CAPTAIN AYUSHERH..6

6 0 0
                                    

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
                                  
       
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡

Don't Forget To Follow My Both Accounts;
Nainarhkd3 @Wattpad.
Nkds @Arewabooks.
..

Episode 6.

Yanzu kuma Ali da Yayankaka ne suka haɗa baki wurin faɗa.
Girgiza kai kurum Tata ya yi dan shi ya sa ni Ayusherh ba zata iya ba! Ina ai da sauran ta, ƙarfinta bai kai nan ba.

.
“Yarinyata akwai ki da taurin kai.”
Tata ya faɗa, yana ƙoƙarin hawa bayan nata. Ita ko Ayusherh har da cicciɗa shi lokacin da ya hau. Kamar da wasa ta taƙarƙare ta fara taku da Tata a bayanta an yi ɗaya, biyu, ana ukun ne gaba ɗayansu daga shi har ita suka yo ƙasa sakamakon ƙafarta da ta gurɗe.
Ai kuwa Ali da Yayankaka mai zasuyi da ya wuce dariya.
Ita dai Yâ tâ abin kunya ma ya bata, girgiza kai ta yi, ita tasan kaɗan ke nan daga aikin Ayusherh Yarinyar akwai kafiya, ita ta raineta saboda haka ta santa ciki da waje.
“Wayyo! yi haƙuri Tata ƙafata ce ta gurɗe amma zan kiyaye Bara na taimaka maka ka tashi mu ci gaba da tafiya.”
Cewar Ayusherh a lokacin da ta miƙe tsaye a ƙoƙarin ta na taimaka masa ya miƙe take wannan maganar.
Cikin nutsuwa Tata ya ce.
“Kin ga samomin sanɗa mai kyau da kuma kwari kawai da zata taimaka min wurin tafiyar.”
Ya faɗa lokacin da ya samu ya tashi zaune.
Amsa wa Ayusherh ta yi nan ta fara duba wurin da zata sama irin sandar da zata masa dai dai. Ta kuwa ci Sa'a ta samu, dawowa wurin ta yi tare da ba shi sannan ta taimaka masa ya miƙe tsaye da taimakon wannan sandar ya fara taka wa duk da haka Ayusherh tana taimaka masa.
Yâ tâ da ɗan sauran gwarinta da kanta take taka wa haka suka fara tafiya, sai da suka yi doguwar tafiya sannan suka isa ƙauyen da Ayusherh ta hango. Ruga ne ma kuma ta Fulani. Kuma koda jin abin da ya samesu Fulanin da yake na kirki ne sun matuƙar tausaya musu sosai kuma sun basu wurin zama, sannan ne a ka sama wanda ya duba ƙafar Tata bayan sun basu abinci sun ci, da yake tun a hanya sun yi salla ta hanyar taimama.
Kwanakin su Ayusherh biyar a wannan ruga zuwa lokacin ƙafar Tata ta warke sai dai ba ya iya tafiya har sai da sanda domin ba duka ya gama warware wa ba.
A lokacin ne kuma suka fara shirya-shirye na ci gaba da tafiyar zuwa Nigeria. Sosai suka yi ma waɗan nan Fulani godiya da halaccin su a gare su kafin suka ɗauki hanya da su kansu basu san Ranar isa ba.
***
Sun matuƙar shan wahala fiye da tunani ga yunwa da ƙishirwa domin guzurin da suka yi ma ta ƙare amma haka suka daure suke ci gaba da tafiya duk ƙauyen da suka gani za su ɗan tsaya su huta na ƴan kwanaki idan mutan ƙauyen sun tarbe su da ban girma matsayinsu na baƙi kuma matafiya.
Daga ƙarshe dai a hanyar su na tafiya suka haɗu da wasu mutane suma masu tafiya amma saman raƙuma, su ne suka taimaka musu suka shiga dasu har ƙasar Nigeria a kan raƙumansu.
