•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.Perfectly Pen's 🖊️
Episode 9.
*National Muslim Orphanage, Plot 135, Cadastral Zone B02, Wuse II, Abuja.*
Wata farar mota ce ƙirar Mercedes-AMG One, ta ƙari sa dai dai ƙofar Gate na Orphanage ɗin sannan budurwar dake driving ta paker motar a ɗan gefe kaɗan da Gate ɗin. Buɗe Handbag ɗin ta dake a je a gefe ta yi tare da ciro Wayarta ƙirar Huawei P40 Pro (Porsche Design) gyara zaman white medicated glass dake maƙale a idanunta ta yi, sannan ta lalubo wata lamba da a ka yi saving da emoji alamar. Protest, Power. (✊) Sannan ta danna kira, ringing ɗaya a na biyun ne kuma a ka katse kiran ta can ba tare da an ɗauka ba. Girgiza kai kurum ta yi domin inda sabo ya ci a ce ta saba da halinsa, wannan kaɗan ke nan daga ɗabi'arsa. A hankali laɓɓanta suka furta. “Arham! Sometimes you're protest but you're the G.o.a.t (The greatest of all the time!) for me and everyone.”
Bata ƙara sakan biyar a hakan ba, a ka buɗe ƙaramar ƙofar Gate na Orphanage ɗin kafin wani dogo fari kyawawan Matashi ya bayyana, tafiya ya fara domin ƙari sawa wurin motar, yayin da Budurwar ta zuba masa idanu zuciyarta na ƙoƙarin kai ta ga wani tunani daban.
Yes!! Arham kyakkyawa ne irin ajin farko ɗin nan babu Mace mai ji da kanta da zata gansa ba tare da ta kyasa ba, yana da tsayi wanda ya yi dai dai da yanayin jikinsa da ba rama ko kaɗan kuma ƙibarsa bai yi yawa ba, jikin nasa a murɗe kai da gani kasan ana bawa jikin kulawa da ta dace ta hanyar Gyming da sauran abubuwa na motsa jiki.
Kwankwasa Glass na motar da ya yi bayan ya ƙari so, shi ne dalilin katsewar tunanin nata. Dubansa ta yi tare da buɗe gaban motar, ta gefanta, shiga ya yi ya zauna ba tare da ya kalle ta ba sai wani ciccin magani yake.
Dariya ya bata, amma ta gimtse, ta ɗan saci kallon sa sannan ta kira sunanta tare da ci gaba da faɗin.
“Arham Bro Me! Fushi kake dani ne wai?.”
Ta yi masa tambayar tana kafesa da kyakkyawan idanunta dake cikin Glass.
Huci ya furzar yana shafa sumar kansa mai ɗan yawa, ba tare da ya dubeta ba ya ce.
“Haka na faɗa miki?.”
Girgiza kai ta yi sannan ta ce.
“Sam a'a, sai dai hakan na fahimta.”
“Ba fushi nake ba.”
“To tun da haka ne kayi dariya mai bayyana haƙora na gani.”
Ta faɗa tana harɗe hannu a ƙirji tare da kafesa da ido, duk da tasan abin da ta faɗa ɗin bamai yiwuwa ba ne indai Arham ne.
A karo na farko tun shigarsa motar ya dubeta ita ma shi ɗin take kallo.
A hankali fuskarsa dake murtuke ta fara sauyawa yayin da simple murmushi ya bayyana.
“Hakan ya miki?.”
Ya tambaya tana mayar da fuskar yadda take a fari.
Dariya take ta danne wa, ta daure ta ce.
“Sam bai yi ba.”
Wage ma ta baki ya yi dukkanin haƙoransa thirty two suka bayyana. A hakan ya ce da ita. “To haka ya yi.”
Ya yi maganar muryarsa a sama kuma ta fito wata iri sakamakon bakinsa dake a buɗe.
Gaba ɗaya suka saka dariya. Sai da ta nutsu sannan ta tada motar suka ɗau hanya, kana ya ce faɗin.
“Kin iso lafiya?.”
Idanunta na kallon titi ta amsa masa da faɗin.
