•... 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡Episode 8.
*_AYUSHERH! TA GIRMA 💃 TSAMMACI ABIN DA BA'AI TSAMMANI BA!!🔥_*
..
BAYAN WASU SHEKARU!*Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.*
Kyakkyawar budurwa ce doguwa da tsayinta yake dai dai misali. Tana da dara-daran idanu masu ɗaukar hankali launin meadow green, sai zuba shining suke daga cikin white eye glasses dake maƙale a idanunta da take ɗan lumshewa a hankali tare da buɗe wa. Hancinta dogo ɗan dai-dai da ya zauna kuma ya yi dai-dai da madaidaiciyar kyakkyawar fuskarta. A hankali laɓɓanta mai launi biyu, daga sama ɗan dark-dark yayin da daga ƙasa yake flash pink. Suke ɗan motsawa.
Tsaye take kuma ta yi dress in Combat Uniform na female soldier.
Shirt: Khaki-colored, short-sleeved shirt. Sai Jacket: Khaki-colored, lightweight jacket with epaulets. Sai kuma Trouser: Khaki-colored, combat-style trousers. Tana sanye da Black combat boots. A ƙafafunta.
Tsaye take a tsakiyar Barrack ɗin cikin wannan shigar. Gyara Peak Cap dake a kanta ta yi sannan ta kai hannu cikin trouser pocket nata ta ciro wani farin Handkerchief mai kyau dake fitar da daddaɗan ƙamshi, riƙe Handkerchief ɗin ta yi tare da zuba masa ido tana tuna abubuwa da dama, a koda yaushe idan taga Handkerchief ɗin nan mutane biyu masu matuƙar muhimmanci a rayuwarta da ƙaddara ta yi sanadiyar rabuwar su na har abada take tunawa. Mman ɗin ta da kuma Abyaz.
Murmushi ta yi kana ta fara magana cikin cool voice ɗin ta kuma idanunta a kan Handkerchief ɗin.
"My Mman and Abyaz ɗina, Naso ace both of you kuna raye domin tayani murnar ganin wannan Ranar da zan fara aiki a matsayin Nigerian Army kuma ta musamman, bayan shafe shekaru cikin gwagwarmaya da karatu mai zafi tare da koyon training kala-kala da fuskantar ƙalubale ba adadi, kuma duka na jure har Allah ya nufa na kammala karatuna gaba ɗaya a Military School. Kun san mene ne ya faru daga nan?." Ta yi tambayar sannan ta ɗan yi shiru kamar wacca take jiran amsa, sai kuma ta ci gaba da faɗin. "Potential path to consider na bi, wurin yin Apply for specialized training programs, na tsawon watanni, daga nan kuma bayan wasu watanni na gama cikewa tare da kai ga duk wasu sharuɗa na zama Soja. Briefly dai na zama cikakkiyar Soja da a tashin farko na sama muƙamin Captain bisa ga jajircewata." Ta kai maganar in proud tana ɗa ga kai. Ɗan shuke bakinta ta yi, tana ci gaba da faɗin. "Gashi kuma yau gani tsaye a tsakiyar Barrack ɗin mu a matsayin cikakkiyar Captain kuma ta musamman, kamar yadda nayi rantsuwa a baya domin kare ƙasata da kuma aiki bisa gaskiya da jajircewa, to yanzu ma zan ƙara yi muku. Mamman Mman ɗina nayi maka Alƙawari a kan mayar da hankali wurin aiki da gaskiya domin kawo ƙarshen ira-iren ƴan ta'adda da suka kai farmaki ƙauyenmu har suka zama sila na rabuwar mu ta har abada!. Abyaz ɗin Ayusherh my friend, bestie, souvenir and everything nayi matuƙar kewarka irin sosai sosai ɗin nan har yanzu zuciyata ta kasa yarda a kan cewar ka mutu a wancan hatsarin sai dai yarda da hakan ya zama dole a gareni..." Ta ɗan ja ajiyar zuciya tare da yi ma Handkerchief ɗin kyakkyawar sumba tana ɗan lumshe ido. Haƙiƙa taso Mman tun batasan mene ne so ba, daga baya ta rasa shi, sai kuma ga Abyaz ya shigo Rayuwarta na ɗan lokaci bayan ta tabbatar ta rasa Mman ɗinta na har abada, shima Abyaz ɗin kuma tazo ta rasa shi by accident. Bayan rasa waɗan nan mutane masu daraja da Muhimmanci a Rayuwarta batajin zata sama wani wanda zai maye gurbinsu koma ya kai. Sannan bayan so da ta yi ma kowannensu kuma tazo ta rasa su bata tunanin akwai wani mahaluki kuma da zata iya ƙara so duk da batasan mene ne ƙaddara ta tanadar ba, sai dai koma mene ne batajin akwai sauran gurbi na son wani a zuciyarta.
