•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 21.
“Ba zai yiwu ba!.”
Uncle ya faɗa a tsawa ce yana ci gaba da faɗin.
“Ya zama dole Abaan ya bar aiki a ƙarƙashin Nasamu muddun ba so kake mu rasa shi ba.”
Uncle ya ƙare maganar a zafafe yana juyowa tare da duban Arham da ya harɗe hannu a ƙirji tun bayan gama faɗa masa halin da ake ciki da ya yi.
Arham ya ɗan waro ido ya ce.
“To ta ya ya ke nan hakan zata yiwu bayan kuma already ya fara aiki a gidan nashi kuma yau ne yaje a domin ya yi masa interview domin ɗaukarsa aiki a ɗaya daga cikin company's ɗin sa.”
“Ba zaka gane abin da nake hangowa ba Arham saboda Nasamu ya wuce duk tunanin mu tantirin Tantiri ne na san zai yi tsatstsauran bincike a kan Abaan kuma zai gano daga gidan marayun da ya fito, daga nan kuma ba zai tsaya haka ba dole bincikensa zai kai sa zuwa wurin da bamu buƙatar ya kai domin muddun ya kai wurin to fa tamkar asirin mu ne ya tonu.”
Arham ya fesar da zazzafan huci yana ɗan gyaɗa kai ya ce.
“To mene ne abin yi ?.”
“Abin yi shi ne kawai kasan duk yadda za kayi ka hana Abaan komawa gidan Nasamu balle har ya kai ga fara aiki a Companyn sa.”
“But..”
Katse Arham dake yunƙurin magana Uncle ya yi sannan ya ce.
“Nasan mai zaka ce kana tunanin Nasamu zai yi zargin wani abu ba?.”
Jinjina masa kai Arham ya yi bai iya cewa komai ba.
Uncle ya saki murmushin takaici ya ce.
“Karka damu zamuji da lamarin.”
Yana faɗin hakan ya taka ya isa wurin Bene dake a gefe cikin Ɗakin matattakalan benen ya taka ya yi sama sannan ya fito daga Ɗakin ƙasa da suke ciki. Arham ya sake furzar da iska sannan ya bi bayansa.
Tun bayan baro Prison ɗin da suka yi da fari Arham ya nufa Gidan marayun amma Uncle ya hanasa tare da yi masa kwatancen nan inda suke sannan suka ƙari so anan ne Arham yake sanar da Uncle tsiraru daga abubuwan da suka faru bayan kasancewarsa a gidan kaso na tsawon shekaru goma sha Tara.
Fitowa suka yi daga ƙaramin gidan da ya fi kama da gidan gona kai tsaye hanyar da zata sadasa da gidan marayun Arham ya miƙa lokacin da suka shiga motar. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙari sa da su gidan marayun a nan tare da shugaban dake kula da gidan marayun Arham ya bar Uncle yayin da a gaggauce ya wuce zuwa Ɗakin sa da yake a ɓangaren maza samari kamarsa.
Da sauri ya faɗa Ɗakin yana dafe kansa dake mugun sara masa, ƙam ya riƙe kan nasa ya tsaya a tsakiyar Ɗakin har yanzu juwa bata sakesa ba, kuma ba komai ne dalilin hakan ba sai tuno abin da ya faru da shi a shekarun baya da ya yi, da irin kisan wulaƙanci da Nasamu ya yi ma Mahaifansa a gaban idonsa take komai ya fara dawo masa a kai tirya-tiryan.
_Flash Back._
_“Ki yarda dani Yarinyar nan ta zama ruhi da ɓargo na yaronmu bakiga yadda ya zama ba daga baro garin da muka yi ba?. Ya kamata ki fara shiri tun yanzu dan da alama yaron naki da gaske yake.”
Dad ya yi maganar yana ɗan waigawa ya dubi Mom dake zaune a kusa da shi a gidan baya na motar.
Mom ta saki murmushi cikin annashuwa ta ce.
“Ai ko da zan fi kowa farin ciki idan hakan ta kasance domin na lura ita ma Yarinyar tana da feelings a kan sa.”
Abyaz dake zaune gidan a gaba na motar kusa da driver ya ɗan juyo yana kallonsu fuska tab da walwala ya ce.