“Lafiya Qlau. Fatan na sameka lafiya?.”
“Alhamdullilah..”
A cewarsa. Shiru ya ɗan biyo baya. Sanin da ta riga ta yi muddun ta biye ta nashi sai dai su ci gaba da kasancewa zaman shiru a motar ne ya sa ta ce.
“Allah ya sa ka fito da duka takardun da za'a nema?.”
“Uhump.”
Ya faɗa. Ita kuma ta jinjina kai, ta ƙara da faɗin. “Please Bro ka daure karka bani kunya a wannan karon ka nutsu ka amsa duka tambayoyin da za'ayi maka a yayin gudanar da interview ɗin kaji?.”
Ta ƙarishe maganar tare da ɗan dubansa kaɗan. Murmushi ya saki yana amsa ma ta da faɗin. “To Mama, what next?.”
Ɓata fuska ta yi. “I'm serious fa, kaga kusan companies biyar ke nan a ke nema maka aiki, amma zafin rai yake sa ka ka saka bada haɗin kai tun a wurin interview. Dan Allah ka daure kayi zuciya a wannan karon na shida ka basu haɗin kai wurin gudanar da interview ko dan na dena maka gori.”
Ta kai maganar da ɗan murmushi.
“Yusra!..”
Ya ɗan ja sunan nata. “Na'amm!..” Ita ma taja wurin amsa wa, ba tare da ta dube inda yake ba, a ƙoƙarinta na kauce wa truck dake tunkaro su.
“I Promise zan yi iya kar bakin ƙoƙari na wurin ganin wannan karon ba'a sama matsala ba, nayi miki alƙawari.”
Tsaban farin ciki da mamakin kalamansa ya sa Yusra kusan sakin steering motar tana washe baki, da mugun sauri Arham ya kai hannu kan steering tare da kaucewa Truck ɗin da ta kusa yin ciki da su.
“Yusra! Kina a hayyacinki kuwa? So kike kija mana mummunar accident ne?.”
Ya tambaya murya a ɗa ge. Lokacin da ya yi gefen titi da su tare da tsaida motar idanunsa a kan ta.
“Am so sorry Arham amma tsaban farin ciki ne ya sa na kusa sakin steering ba tare da na ankara ba.”
“Farin ciki da me?.”
“Da kalamanka mana.”
Girgiza kai ya yi. “Dawo nan na lura ba zaki iya driving ba.”
“Ah ka bar shi kawai ai yanzu ne zan matuƙar iya wa ma kuwa.”
Ta yi maganar tana ƙoƙarin tada motar, shi dai bai ƙara cewa komai ba. Yusra ta ja motar suka ƙara hawa titi. Sanin da ta yi ne a kan da wuya ya ƙara magana kuma, hakan ya sa ta kunna. Karatun Alkur'ani mai girma, ta speaker na motar, daddaɗan ƙira'a na matashin Balaraben nan wato Saad Al-Qureshi na tashi cikin Suratul Maryam.*Precise Financial Systems Limited - Plot 1245, Cadastral Zone A05, Maitama, Abuja.*
A nutse kowannensu ya fito daga ɓangaren sa bayan Yusra ta shiga da motar a cikin Company ɗin sannan ta yi parking a wurin da a ka tanadar.
Ɗan gyaran murya Yusra ta yi, hakan ya sa Arham dubanta.
“All the best.”
Ta faɗa tana sakar masa murmushi. Jinjina kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya yi ciki. Yayin da Yusra ta jingina a jikin motar tana kallon makeken ginin zamani skyscraper na companyn.
Rurin da Wayarta ta fara alamar shigowar kira ne, ya sa ta ciro wayar tana duba sunan da ya bayyana saman screen na wayar. My Nusra, shi ne sunan da ya bayyana, hakan ya sa ta yi azamar ɗagawa ta kara a kunne tare da buɗe motar ta shiga, zama ta yi tana faɗin. “Ni kam nayi fushi domin an manta dani tun da a ka tafi Dubai.”
