CAPTAIN AYUSHERH...2

16 1 0
                                    

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
                                   https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
       
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡

Don't Forget To Follow My Both Accounts;
Nainarhkd3 @Wattpad.
Nkds @Arewabooks.
..

Episode 2.

A cikin dare kuma suka sama baƙon cin waɗan nan gawurtattun ƴan ta'adda da suka farma ƙauyen da mutanen cikinsa. Ƙauyen yana a dab da Iyakr  Nigeria da kuma Cameroon ne.
..
Basu kyale kowa ba sun kashe mutane da dama yayin da suka raunata da yawa daga cikinsu. A lokacin Matar da ta faɗa masa ita ɗin General ce tana jinyar jikinta bayan an samu an cire wuƙar da a ka caka ma ta ne a yayin da a ka biyo ta.
Duk iya kar ƙoƙarin Jakadi wurin ganin ya taimaka ma ta ta tsira daga hannun waɗan nan mugayen ƴan ta'adda abin ya cutura yanaji yana gani ta mutu shima ɗin da kyar ya tsira a hannunsu tare da wannan Jaririyar da ya ɓoye bai bari komai ya sameta ba, sai dai shi kam ya sha wahala ba kaɗan ba, domin sun sassareshi a baya wurare sun kai huɗu. Bayan guduwa daga gare su ne har Allah ya nufesa da ƙari sowa ƙauyen su har zuwa yanzu da yake tuna komai turyan turyan. Ƙasa da awa arba'in da takwas komai ya faru.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana duban Jaririyar da ta yi shiru kuma har yanzu idanunta a buɗe suke tamkar mai wayo. Yana sane da yadda tun da a ka haife ta bai ji ta yi koda irin wannan kuka da jarirai ke yi ba. Kuma abin ya ɗaure masa kai sai dai ya ƙudurta ba zai bar komai ya sameta ba zai tsaya da ƙarfinsa da jajircewarsa wurin ganin ya kula da ita har ta kai Matakin da Mahaifiyarta take so a Rayuwa zuwa nan kuma shi kansa bai san mai zai faru ba. Abin da ya sa ni, shi ne zai yi ƙoƙari matuƙa wurin koya ma ta duk wani abu da ya da ce ba kuma zai bari ta yi maraici ba, zai zama uwa kuma uba a gare ta, sannan kuma Gatanta. Yana da dalili na kawo ta cikin ƙauyen su domin anan ne yake da tabbacin Rayuwarta bata a cikin hatsari, zai ci gaba da zama anan tare da ita, har zuwa nan da ɗan wani lokaci kafin ya koma da ita Nigeria ya sakata a Makarantar sojoji.  Wannan shi ne tsarin sa a yanzu.
Duk ya gama ƙudurce hakan a ransa ba tare da ya san me ce ce abin da ƙaddara ta tanadar ba a gare su baki ɗaya.
Haka ya kwana a zaune riƙe da Jaririyar nan da ya yi ma laƙabi da Ayusherh kamar yadda Mahaifiyarta ta so.
Washe gari koda Mahaifiyarsa tsohuwar arziƙi ta yi masa magana a kan Jaririyar da neman yardar sa a kan ya bata ta kula da ita zuwa lokacin da zai ƙara Aure domin naimawa Ayusherh uwa don shi ɗaya ba zai iya rainonta ba.
Jakadi bai ƙi ba domin ya san wacece Mahaifiyar tasa Mace ce da ta yi daban da saura. Sai dai tsoronsa ɗaya yana gudun kar Ayusherh ta taso da al'ada irin nasu da kuma addini duk da yanajin ba zai bar hakan ta kasance ba, koda kuwa hakan zai zama sila na Rayuwarsa.
Ya ƙudurce abin da zai yi domin gina Rayuwar yarinyarsa Ayusherh ta taso cikin inganci da burgewa.
Koda a ka tambaye sa mene ne sunan Jaririyar sai ce musu ya yi sunanta CAPTAIN! To da yake basu san mene ne ainihin ma'anar sunan ba, hakan ya sa suka yi ta yaba sunan kuma sunan ya kama bakin kowa kamar yadda Yarinyar ta shiga ran kowa. Sai dai fa duk kwakwazon mutum sai dai ya yi ya gama. Jakadi baya bari koda wasa Hannu ma ya kai ga Ayusherh da a ke kira da Captain, wai domin a taɓa ta, sai dai kallo, shima kuma daga nesa nesa. Ban da Mahaifiyarsa wato Mahtah baya taɓa bari wani daban ya ɗauke ta, to sai Arɗo shima da dai bawai don ya so ba, dan kuwa tsakani da Allah yana tsoron hali irin nasu, kar suyi ma ta wani abu dalilin bijire musu da ya yi a baya.
Tun Ayusherh tana Jaririyar ta Jakadi ya kan goya ta, ya ɗauke ta, ya shiga daji farauta da ita a haka, tun Mahtah tana faɗar a kan hakan har ta haƙura ta zuba masa ido.
