dube sa ta ce.
“Haƙiƙa kayi dacen mahaifiya da take ƙaunar ka kuma take gudun abin da zai sameka, ka riƙe da kyau kaji kuma ka bata kulawa ka nuna ma ta ƙauna fiye da yadda take maka saboda Mahaifiya daban take da kowa da kuma komai kaji?.”
Jinjina kai yaron ya yi sannan ya ce.
“To Anty Amma ina fata kema haka kike ma mahaifiyarki?.”
Ayusherh ta ɗan yi jim da jin tambayar da ya yi mata, sai ta girgiza kai tana ɗan shuke baki ta ce.
“Bani da mahaifiya, domin an faɗa min a lokacin da ta haifeni ta rasu, amma ina matuƙar ƙaunar ta kuma nayi kewarta sai dai a koda yaushe na tuna ta ina Kasancewa ne mai yi ma ta addu'a a koda yaushe.”
Yaron ya yi shiru yayin da mutanen wurin jikinsu ya da ɗa sanyi.
“To na bar miki Mahaifiyata daga yanzu ta zaman Mahaifiyarmu mu biyu dama ta ce tanason ƴa Mace sai dai bata ita daga yanzu kin ga ita ma mamana ta sama ƴa ko? Kuma muma mun sama soja a gidan mu.”
Maganar yaron ta bawa Ayusherh dariya da kuma tausayi. Sai kawai ta ce.
“Ai kuwa na gode kuma naji daɗi ina fata Maman zata karɓa sabuwar ƴar nata.”
Ayusherh ta ƙare maganar tare da saita tsayuwarta.
“E mana ko Mama ina ce zaki karɓe sabuwar ƴar ki soja?.”
Jinjina mai Mahaifiyar yaron ta yi alamar e.
Ayusherh ta ɗan yi murmushi zatayi magana Jasmine ta ce.
“Woww kuma fa zakuyi kyau as a family, please Captain ɗan gyara nayi kuma hoto.”
Ta faɗa da ɗan magiyarta. Murmushi kurum Ayusherh ta yi sannan ta gyara suka saitu, ita da Matar da kuma yaron ai kuwa Jasmine ta kafta musu photo. Daga haka ita ma Ayusherh ta yi musu selfie kala biyu ɗaya har da Jasmine, ɗaya kuma banda ita.
Daga haka dai suka saka Sa'idu a motar da Ayusherh tazo ita da Lieutenant Hammad.
Lieutenant ne ya ja motar yayin da Ayusherh ta shiga motar da Jasmine take daga nan suka bar Anguwan.
_NOTE; Ba wai an ƙirƙira wannan ɓangare na Sa'idu ba ne ba wai domin cin mutumci ga wani ko wata. An yi ne duba da ganin irin makamacin abin da Sa'idu ke yi da wasu daga cikin mutane suka ɗauka suna yi ne bayan su da kansu sun san hakan ba dai dai ba ne. Muna fata za'a gane kuma a gyara, idan ma anga wasu sunayi sai a samesu domin sanar da su gaskiya idan ma hakan ba zai yiwu ba, a sama Malami na addini kuma na kirki a faɗa masa domin yaja masa kunne. Daga ƙarshe, Dan Allah Iyaye mata a dage a kan tarbiyyar yara domin su ne manyan gobe, makarantar nan idan sun je a ke kulawa da abin da suke yi dama yanayin hulɗar su da sauran yara Sa'anninsu, a wannan zamani da komai ya gurɓace bai kamata ake barin yara kara zube ba;;;; Allah ya sa mu gyara gaba ɗaya._
_Sannan mu haɗu a next page domin sanin yadda zata kasance. Kar fa a manta har yanzu Captain ɗin mu bata haɗu da Haisam namu na zamani ba 😂 Ni kaina na ƙosa su haɗun domin ganin yadda zata kasance 😆🔥_
Ga masu wani ƙorafi ko son magana dani zasu iya tuntuɓana ta lambar what'ssapp ɗina kamar haka; 08081129487 ko kuma 07067953066.
Nainarh ce ƴar mutan KD na gode. 🥰🪄💝🌷🥀

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now