•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
https://chat.whatsapp.com/KuZ1S0lUnmXGyThdLj9dVO
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
+234 808 112 9487.
*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 12.
A jere motocin suka shiga katafaren ƙeraren gidan, haɗaɗɗe iya ganin ka, basu kai ga ƙari sawa parking lot ba wasu motocin sojoji guda uku suka danno cikin gidan suma. A compound na gidan motocin sojojin suka faka. Da sauri sojan ya ƙari sa tare da buɗe motar dake tsakiya. Fitowa General Lamrat Jabir Junaid ta yi sanye cikin uniform na soji idanunta maƙale da Space yayin da take riƙe da Jacket a hannunta. Dai dai lokacin suma su Alhaji Dawud suka fito daga nasu motar shi da wannan Matar rungume da juna. Ɗauke kai General Lamrat ta yi tamkar bata gansu ba. Magana ta yi ma sojan da ya buɗe ma ta motar, sannan ta yi ciki.
Matar nan ta ja tsaki ƙasa ƙasa tana bin General Lamrat da kallon banza. Yayin da shi kuwa Alhaji Dawud ya jinjina kai, rai a ɓace wato har shi ne Lamrat zata gani ta ɗauke kai. Lallai wannan aikin sojin ya saka kanta ƙara girma ringingin tun da har zata gansa ta ɗauke kai sai dai zai yi wa tufkar hanci.
Kai ya kaɗa suma suka shiga ciki shi da ita, part ɗin sa suka wuce direct, ta taya sa ya yi wanka ya shirya sannan ta koma nata part ɗin.
...
Shiga palon ya yi da sallama sai dai ba'a amsa ba, hakan ya sa shi ƙari sawa ciki sai dai ba kowa, direct bedroom ya nufa, tare da shiga ciki a masifance tsaban bala'i dake cin sa har wani kumfa kumfa yake fitarwa daga bakinsa.😅
“Wato ke Lamrat kin rainani ba, saboda kwana biyu nayi sanyi ko wato shi ne ɗazu kina gani na kika ɗauke kai sannan kikayi tafiyar ko saboda kin mayar dani shashashan namiji, to wallahi ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, kuma waɗan nan gaddawan ɗirka ɗirkan mazan da kike zuwa dasu bana da ra'ayin sake ganinsu a gidana ina fata kinji?.”
Ya ƙare maganar a wani kausashe yana nuna ta da ƴasa.
A hankali cikin nutsuwa ta ɗa go tana dubansa, tun da ya fara maganar bata dubesa ba kuma bata tanka sa ba, har sai da ta ji ya yi shiru alamar ya gama.
Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai still bata ce masa ƙala ba, ta dubi Ma'aikaciyarta dake tsugunne tana goge ma ta ƙafar da ta gama gasa ma ta da towel, a sakamakon ɗan rauni da taji a wurin aiki, ya sa taji ciwo a ƙafar yanzu haka ma daga hospital ne tayo gida.
“Amira zaki iya tafiya na gode.”
Ta faɗa bayan ta kauda kanta daga dubansa.
Miƙe wa tsaye Amira ta yi kanta a ƙasa ba tare da ce komai ba ta fice sum-sum cike da tausayin uwar Ɗakin nata da wannan rashin mutunci da tijara da miji ke mata bai damu da su ƴan aiki suna wurin ba, wannan yana faruwa ne tun lokacin da ya aure ta gashi har yau bata canza zani ba shekara ɗai-ɗai har Ashirin da ɗauriya.
Miƙe wa tsaye wa ta yi daga saman stool da take a ɗan kishingiɗe tare da ƙari sawa gaban dressing mirror ta zauna tana duban kanta a madubin dake a wurin.
Shi kuwa sororo ya yi yana dubanta baki sake wato yau shi Lamrat take sharewa har haka lallai ne.
“Kayi haƙuri ka dena yi min faɗa a gaban Ƴan aiki baka gudun su raina ka a matsayinka na President mai ci yanzu? Kuma Babban Mutum a idon kowa?.”
Ta faɗa cikin sanyin murya.
