CAPTAIN AYUSHERH...4

5 1 0
                                    

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
                                  
       
https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5

BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡

Don't Forget To Follow My Both Accounts;
Nainarhkd3 @Wattpad.
Nkds @Arewabooks.
..

Episode 4.

Dubanta ya ƙara yi jin batace komai ba.
Ya ƙara kiran sunanta kamar yadda ya saba da faɗin.
...
“Captain!.”
Ya kira ta. Bata amsa ba, sai ma kauda kai da ta yi domin zuwa yanzu Tata ya sanar da ita ma'anar da kalmar CAPTAIN ke nufi, wani muƙami ne na sojoji. Wato ke nan tun kafin ta zama Sojar shi har ya zaɓa ma ta muƙamin.
“Kamar fa kina cikin damuwa, ina lura dake tun kwanaki biyu baya, ki faɗa min mene ne yake damun ki, ni kuma nayi alƙawarin zan yi matuƙar ƙoƙari iya iyawata ganin cewar na yi maganin ko mene ne yake damun naki.”
Ya ƙara faɗa cike da son sanin ainihin abin da yake damun nata har ya sakata a damuwa.
Ba tare da Ayusherh ta kalle sa ba ta fara magana da faɗin.
“Tata ne! Ya takura a kan zamu koma Nigeria wai zai sakani a makarantar sojoji na ƙasar, saboda soja yake so na zama wai ma ashe Captain da ya sa a ke kira na, sunan wani muƙami ne a cikin sojojin.”
Ta ƙare maganar tare da dubansa da Meadow Green Eyes ɗin ta, bata bari ya ce komai ba ta ƙara da faɗin.
“Ni kuma banason zama wata soja, nafi son ya bar ni cikin marayana na ci gaba da Rayuwa cikin ƙauyen nan da Mutanen cikinsa domin da hakan na saba.”
Shiru ya yi yana sauraren ta, bai katse ta ba, har sai da ta kai a ya, sannan ta yi shiru dan kanta, sannan ne shima ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin.
“Matsalarmu da damuwarmu kusan ɗaya ne.”
“Kamar ya ya?.”
Ayusherh ta tambaya cikin rashin fahimta.
Mamman ya ɗan taɓe baki tare da ci gaba faɗin.
“Kin san dai kafin mahaifin ki, mahaifiyata ce mace ta farko a ƙauyen nan da ta fara taka al'ada ta bar ƙauyen a kan za'a aura ma ta wanda bata ra'ayi, har ta je ƙaddara ya kaita can wata ƙasar daban har ta yi Aure ta kuma haifeni, daga bisani kuma ta dawo nan dani ta nema gafarar kowa kuma take sanar da cewar mijin da ta aura ya sake ta shi ne ta dawo. Da hakan ya sa gulma da tsegumi ya yi yawa a kanta mutanen ƙauye suke cewa ba wani Aure da ta yi kawai taje a wayon duniya ne ta sameni, har wasu ma suke kirana da ba ɗan halak ba, a yawon duniya a ka sameni...”
Mamman ya ɗan dakata a nan. Yayin da Ayusherh da ta yi zuru tana sauraren sa,  tana kuma gyaɗa kai yadda kasan ƙadangaruwa, jin ya yi shiru ya sa ta faɗin.
“Sai mai kuma ya faru da ka ce matsalar mu ya zo ɗaya?.”
Mamman ya jijjiga kai tare da ci gaba da cewa.
“Sanin kanki ne har Mahaifiyata ta rasu mutanen ƙauye basu daina yamuɗiɗi da ita ba a kan cewar yawon duniya ta tafi har hakan ya yi silar samuna. To ashe kafin rasuwar ta, ta bar wasiyya a kan inda za'a sama mahaifina ta kuma roƙi da a kaini wurinsa, to shi ne fa yanzu Ûná Arɗo ya matsa a kan zai ware mutane a dangi da zasu tafi tare dani domin neman mahaifina kuma su bar ni a wurinsa.”
Mamman ya ƙara shiru da ya kai nan a zancen sa.
Ayusherh da ta yi ma sa tsuru da idanu ta yi saurin faɗin.
“To yanzu fa, ka yanke shawarar tafiya ne ka bar mu?.”
Ta yi masa tambayar tana zuba masa Manyan idanunta.
Mamman ya girgiza kai.
“Banason hakan har zuciyata domin ba zan iya tafiya na bar ki ba, sai dai kuma idan na ci gaba da zama a nan haka zan ƙare rayuwata a na ɗauka na matsayin ba ɗan halak ba.”
Wannan karon da tausaya wa Ayusherh ta dubesa da sauri ta ce.
“To mene ne abin yi?.”
“Nima ban sa ni ba.”
Ya bata amsa.
Ayusherh bata ƙara cewa komai ba, sai ma kanta da ta ɗaura bisa kafaɗarsa suka ci gaba da zaman shiru, zuwa can ya sauke kanta daga kafaɗarsa yana faɗin.
“Babu kyau, ko kin manta mu ɗin ba muharraman juna ba ne?.”
Turo baki Ayusherh ta yi ba tare da ta ce Komai ba, sai ma gunguni da ta fara.
Mamman ya yi murmushi yana shirin magana ke nan suka ji wata ƙara da ta amsa a ko'ina na wurin da alama daga wuri mai nisa ƙarar ta taho.
Gaba ɗaya suka zazzaro ido. Ayusherh na faɗin. “Wannan ƙarar kuma daga ina haka?.”
Sai dai kafin ta rufe baki ne ta hango abin da ya tashi hankalinta matuƙa. Da sauri ta kai hannu tana yima Mamman nuni da cikin ƙauyen da suke hangowa wuta na tashi ta wasu wuraren yayin suke hango Mutane a warwatse da alama dai ba lafiya.
Shima Mamman ya ga abin da ta gani, hankali tashe ya buɗe baki domin magana, sai dai tuni Ayusherh da ta tashi ta yi nisa yayin sauka daga saman dutsen, ganin haka ya sa shima ya yi saurin bin bayanta yana kiran sunanta domin ya fahimci ba lafiya da alama ƴan ta'adda ne suka kai ma ƙauyen nasu hari a wannan yammacin.
Sai dai Ayusherh bata saurare sa ba har ta samu ta ƙari sa sauka gaba ɗaya daga saman Dutsen da mugun gudu ta nufa cikin ƙauyen nasu. Da kyar shi kam Mamman ya kusa saukowa daga saman dutsen yana dab da saukowa ne ƙafarsa ɗaya ta gurɗe gaba ɗayansa ya yo ƙasa. Ai kuwa ya yi mugun buguwa, amma haka ya daure yana ciccijewa ya miƙe tsaye tare da takawa shima ya nufa ƙauyen yana ci gaba da kiran sunan Ayusherh da tuni ta kai ƙauyen sai dai tashin hankali da ta tarar ne ya yi matuƙar gigita lissafin ta domin da gawarwaki na mutanen da a ka harbe ta fara cin karo, wasu a ma ce, wasu kuma iya rauni suka ji. Da gudun bala'i ta nufa hanyar gidansu tana kwala kiran sunan Tata da sauran mutanen gidan ganin haka shima Mamman yabi bayanta yana ci gaba da kwala kiran sunanta shima.