Jakadi yana da watanni Biyar da dawowa ƙauyen, zuwa lokacin kuma Captain ta daɗe da fara zama har tafiya take ƙoƙarin farawa abin nata yana bawa kowa mamaki. A lokacin ne kuma a ka kawo masa wata magana a kan wai ya Aure Babaya ɗiyar Arɗon yanzu, wai ko dan Ayusherh ta sama uwa da ta rasa.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya ce musu shi kam baya da ra'ayin Aure a  lokacin, kuma koda zai yi bayajin zai iya auren Babaya. Yarinyar da bata haure shekaru goma sha uku ba a lokacin, wai kuma a hakan ita ce ƙatuwar budurwa a ƙauyen.
Badan ransu yaso ba suka haƙura da zancen sai dan basa so wani abu ya gifta da zai yi sanadiyar sake barinsa garin, wannan dalilin ya sa ko ibada basa iya hanasa.
Haka Rayuwar take gudu yayin da Ayusherh take ƙara girma tana ƙara wayo kuma kyawun ta da kuma asalin kalan idanunta suna da ɗa bayyana, da kuma wata ɓoyayyiyar baiwa dake gare ta.
Idanunta wasu kalar Meadow Green ne da basa tashi komawa Green color har sai dare ya yi, yayin da idan kuma rana ce sai dai su kasance su ba grey ba sannan kuma ba blue ba, su dai gasu nan ne tsaka tsaki gunin ban sha'awa.
Har wa girman Ayusherh Mahaifin ta Jakadi bai dena zuwa da ita daji ba, idan zaije farauta kodai wani abun shi ya sa kuwa Ayusherh ta taso bata da wani wuri sai daji tun tana da shekaru goma sai ta ɗauki kwari da baka, ko wani abun na farauta, sai ta ce za ta tafi daji ta yi farauta kamar yadda Tata (It mean Father.) ɗin ta yake yi, kuma duk yadda a ka yi da ita, a kan kar ta je, to fa ƙi take yi, domin Ayusherh ta taso ne wata iriyar jarumar Mace da ba komai ne kasafai yake bata tsoro ba akwai ta da dakakkiyar zuciya.
BAYAN WASU SHEKARU.
Zuwa yanzu sai dai a ce Alhamdullilah, domin kuwa abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da Musulunta na da yawa na daga cikin mutanen ƙauyen su kayi, har shi kansa Arɗo tsoho da sabon ma da iyalansu, sai ya zamana ilimin addini ya yawaita a ƙauyen, a hankali, a hankali kuma mutanen ƙauyen dama makwabtan su suna ta tururuwar shiga addinin Rahma Addinin Musulunci.
A lokacin da Ayusherh ta kai shekaru Biyar ne kuma a ka samu Jakadi ya Aura Babaya, bayan an sha fama da shi da kyar ya aminta, dama ita ta ce bata da miji sai shi, kuma sanadin hakan ne ma a lokacin Babaya ta karɓi addinin Musulunci. Ƙarin abin ya ja hankalinsa i zuwa auren ta shi ne tsananin so da kulawar da take yiwa Ayusherh, Shalelen sa.
A halin yanzu Ayusherh tana da shekaru goma ta sha biyu a Duniya. Ta kasance ta taso ne wata kalar Mace da halayenta da ɗabi'unta suka sha banban da na sauran yaran ƙauyen, takan ware kanta taje saman wani ƙaton dutse dake kusa da katon tafki na garin, duk girman dutsen nan bata gani, haka take hawa ta zauna, wani lokacin kuma sai dai ta yi ta hura sarewa da Arɗo ya taɓa ma ta kyautarsa, yayin da wasu lokutan kuma sai dai ta zaune ta yita magana da Aku (Parrot.) nta da ta samu sanadin yawon farauta a daji.
Jakadi ya yi matuƙar ƙoƙari sosai wurin ganin Ayusherh ta sama duk wata kulawa da tarbiyya da ya kamata dai dai gwargwado, ya yi ƙoƙari ta wannan fannin kuma Babaya da a halin yanzu yaranta biyu, Mace da Namiji, Namijin ne Babba sai mai bi masa mace mai suna Yayankaka. Sosai Babaya take kula da Ayusherh kuma kamar ƴa ta ɗauke ta ba cuta ba cutarwa. Kuma hakan ya samo asali ne bisa jajircewar na Jakadi. Domin shi da ka taɓa Ayusherh, Shalelen sa, gwara shi ka taɓa sa.
A Rayuwar Ayusherh ba abin da tafi so sama da shiga daji yin farauta, kuma a yanzu bata da wani Babban buri da ya wuce ta shiga wani gasar takobi da a ke yi duk bayan shekara a ƙauyen, tsakanin Samarin ƙauyen majiya ƙarfi, da kuma Samarin ƙauyen dake makwabtaka da su. An saba a kan yi wannan Gasar ta takobi duk ƙarshen shekara kuma a kan fidda gwani wanda ya zama nasarar zuwa na ɗaya. To Ayusherh bata da wani buri da ya wuce shiga wannan Gasar idan lokaci ya yi duk da bata da tabbacin Tata zai barta, sai dai zata dage wurin roƙonsa domin ya aminta.
Yau ma kamar kullum tana sanye ne da kayanta na saƙi irin na shiga farauta...FOLLOW NKDS @ AREWABOOKS APP. GET IT ON PLAY STORE. DOWNLOAD ON THE APP STORE.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now