A kufule ya tunzura zai yi magana, sai dai ƙarar kira da ya shigo wayarsa ne ya sa ya dakata tare da duba wayar ganin mai kiran ba kowa ba ne fa ce P.A na Haisam ne ya sa ya yi hanzarin ɗa gawa tare da karawa a kunne sai dai bai kai ga magana ba ya zaro ido tashi guda hankalinsa ya ɗugunzuma wurin tashi, murya a ɗa ge ya ce.
“Haisam ɗin ne a ka yi kidnapping nasa to garin ya ya?.”
Sai kuma ya nufi ƙofa da sauri, tsaban sauri har yana kusan ƙumewa da ƙofar bai lura ba.
Ita ma General jin sunan da ya ambata da kuma batun kidnapping ya sa hankalinta kai ƙololuwa wurin tashi kar dai a ce Haisam ɗin ta yake nufi an ce?. Zuciyarta ke yi ma ta wannan tambayar sai dai bata da mai bata amsarta.
..
Da sauri ya ƙari sa shiga palon tare da ƙari sawa wurinta, tana durƙushe ne riƙe da wayar. Tallafota ya yi zuwa jikinsa yana faman lallashi.
“Maimuna ki kwantar da hankali mana nayi miki alƙawarin ba abin da zai sama ɗan mu Haisam koma ina ne kidnapper's ɗin suka kaisa zai dawo wannan alƙawari na ne.”
Kwace jikinta ta yi daga nasa tana yi masa wani kallo take faɗin. “Na kwantar da hankalina fa kace a sace yaron nawa guda kake maganar na kwantar da hankalina iye Dawud ka amsamin?.”
Wani irin duba na tsanaki Mr President yake yi ma Maimuna wato mahaifiyar Haisam.
Ƙasa ta yi da kanta tare da durƙusa wa, tana ƙara sautin kukan ta.
“Mene ne yake faruwa?.”
Gaba ɗaya suka jiyo dan ganin mai maganar.
Wata kyakkyawar Mace ce da ba zata haure shekaru arba'in zuwa da sama ba, tana tsaye sanye cikin wata doguwar riga har ƙasa ta yi rolling da mayafi mai girma da kuma faɗi simple make-up ne a fuskarta ƙafafunta rufe cikin wasu flat shoe yayin da take riƙe da wasu littattafai a hannunta. Ta zuba musu ido tana jiran amsa.
“Yaya Dawud magana fa nake wai meke faruwa ne naga Anty Muna tana kuka haka?.”
Ta ƙara jefo masa tambayar.
Ajiyar zuciya Alhaji Dawud ya sauke yana faɗin.
“Dawha yaushe kika dawo? Dama Haisam ne masu garkuwa da mutane suka yi kidnapping nasa a hanyarsa na dawowa daga Lagos zuwa Abuja.”
Wani irin banbara kwai maganar tasa ta yi ma ta. “Kidnapping!!!.” Ta maimaita a fili fuskarta ɗauke da zallar mamaki, sai dai duk abin da take yi cikin nutsuwa ne.
Jinjina ma ta kai kurum Alhaj Dawud ya yi yana kara wayarsa a kunne sakamakon kira da ya shigo.
Zuwa washe gari babu inda labari bai zagaya ba a kan sace Haisam da ƴan garkuwa da mutane suka yi, abin akwai matuƙar ɗaure kai a ce Mutum har Mr President Alhaji Dawud Nasamu ne a ka sace yaron sa guda, Lallai abin ya koma kan su ya bar kan ƙanana-ƙanana.
*Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.*
Shigowa cikin Ɗakin taron General Lamrat ta yi kana Ganinta kaga wacca ta kwana ba bacci ga idanunta sun ɗan kumbura yanayinta sam ba walwala ta shigo wurin tare da ƙari sawa matsayarta ta tsaya kusa da farin allon wanda hasken kwan wutan projector ya haskesa, tare da nuna hoton wani Matashi da allon ya bayyana. Sannan ta fara magana kamar haka;
_You can continue reading this book on Arewabooks App, search @nkds._
It very short page sorry ahh!!!!
_Oooo Mah people mu haɗu gobe huh domin sanin yadda za ta kaya in Allah ya kai mu, thank you for your support and love, Nainarh KD As you know na yi muku fatan Alkhairi bye...💋👋_
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romansa# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