“Dad and Mom to tun da kun lura da haka ai kawai mu juya kawai a ɗaura mana Aure sai mu taho tare da ita ko ya kukace kun ga daga nan kuma kun sama ɗiyar da baku da ita.”
Ya yi maganar yana dariya. Mom ta yi masa daƙuwa tana faɗin.
“Ungo naka wai Abyaz yaushe ka zama haka ne.”
Dad yana dariya ya ce.
“Ai da gaskiyarsa saboda haka ina ga abi shawarsa kawai mu juya.”
Gaba ɗaya suka yi dariya shi da Abyaz yayin da Mom ta yi kicin-kicin tana faɗin. “Yaushe kuka taɓa jin an yi haka? Ai shi Aure ba'a masa haka, kuma ma ai Abyaz ɗina ba yanzu ba tukunna...”
“Ai kuwa Mom da alama so kike in na koma Military School na kasa taɓuka komai.”
Abyaz ya yi gaggawar faɗan hakan yana dariya.
Maganar da Mom take yunƙurin yi ya katse a sakamakon mummunar karo da motarsu ta yi da wata Truck. Ko kafin ɗaya daga cikinsu ya sama zarafin wani yunƙuri motar ta yi sama da su sannan tayo ƙasa a karkace duk suka koma sama ta ƙasa.
Kafin kowannensu ya kai ga tunanin abin da ke afkuwa a duniyarsa motar ta fara gungure da su bata tsaya ba sai da ta sadu da wata bishiya sannan motar ta tsaya. Tuni duk sun fi ce daga hayyacinsu yayin da tuni driver rai ya yi halinsa. Sakamakon mummunar buguwa da ya yi.
Abyaz da bai wani bugu sosai ba sai kansa da ya bugu jini ya wanke masa fuska ya samu da kyar ta ƙuƙuta ya fito daga motar yana dafe kansa tare da isa ta saitin wurin da Iyayen nasa suke ya fara kiran sunansu cikin fitar hayyaci sai dai cikinsu ba mai amsa masa, sai can Dad ya ja wata doguwar ajiyar zuciya sai dai duk yadda ya so ya fito daga motar gagara ya yi a lokacin ne kuma hankalinsa ya kai kan Mom da bata numfashi cikin razana ya kai hannunsa dai dai saitin hancinta sai dai ba alamar numfashi a tattare da ita, bai fita daga wannan tashin hankali ba ya fara jin ƙarar taku yana isowa dab da su a razane ya kalla Abyaz dake durƙushe riƙe da kansa da har lokacin jini bai dena zuba ba.
“Yarona tashi ka gudu!.”
Abyaz ya ɗa go cikin razana da jin kalaman da Dad ya yi, sai dai kafin ya sama zarafin magana Dad ya ƙara da faɗin.
“Mahaifiyarka ta riga da ta mutu nima kuma nasan ba za su barni a raye ba saboda haka rayuwarka tana da matuƙar muhimmanci shi ya sa nake cewa ka gudu Abyaz!!.”
Dad ya ƙare maganar cikin azaba da kyar ya samu a hakan yadda yake sama a ƙasa ya lalubo briefcase ɗin sa da kyar ya samu ya jefa waje ya ce ka riƙe wannan zatayi maka amfani anan gaba kuma ita zata taimaka maka wurin sanin wanene wanda yake da alhaki a duk wannan.”
Dad bai ƙare maganar ba yaji takun da yakeji yana ƙara isowa dab da su. A raunace ya kalla Abyaz dake rungume da briefcase ɗin da alama ya kasa yarda da abin da yake faruwa a ce cikin ƙanƙanin lokacin da bai haure minti biyu ba gaba ɗaya rayuwarsa ta karkace ta koma zuwa upsidedown.
“Ka tafi Abyaz!!!.”
Shi ne kawai abin da Dad ya iya furta wa sai dai kafin ya kai ga ƙare maganar wasu irin jibga-jibgan ƙosassun maza je masu ƙira da yanayi irin na samudawa suka bayyana su huɗu suka zagaye motar kuma a cikinsu drivern Truck ɗin da ya bige motarsu Abyaz yake.
