CAPTAIN AYUSHERH..10

16 2 0
                                    

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)

https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
                                  
        BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.

*(🔥P.P✍️)*
Episode 10.

*No. 20, Kubuwa Road, Gwagwalada Abuja.*

Buɗe ƙaramar ƙofar Gate na gidan ta yi bayan fitowarta daga Cab da ya kawo ta Anguwan.
Madaidaicin Duplex ne mai kyan tsarin gini gashi ɗan dai dai mai hawa ɗaya, daga ta ciki three bedrooms ne a upstairs da kuma down, sai kuma kitchen da sauran wuraren da ba'a rasa ba, daga waje kuma bayan haɗaɗɗen garden da a ka qawata Duplex ɗin da shi daga gefansa kuma wani madaidaicin swimming pool ne, ga kuma waterfall gunin burgewa a tsakiyar compound na gidan, briefly dai Duplex ɗin duk da madaidaici ne amma fa ya haɗu obaaa.
Gidan ya yi shiru tamkar babu kowa hakan kuma ba ƙaramin mamaki ya bata ba domin tasan kafin ta taho ta yi waya Tata har yana sanar ma ta da cewar dukkaninsu suna gida hatta Yayankaka dake makaranta ta dawo.
Sannu a hankali take taka ƙafafunta dake rufe cikin Black combat boots. Har ta ƙari sa Entrance na palon, ta ɗan dakata da tafiyar tare da saka wani card ƙofar ta buɗe. Tura kanta ciki ta yi bakinta ɗauke da sallama tana kuma mamakin duhun da palon ya yi gashi shiru sai dai bata gama mamakin ba lokaci guda hasken sparkling mai kaloli blue da red sai yellow ya mamaye palon yayin da gaba ɗaya suka haɗa baki wurin faɗin. “Surprise.” Suna faɗa hakan ya yi dai dai da wasu irin ƙananun ƙyalƙyali suka fara zubawa daga sama suna sauka a dai dai saitin da take, can kuma daga gefe ilahirin mutanen gidan ne tsaytsaye kowannensu fuska ƙayace da kyawawan murmushi yayin da duk suka haɗa baki wurin faɗin. “Muna tayaki murna ta Ranar farko da fara aiki a matsayin soja.”
Tsaban mamaki ya sa Ayusherh ta kasa magana ji take maganar ta yi kuka duk wani abu da zai sakata farin ciki Tata ya sanshi. Tahowa wurinta suka fara yi gaba ɗaya, ai bata bari sun ƙari so ba da sassarfa ta ƙari sa wurin Tata tare da shigewa jikinsa tana sakin kuka na farin ciki.
Murmushin kowannensu ya faɗaɗa domin muddun a gidan mai cike da farin ciki kake to fa zakasan irin tsaftatacciyar ƙauna dake tsakanin ƴa da uban.
Ɗan bubbuga bayanta Tata ya yi cikin dauriya ya ce. “To wannan kukan fa, yau fa Rana ce ta farin ciki a gareki damu Ahalin ki baki ɗaya ko kin manta?.”
Ya faɗa bayan ya rabata da jikinsa yana goge ma ta hawayen.
Murmushi ta yi yayin da kwalla ya taru a idon ta.
“Dole nayi kuka Tata domin bani da bakin magana ko kuma godiya a gare ka haƙiƙa kai ɗin na musamman ne a cikin ubanni na duniya ina alfahari da kai.”
Murmushi Tata ya yi kurum yana gyara tsayuwarsa tare da riƙe crutches dake taimaka masa wurin tafiya, yayin da ya sa hannu ya karɓa wani surprising box daga wurin Ali sannan ya miƙa ma ta yana faɗin.
“Ga ƴar ƙaramar kyauta daga Tatan ki.”
Hannu na rawa Ayusherh ta sa ta karɓa box ɗin bakinta a washe tsaban farin ciki ta rasa inda zata saka kanta. Hannu ta sa a hankali ta fara warware box ɗin sannan ta buɗe ta sa hannu tare da ciro wata Princess Gown dake zuba walwali, kallon Tata ta yi tana ɗan zaro ido kafin ta yi magana key dake jikin rigar ya faɗi ƙasa, da sauri ta tsugunna tare da ɗauka ga tsananin mamakinta key ɗin mota ne. Ayusherh ta tsuke baki kwalla na taruwan ma ta, ta kuma duban Tata jinjina ma ta kai ya yi tare da nuna ma ta box ɗin, ta ƙara kai dubanta ga box ɗin dake hannunta, ɗan ring box da kuma roba na sarƙa ta gani, ta ɗauka ring box ɗin tare da buɗe wa, hasken walwalin da ring ɗin ke yi ya daki idonta da yasaka ta lumshe ido jikinta na rawa.
“Tata duk waɗan nan fa, duk dan ni ne?.”
Ta faɗa cikin sanyin murya tana kallon sa.
Jinjina ma ta kai ya yi tare da faɗin. “Muje daga waje kiga motar Allah ya sa ta yi dai dai da ra'ayinki.” Ya faɗa yana mai kamo hannunta suka nufa ƙofar fita, yayin da su Ali suka mara musu baya, Yayankaka tana riƙe da Yâ tâ da zuwa yanzu tsofa sosai ya kamata, sai kuma wani Matashi da bai wuce sa'an Ali ba sannan sai wata budurwa duk su kayi waje.
Hannu Tata ya sa tare da ya ye yadin da aka rufe motar da shi ai kuwa take motar ƙirar Lamborghini Countach, mai launin ja ta bayyana.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now