Ta faɗa tana ɓata fuska tamkar wacca ta kiratan tana a gabanta. Daga ɗayan ɓangaren mai kiran, ta saki murmushi mai sauti sannan ta ce. “Kinji ki ke ma, ban da abin ki kwata kwata yaushe ne Bama tare, 2 days ne fa, kuma ai gashi yanzu na kira.”
Yusra ta ɗan gyaɗa kai sannan ta ce. “Ni dai kam duk da haka nayi fushi.”
“Kaina bisa wuya, Anty Yusra Tah ayi min afuwa tohm...domin kin san muddun baki dena fushin nan ba to fa ba zan iya ƙara kwana a Dubai ba, Nigeria zan yo direct.”
Dariya maganar nata ya bawa Yusra ta dara tana faɗin. “Ah ah ba'ayi haka ba kuwa, tohm shikenan na haƙura, sai dai ina mamaki yau Nusra ɗita ce ta kirani da Anty da alama dai buri ya cika ko nace yana kan cika bani labari.”
Ta faɗa tana gyara zama, ai kuwa nan Nusra ta fara bata labarin a kan abin da ya kaita Dubai da irin nasarar da ta samu a kwanaki biyu da ta yi a can.
Sun ɗan jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama. Yusra ta katse kiran tana ɗan murmushi, Allah ya gani tanason twins sister ɗin nata duk da cewar ta kasance wata kalar Mace da ba'a gane gabanta balle bayanta. Fitowa ta sake yi, ta jingina da motar ba tafi minti goma ba ta hango fitowar Arham yana nufota. Tun kafin ya ƙari so take faman washe baki duk da gefe guda na zuciyarta na ɗan harbawa domin batasan tsiyar da ya yi a ciki ba.
Takardun dake hannunsa ya miƙa ma ta da sauri ta karɓa ba tare da ta duba ba, ta riƙe a hannun nata yayin da ta zuba masa ido tana jiran ji daga bakinsa.
Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya dubeta kamar yadda ita ma shi take duba.
“S...Su...sun ɗauki Arham a aiki. Ina nufin na sama aiki.”
Ya ƙari sawa maganar da ɗan ƙarfi yana sakar ma ta wani murmushi mai burgewa da ya sa ta kusan daskare wa a wurin. Idanunta a kan sa tana ƙoƙarin tariyo abin da taji ya faɗa dan ji take kamar ba dai dai taji ba.
Ihu ta fasa tare ta rungumo sa tana faɗin. “Alhamdullilah Amma wallahi naji daɗi sosai...wato shi ne da fari ka rarraba maganar saboda kanason cikina ya ɗuri ruwa ko?.”
Ta kai maganar tana sakinsa da ɗan hararar na wasa. Sai kuma a lokacin taji kunyar rungumar da ta yi masa ganin irin kallon da yake ma ta.
“Sorry.”
Ta faɗa cike da kunya tana buɗe motar ta shiga. Ya ɗan girgiza kai shima sannan ya shiga motar.
“Ya kamata muyi kwarkwayar shagali na murnar aikin da ka samu ko?.”
Ta tambaya tana kallon sa bayan ta tayar da motar. “A'a ba yanzu ba tukunna ki bani sati ɗaya muga yadda lamarin aikin zai kasance.”
Ya faɗa ba tare da ya dubeta ba, idanunsa na kallon mirrorn waje na motar dai dai satin da yakeso dai dai lokacin kuma Baturen dake tsaye gaban wall Glass ɗin dafe da fuskarsa da ta ɗan kumbura ga kuma shatin yatsa alamar ya sha mari ya kai duba ga saitin da suke.
Arham ya saki kyakkyawan murmushi yana girgiza kai tare da gyara zama.
Yusra ta ja su suka bar Company ɗin....🪄💖
Ayusherh bata da ra'ayin zama a Barrack sam kuma Barrack ɗin akwai nisa sosai da Gidansu wannan dalilin ya sa a ka ware ma ta wani Flat home a ɗan gefe da Barrack ɗin kuma a zuba ma ta dukkanin abin buƙata zata zauna a ciki... Ta fara gudanar da aikinta cikin kwarewa da sanin makamar aiki, tun daga ranar ta ta farko.

YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...