"Ke nan har abada a haka zaki ci gaba da kasancewa As a single?."
Wani ɓangare na zuciyarta ya jefo ma ta tambayar da ya saka ta buɗe ido da sauri cikin son lalubo amsar. Dai dai lokacin kuma wata soldier dake sanye cikin uniform ta ƙari so wurin da ɗan gudu-gudu tare da tsayawa tana kallon Ayusherh kamar yadda ita ma Ayusherh ta zuba ma ta ido ba tare da ta ce komai ba.
"Jasmine Jasmir."
Ayusherh ta karanta sunan dake gaban rigar jikin Budurwar. Sai dai kafin ta ce wani abu ta jiyo sautin Muryar budurwar tana faɗin.
"Hello! i am Jasmine Jasmir, Second Lieutenant (2LT) yau ce rana ta ta farko a aiki."
Ta yi maganar tana miƙa ma Ayusherh hannu kuma fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi mai bayyana haƙora.
Ita ma Ayusherh ta miƙa ma ta nata Hannun tana amsa ma ta da faɗin. "Hello! I am Ayusherh Tata, Captain (CAPT), ranar farko a aiki."
Murmushin Soldier ɗin mai suna Jasmine ya faɗaɗa, tana duban three star's dake jikin rigar Ayusherh ta shouldernta sannan ta ce.
"Woww Babban muƙami haka tare da kyakkyawar soldier kamar ki, gaskiya hakan ya yi 100%."
Ta kai maganar tana haɗe yatsarta manuniya da kuma Babbar.
Ɗan murmushi ta yi kana ta ce.
"Thanks."
Jasmine ta ce.
"Nevermind Dear, can we be friends?."
Ayusherh ta ɗan ƙara girman idanunta tana faɗin. "Why not."
Cikin murna kamar ba Soja ba Jasmine ta ce. "Many thanks Captain, daga yanzu mun zama abokai, nayi farin ciki da hakan, sannan naji daɗin haɗu wa dake dan nasan zan ƙaru sosai dan na fahimci kina da kirki."
Ayusherh tana ƴar dariya ta ce. "Ooo ke nan ke bashi da shi Kirkin?."
Jasmine ta ɗan zaro tana faɗin.
"I have no word Captain Kawai ko ma ina da shi ko babu a ƙawancen mu zaki gane."
"Good." cewar Ayusherh sannan ta ƙara da faɗin. "Ofishin General nake nema ko zaki iya nunamin?."
"Laaa ai nima ɗin can na nufa, muje kawai."
Jasmine ta amsa ma ta da faɗin hakan sannan suka nufa hanyar da Jasmine ta nuna suna fira Jasmine sai fira take zuba ma ta kamar dai ba Soja ba, sai ta zama kamar wata ƴar gidan radiyo a wurin Ayusherh a ɗan wannan taƙin.
Fitowa suka yi daga elevator da suka hau dai dai Ayusherh ta sawo kai domin fita taci karo da soldier ɗin dake ƙoƙarin shiga elevator ɗin ita ma sanye cikin Uniform sai dai ya babanta da nasu.
"Am so sorry..."
Matar ta kasa ƙari sa maganar da ta ɗauko sakamakon ɗa gowa da Ayusherh ta yi tana dubanta, su kayi ido huɗu.
"Sorry ban lura ba ne."
Ayusherh ta faɗa ganin yadda Matar ta zuba ma ta ido. "Kece Aysherh ko? Ahm ina nufin Captain da zata fara aiki a yau?."
Matar ta tambaya cikin murmushi. Da sauri Ayusherh da Jasmine suka kalla juna bayan kowannen su ya ga sunan dake jikin rigar soldier ɗin tare kuma da muƙamin ta. Cikin girmamawa Ayusherh ta ce. "Yes Sir! Dama office ɗin ki muka nufo tare da Jasmine."
(Kun dai san Sojoji mata ba'a kiransu da Ma ko kuma Madam a wurin aiki ba, sai dai Sir...😃)
"Okay, Follow me."
General Lamrat Jabir Junaid ta yi maganar tana juyawa bayan taji abin da Ayusherh ta faɗa.
Kallon juna Ayusherh da Jasmine suka yi sai kuma a tare suka saki dariya mara sauti kowaccensu tana toshe baki.
Cikin raɗa-raɗa Jasmine ta ce. "Da alama ba mai zafin kai ba ce."
Murmushi Ayusherh ta yi, bata ce komai ba sakamakon office ɗin General ɗin da suka ƙari sa, ta nuna musu wuri suka zauna bayan ta zauna.