Da gawar Matar mahaifin nata wato Babaya dake kwance a tsakiyar gidan cikin jini Ayusherh ta fara cin karo, ta saki wani lalataccen ihu tana Zubewa ƙasa tare da kiran sunanta sai dai shiru domin babu rai a tare da ita.
“Ayusherh garin nan fa ba lafiya ki tashi kawai mu gudu muma a domin mu tseretar da Rayuwar mu.”
Cewar Mamman yana ƙoƙarin kamo hannunta.
Kallon sa Ayusherh ta yi kamar wata zararrariya tana girgiza masa kai. Ta share majina tare da miƙe wa tsaye da gudu ta fara dube duben ɗaku nan wai ko zata ga sauran mutanen gidan nasu. Kusan ɗaki biyu ta duba amma babu kowa, har ta fara cire rai ta shiga ɗaki na ƙarshe Mamman na biye da su. Har zata fi ce ganin babu kowa amma sai taji an riƙo ƙafarta ana kiran sunanta.
Da sauri ta duba wurin, sai dai uban kaya ta gani, da mugun sauri ta fara yayyaye kayan ai kuwa ta ke Yayankaka ta bayyana, sai dai ba abin da ya sameta ita. Hankali a mugun tashe Ayusherh ta ce.
“Yayankaka ina Tata yake ina kuma Ali shima yake?.”
Kuka yarinyar ta saki tare da rungumo Ayusherh tana faɗin.
“Nima ban sa ni ba, sai dai an kashe yah-yah (mama)”
Da sauri Ayusherh ta miƙe tare da ɗaukar Yayankaka ta goyata katamau, yayin da shi kuma Mamman ya kamo hannunta da gudu suka baro gidan, hanyar gidan marigayi Arɗo Ayusherh ta nufa, sai dai ganin yadda gidan yake kamawa da wuta ga kuma ƙarar harbi dake ƙara tunkaro su ne yasa, Mamman jan hannunta suka ɗauki hanyar barin garin da gudun tsiya gudu suke kamar zasu tashi sama, zuwa yanzu sun gaji ga Ayusherh dake goye da ƴa ga kuma Mamman da yaji ciwo a ƙafa.
Sun yi nisa sosai har sun kusa kai ƙarshe hanyar da suka ɗauka, suna dab da wani dogon tsauni wanda kogi ne  shirgegen gaske a ƙasan sa.
Kamar an ce Mamman ya juya ai kuwa ya hango ɗaya daga cikin ƴan ta'addan ya saitasu da bindigar sa katuƙar gaske, wani irin zaro ido ya yi tare da sakin hannun Ayusherh, ya matsa tare da ta re su Ayusherh dai dai ɗan ta'addan ya saki harbi. Ai kuwa alburushin bai sauka a ko'ina ba sai a saitin ƙirjinsa. Wani irin baya ya yi yadda kasan an ɗa ga shi sama, ya yi sama tare da faɗa wa ƙasan wannan tsaunin, da sanadin hakan ya sa Ayusherh sakin wani gigitaccen ihu tana duƙawa ƙasa ta ɗauki wani dutsen Marmara ƙarami dake wurin sannan ta ɗa go dai dai ɗan ta'addan ya kuma saitawa zai harbeta ta yi saurin jifarsa da dutsen cikin sa'a ta samesa a goshi ta ke wurin ya fara zubda jini ƙara jifarsa da wani dutsen ta yi wannan karon a hannu ta samesa da hakan ya sa Bindigar dake hannunsa ta faɗi.
Ganin ya faɗi ƙasa ne ya sa Ayusherh saurin ƙari sawa tana leƙen ƙasan tsaunin, sai dai ganin ƙaton kogi da ta yi ne ya sa batasan lokacin da hawaye ya zubo ma ta ba, domin ta tabbata shikenan kuma Mamman ya mutu.