To a ƙasar ma sun sha garari wuri wuri daji daji kafin Allah ya sa suka tsaya a wani ƙauye cikin jihar Taraba Mutanen ƙauyen sun haɗa da Fulani da kuma ƴan kabilarsu sai dai Fulani sun fi yawa, sun tarbe su cikin mutumci kuma Tata ya yanke zasu ɗaura da sabuwar rayuwa a ƙauyen har zuwa lokacin da zai sama wani abu mai gwabi su shiga cikin birni domin ya saka Ayusherh a makaranta, kuma su fara sabuwar rayuwa. A taƙaice dai yanzu suna a ƙauyen mai suna Mayo-Danay, kuma lokaci ƙanƙani suka saba da mutanen ƙauyen rayuwarsu ta fara komawa kamar baya. A halin yanzu Shekara guda ta wuce. Ayusherh ta kasance matashiyar jaruma wurin shiga daji domin farauta a kaf ƙauyen ba kamar ta a cikin ƙananun shekarunta da ba zasu haura Goma sha Uku ba.
_Note: Mayo-Danay ya kasu kashi biyu ne, akwai a ƙasar Cameroon wato ƙauyen su Ayusherh. Akwai kuma a ƙasar Nigeria jihar Taraba wato nan inda su Ayusherh suka sauka._
..
AYUSHERH
Baya ta yi, sannan ta yi ƙasa da gwiwarta ɗaya, ta rage girman idanunta tare da sakin kibiyar dake hannunta dai dai wurin da ta saita.
Kibiyar ta ratsa ciyayun masu tsayi dake wurin ta nufe abin harin da Ayusherh ta saita da mugun sauri, wani irin zaro ido ya yi tare da yin ƙasa da sauri, hakan ya sa kibiyar bata samesa ba ta sauka a kan bishiyar dake wurin.
Wata kibiyar Ayusherh ta ƙara cirowa zata saita wurin da ya tsugunna dai dai shi kuma ya sa hannu tare da ya ɗan yaye ciyawar dake basa kariya ke nan ya ga abin da take shirin yi da sauri ya miƙe tsaye cikin zaro ido yana faɗin.
“No! Please don't...”
Ya yi maganar yana ɗa ga hannu tamkar dai yadda ɓarayi ke yi in sun shiga hannu, to shima hakan ya yi, yana mai fara taka wa zai ƙari sa inda take.
Ayusherh bata sauke kibiyar ba, kuma bata dena saita shi ba, har sai da ya gama fitowa daga maɓoyar nasa gaba ɗaya ya fara taka wa zuwa inda take a ɗan dake.
Ita kuwa a karo na farko ta kai dubanta ga fuskarsa domin da fari da yake maganar ko dubansa batayi ba, lokaci ɗaya kuma tana ƙoƙarin magana cikin harshen fulatanci da zuwa yanzu ta gama kwarewa sai dai me?... Wani irin abu taji tun daga ƙwaƙwalwar kanta ya tsarga har ƙafafunta sakamakon ido huɗu da suka yi da shi, ba wai haɗa ido da suka yi ba ne ya jefata cikin wannan yanayi, a'a fuskarsa ce sanadi, fuskarsa da ta gani ne ta yi matuƙar rikita tunanin ta.
Da wani irin sauri ta miƙe tsaye cikin rarrabewar murya take ƙoƙarin magana da kyar ta fisgo kalmomi ta tattara tare da kiran sunansa da faɗin.
“Mamman!.”
(..😳😳..)
Ta yi maganar ne cikin wani irin yanayi tana kuma ƴar dariya jerarrun haƙoranta farare suka bayyana, da sauri ta fara taka wa domin ƙari sawa gare sa. Yayin da shi kuwa ya tsaya cak da tsananin mamaki ganin lokaci guda Mafarauciyar Yarinyar dajin dake ƙoƙarin farmakinsa ta dakata daga ganin fuskarsa har take kiransa da wani suna da bai taɓa sanin akwai sa ba sai yanzu. Fuskarsa da alamar mamaki ya saki baki yana dubanta.
“Mman ɗina dama baka mutu ba?.”
Ayusherh ta yi Maganar cikin wani irin yanayi na zallar zumuɗi, lokacin da ta ƙari sa garesa ta sa hannu tare da shafa fuskarsa tana ci gaba da faɗin.
“Nayi kuka sosai a wancan lokacin saboda a tunanina shikenan Abokina Aminina sannan ɗan uwana Mman ɗina ya mutu! ashe ba haka ba ne kana raye..”
A yanzu ta yi maganar ne gaba ɗaya fuskarta a washe tana zare manyan idanunta saman fuskarsa.
“Ka sauya da yawa sosai fa!.”
Ta faɗa tana duban yanayin fatarsa da ta kasance wata kalar ja jajur ɗin nan, gashi da ka gansa kasan hutu ya zauna ba ƙarya...FOLLOW MY ACCOUNT NKDS @ AREWABOOKS APP.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now