Ko kafin Abyaz ya yi wani yunƙuri domin ceton ransa wani irin hayaƙi ya turniƙe wurin kafin Mutumin ya bayyana yana busa sigarin kallo ɗaya zakayi masa kasan ba ƙaramin tsagera ba ne.
“Nasamu!”
Maganar Dad ya dawo da Abyaz hayyacinsa Mutumin ya saki wani lalataccen murmushi ya juya ido tare da duban Abyaz da ilahirin jikinsa ba inda baya rawa, ai take Abyaz ya fara ja da baya sai dai tuni biyu daga cikin waɗan nan garɗa-gaɗan mazan suka rirriƙeshi suna ƙoƙarin gwace briefcase ɗin hannunsa.
“Nasamu, muddun wani abu ya sama yarona to fa ba zan taɓa kyaleka ba...”
Fiuuu! Kakeji fitar harsashi daga jikin ƙaramar Bindigar dake hannun Mutumin da Dad ya kira da Nasamu, kwaf ɗaya harsashin ba tare da saɓa saiti ba ya fasa kan Dad ya shige. Ɗiff!! wutar Abyaz ya ɗauke yayin da gaba ɗaya duniyarsa ta tsaya cak, sakamakon abin da ya faru, da wani irin ƙarfi ya gwace kansa daga riƙon da waɗan nan mazan suka yi masa ya ƙari sa gaban motar yana jijjiga Dad da babu rai a tattare da shi, tsaban tashin hankali muryarsa ma bata fitowa. Cikin wani irin zafin nama ya miƙe tsaye tare da daka tsalle ya kai ma Nasamu wani naushi a ido a ka ci sa'a kuwa zoben hannunsa ya yi ma idon illa sosai, wafce briefcase ɗin dake hannun Nasamu ya yi tare da shammatar Mazan majiya ƙarfi ya fara gudu gaba ɗaya suka bi bayansa, yayin da Nasamu ya zube a wurin yana zuba ihun da ya amsa a gaba ɗaya dajin yana kuma dafe da saitin idon nasa da jini ke fita.
Duk yadda waɗan nan maza majiya ƙarfi suka so su kama Abyaz abin ya ci tura domin yaron wani irin ƙarfi ne na ban mamaki ya zo masa domin har jima biyu daga cikinsu, mummunar rauni a fuska ya yi, suna tsaka da haka wata mota ta sha gaban Abyaz hakan ya sa ya tsaya cak, cikin sadaƙarwa dai dai lokacin kuma ɗaya daga cikin waɗan nan mazan ya ƙari so ta bayansa tare da buga masa bayan bindiga a kai, sai dai kafin ya sauke hannunsa, fiuuu!, kakeji harsashi ya ratsa ta goshinsa, mutumin da ya fito daga motar kuma ya yi harbin ya yi saurin tallafo Abyaz dake yunƙurin faɗuwa ƙasa a sume, nan da nan a ka shiga sakin wuta tsakaninsa da waɗan nan mutanen daga ƙarshe ya yi galaba a kansu ai kuwa da gudun bala'i ya tashi motar ya bar dajin tare da Abyaz da baya a hayyacinsa..._
Dai dai nan kuma Arham ya dawo hayyacinsa ya zube jigib saman Bed har yanzu bai saki kansa ba, can ya miƙe yana nanata sunan 'Nasamu a fili kana ya ci gaba da faɗin.
“Ba zan Barka ba ka jira zuwa na gareka.” Sai kuma ya yi shiru, can ya faɗa cikin wata raunatacciyar murya. “Mene ne laifin da Iyayena suka aikata maka har ka zaɓi kayi musu wannan mummunar kisa? Shin laifi ne don Mahaifiyata ta tsaya takara kai ma kuma ka tsaya? Ko kuwa ceton Rayuwata daga hannun yaranka da Uncle ƙanin Mahaifiyata kuma Mataimakin ta ya yi shi ne ya zama laifi da har ka laƙaba masa sharrin kisan Iyayena da hakan ya zama sanadiyar da ya shafe tsawon shekaru a gidan kaso?.”
Shiru ya yi yana wassafa abubuwa da dama a ransa game da wannan mutumin wato Nasamu.
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