Gudu ta ci gaba da yi cikin tsananin tashin hankali yayin da take ƙara nesa da ƙauyen nata kuma goye da Yayankaka wacce babu abin da take sai aikin kuka, ita ma Ayusherh tana zubar da hawaye na wannan farmaki da ƴan ta'adda suka kawo wa ƙauyen su. Gashi sanadiyar hakan ta rasa Mamman, mman ɗin ta mutum mai muhimmanci a rayuwarta idan a ka ce cire Tata ɗin ta, gashi yanzu bata da tabbaci a kan Tata yana raye ko shi ma waɗan nan ƴan ta'adda sun kashesa, sai dai jikinta yana bata cewar Tata ɗin ta yana raye.
Gudu ta ci gaba da yi babu sassauta wa zuwa lokacin dare ya yi sosai bata dena gudu ba sai da ta tabbata tayi mugun nisa da ƙauyen, sannan ta fara tafiya a hankali zuwa lokacin ta sauke Yayankaka sakamakon gajiya da ta yi, suka ci gaba da tafiya a hankali ga mugun yunwa da ƙishin ruwa da suke ji, ita kam Yayankaka sai faman kuka take yi. Gaba Ayusherh ta gama galaɓaita, a Duniyarta gaba ɗaya batasan da wata wahala makamancin hakan ba duk da ba ta tashi cikin mugun jin daɗi ba, amma a wannan ɗan ƙaramin ƙauyen nasu ta taso a Babban gida, jikar shugaban ƙauyen. Ajiyar zuciya ta ci gaba da saukewa suna ci gaba da tafiyar da su kansu basu san inda suka dosa ba, tafiyar kawai suke yi.
Kamar da wasa kaifafan kunnuwanta suka jiyo ma ta nishi da a hankali da yake fito wa, ta cikin wata gona da suka zo giftawa.
Dakatawa da tafiyar ta yi tare da duban gonar, jin nishin da yafi kama da na wahala yana ƙaru ne ya sa ba tare da tsoro ko fargaba ba ta fara tunkarar cikin gonar yayin da kukan Yayankaka ya tsananta.
Da mugun sauri Ayusherh ta sa hannu tare da ya ye tumin ɓawon masara da take jiyo ƙarar nishin ta ciki.
Wani zaro ido ta yi a kiɗime cike kuma da tashin hankali na ganin waɗan da suke a wurin. Cikin Wata kalar raunanniyar murya a kato na farko da ta yi magana da kalar muryar ta ce.
“Tata, Yâ tâ, Ali!!”
Ta kira sunayen nasu cikin wata kalar murya tana fashewa da kuka.
Jin sunayen da ta kira ne yasa Yayankaka saurin duban su ai kuwa ita ma ta fashe da kuka tana tattaɓo kakar tasu da suke kira Yâ tâ tana kuma kamo Hannun mahaifinta da ɗan uwanta da suma suke dubansu cikin wani irin yanayi.
“Ayusherh dama baku mutu ba.”
Ali ya tambaya yana kuka shaɓe-shaɓe tare da miƙe wa tsaye yana rungumo ta yana ci gaba da faɗin.
“Sun kashe yah-yah waɗan nan azzaluman mutanan kuma mu ma da kyar muka samu muka gudo ni da Yâ tâ (kakarsu ta wurin Uba). Da kuma Tata gashi kuma sun harbi Tata a ƙafa shi ya sa baya iya tafiya.”
Goge hawaye Ayusherh ta yi tana faɗin.
“Na sani Ali sun kashe yah-yah.”
Ta yi maganar tare da tsugunna wa gaban Tata tana hawaye ta kamo hannunsa, yayin da Ali ya taimaka wa Yâ tâ ƴar tsohuwar ta tashi zaune.
“Kiyi haƙuri Ɗiyata ban iya na nemi inda kike ba.”
Cewar Jakadi da kyar yana rumtse ido sakamakon zugi da gwiwar nasa da a ka harba take masa...FOLLOW NKDS @ AREWABOOKS APP.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now