Dama da jimawa file ɗin Ayusherh ya isa gareta matsayinta Na General kuma hasali ma sune suka buƙaci Ayusherh ta yi aiki a Barrack ɗin nasu sakamakon jarumtarta da suke samun labari akai. Kafin yau basu taɓa haɗuwa da Ayusherh ba. Iyakar saninta da General ta yi, shi ne a photo, to sai ashe ganinta a zahiri ya fi jin labarin ta.
Sosai General ta ƙara yi musu bayani akan aikin yadda zasu fahimta duk da sun yi training na watanni sai dai ta ƙara musu da nata bayanin da kuma jan hankali. Bayan nan da kanta ta kai Ayusherh office ɗin dayake mallakin Ayusherhn matsayin ta na Captain yayin da Jasmine da take da muƙamin Second Lieutenant zata ke aiki a ƙarƙashin ta da kuma sauran Jami'an sojojin da General ta ce zuwa gobe kowa zai hallara gabanta domin ta sansu.
Daga haka ta bar office ɗin Ayusherhn zuwa nata.
Ai kuwa kamar jira suke ta fita Ayusherh da Jasmine suka rungume juna suna sakin ihun murna. Sai kuma Jasmine ta ja baya da sauri tana faɗin.
"Sorry Captain."
Ta faɗa, tuna cewa Ayusherh a samanta take.
A karo na farko Ayusherh ta yi Murmushi mai bayyana haƙora tana maimaita abin da Jasmine ta faɗa cikin magana da hanci da hakan ya sa Jasmine darawa tana faɗin.
"Atoh gudu nake kar nayi wani laifi a rana ta ta farko a aiki, shi ya sa amma ai muna barin wurin aiki zamu ci gaba da kasancewa ƙawaye yayin da a ka dawo fagen aiki kuma ke ɗin ta gaba dani ce kuma ina girmama hakan."
Girgiza kai Ayusherh ta yi tana ɗan zura hannu a aljihu ta ƙari sa wurin da kujerar zamanta take, ɗan dafa kujerar ta yi da hannu guda tana fuskantar Jasmine ta ce.
"Wai bakyajin wani proud haka dai kasancewar yau ce ranar ki ta farko a aiki?."
Ta yi ma ta tambayar tana kallon ta fuskarta da ɗan murmushi, sai dai ganin yadda lokaci guda fuskar Jasmine ya sauya daga murmushi zuwa yanayin Alhini ya sa ta ce. "Sorry in bakiji daɗin tambayar da nayi miki ba."
Ayusherh ta faɗa tana ƙari sawa wurin Jasmine ɗin tare da dafa kafaɗarta.
Girgiza kai Jasmine ta yi tana faɗin.
"A'a ba maganar ki ba ce ta sakani a wannan yanayin, kawai wani abu na tuno."
"Ayya. Sorry, kiyi haƙuri in sha Allah koma mene ke damunki zaki sama mafita da yardar Allah."
Thanks kawai Jasmine ta iya faɗa, tana tuna yadda iyayenta basu goya bayanta a kan burinta na son zama Soja ba. Hatta yau bayan ta shirya da ta zo yi musu sallama. Mom ɗin ta sai cewa ta yi. _"Jasmine kije kiyi aikin da kika zaɓarwa kanki, amma ki sa ni kar daga ƙarshe ki dawo gareni da kuka, na faɗa miki."_ Ajiyar zuciya Jasmine ta sauke. Sai kuma ta yi murmushi tana faɗin.
"Ya kamata mu a je photo na tarihi a ranar mu ta farko a aiki."
Ta faɗa tana ciro wayarta, ta shiga yi musu pictures ita da Ayusherh da ta biye ma ta suna ta yi cikin nishaɗi, har shi kansa office ɗin Jasmine bata kyale ba shima sai da ta ɗauke shi hotuna iri -iri Ayusherh sai dariya take ma ta tana faɗin.
"Ni kam da ace bada Uniform na sojoji na ganki ba, to fa kai tsaye da ma'aikaciyar gidan rediyo zan kiraki."
Dariya kawai Jasmine ta yi tana faɗin. "Kamar kuwa kin sa ni. Burin Mom ɗina ke nan zama Hakan sai dai na wa burin ya sha banban da nata, ah to ya ta iya ta haɗu da ƴar zamani, bata sama cika burinta ba a kai na. Hummp a ƙarni na ashirin da huɗu fa muke normally, da hakan zamani ya zo dole muma bimu a jera da mu, but a cikin ƴaƴana zan yi ƙoƙari ɗaya ta cika ma ta Burin..."😅
Gaba suka yi dariya. A kusan haka kusa ƙarar da wannan taƙin. Kafin suka sama sanarwa na Meeting da General ta haɗa ga sabbin sojoji, sannan ne suka bar office ɗin domin halartar taron.....FOLLOW MY ACCOUNT NKDS @ AREWABOOKS APP.

YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...