•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 19.
“umhp tohm nifa bakya sona.”
Haisam ya faɗa cikin zolaya.
Sai kuma ya ƙara faɗin.
“Saurayina ne kayi haƙuri Tata...”
Haisam ya faɗa yana ƙasa da kai tamkar yadda Ayusherh ta yi ɗazu.
Sai kawai ta kai masa naushi na wasa. Ai kuwa ya kauce cike da farin ciki yake faɗin.
“Yau dai da taimakon Allah da kuma Tata na gano wata ta daɗe da narkewa a kogin so da ƙaunar Haisam.”
“Hump.”
Kawai Ayusherh ta ce tana murmushi domin abin nashi yafi ƙarfinta.
“Maganar gaskiya nayi farin ciki kuma ina cikin farin ciki matuƙa da ganin wannan rana.”
Cewar Haisam lokacin da ya ƙari so dab da ita.
“Faɗa min mai kuka tattauna da Tata?.”
“Sirri ne.”
“Au ɓoye min zakayi?.”
“Gashi kuma.”
“Lallai ne zan rama.”
“Za dai ki rame Yarinya.”
“hump ina son ka.”
“Nima haka kuma fiye da yadda kike tunani ko baki yarda ba?.”
“Na yarda mana tun da naga kayi ƙasa da kai daga ganin Suruki.”
Dariya ya yi suka fara tafiya. Har wurin motarsa ta rakasa lokacin da suka fito domin bataga Tata a wurin ba. Da yake Haisam ya faɗa ma ta wurin shooting zai tafi na wani sabon Film nasa da a ka fara ɗauka. Sai dai kafin nan zai fara tafiya wani wuri kuma zasu ƙari sa ɗaukar sabuwar waƙarsa.
“Ni kam nace, kai ɗin mawaƙi ne ko kuma ɗan rawa?.”
Ayusherh ta faɗa lokacin da ta zura kanta cikin motar da yake zaune gaban motar mazaunin driver domin duk yadda Mom taso ya fito da koda driver ne ƙi ya yi domin a cewarsa duk shirmen banza ne tun da har an iya kidnapping nasa babu abin da suka yi akai.
“Wannne kika so na kasance a ciki?.”
Shima ya jefo ma ta tambayar. Ayusherh ta ɗan zaro ido. “Ni! A'a ba ruwana ko wannne ne ma sai dai nayi ma ka fatan nasara duk da ba zan jura ganin wata ta saka idonta a kan ka ba.”
“Au ashe ana kishi na har haka.”
Murmushi ta yi bata basa amsa ba, ta gyara tsayuwarta tare da yi masa bye-bye shima ya yi ma ta sannan ya tada motar ya nufa Gate.
Ayusherh ta sauke ajiyar zuciya dai dai lokacin kuma Tata ya ƙari so yana faɗin.
“Mu tafi ko?.”
“E Tata amma ina ka shiga ban ganka ba?.”
“kina a cikin shaukin soyayya ta yaya zaki hango ni?.”
Kunya ne ya ɗan kama Ayusherh.
Suka fara tafiya suka nufa Gate na Barrack ɗin.
“Laaa! Tata ina motar naka?.”
“Ta ɗan sama matsala ne a hanyata na zuwa sai dai na haɗu da wani ya taimaka min ya ƙari so dani zuwa nan ita kuma motar an kira bakanike zai gyara ya kai min har gida.”
Tata ya faɗa yana tuna yadda suka ƙare da Ummulkhair sai da ta amshi address ɗin sa acewarta bakaniken zata faɗa ma domin ya kai masa motar har gida sannan ya sake ma ta godiya ita kuma ta bar Barrack ɗin.
“Ayya! Gashi ni kuma na bar tawa motar a gida domin na yanke hawa Cab ne kawai domin ƙari sawa gidan namu bayan na tashi daga aiki.”
“Karki damu yanzu sai mu tara cab ɗin kawai mu koma a ciki.”
Cewar Tata.
Ayusherh ta ɗan yi shiru domin haka kawai taji yau kunyar Tata takeji. Tata yana lura da ita sai kawai ya yi murmushi yana girgiza kai, Ayusherh akwai kunya.
Fitowa suka yi daga Barrack ɗin suka hau titi suna ɗan tafiya. Ganin shirun ya yi yawa ne ya sa Ayusherh ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce.
“Wai kuwa Tata ka bani labari a kan Mahaifiyata mana!.”
Ƙari sa maganar nata ya yi dai dai da bugun da ƙirjin Tata ya yi. Hakan ya sa ya ɗan dakata da tafiyar yana kiran sunan Allah a ƙasan ransa.
“Tata wani abu ne ya faru?.”
Ayusherh da ita ma ta dakata ta tambaya cike da kulawa. Da kuma damuwa dan har sai da ta yi data sanin tambayar da ta yi masa domin a tunaninta saboda ta tuna masa da Matarsa wato mahaifiyarta shi ya sa ya shiga wannan yanayin; tabbas kusan haka ne sai dai ba hakan ba ne domin wani abun ne daban ya faɗo ma Tata a rai, duk da yasan ba'a Barrack ɗin da Ayusherh take aiki ba ne Mahaifiyarta ta yi amma yana gudun kar maƙiyan mahaifiyarta su gano ta har su cutar masa da ita, shi ne abin da ya sa shi faɗuwar gaba.
“Haƙiƙa tun da kike tambayata wani abu dangane da Mahaifiyarki ban kasance mai sanar dake komai ba, amma yau kuma yanzu san sanar dake kaɗan daga cikin kyawawan hali na Mahaifiyarki da yanayin mu'amalarta da kowa cikin sauƙin kai.”
Tata ya faɗa a ƙoƙarin sa na ganin Ayusherh ta fita daga damuwa data shiga na ganin halin da ya shiga.
Murmushi Ayusherh ta yi tana faɗin.
“uhump u'um Tata nah kawai ka faɗa min yadda a kai kuka haɗu da Mahaifiyata.”
Ayusherh ta faɗa fuska cike da annuri.
“Babbar magana....” Tata ya faɗa ƙasa ƙasa. “Kace mene Tata ban jika ba?.” Da ɗan ƙarfi tamkar bata kusa da shi Tata ya ce. “Ban ce komai ba, zan dai sanar dake abin da kika tambaya ne.”
“Yawwa Tata nah ina sauraren ka.”
Tata ya yi gyaran murya har da ƙalƙala da ya yi masifar bawa Ayusherh dariya amma ta daure tanayi ƙasa ƙasa yayin da Tata ya fara faɗin.
“Da fari dai kin san na sanar dake a lokacin da ina Matashi na bar ƙauyen mu da ƙasar mu bisa wasu dalilai na dawo nan Nigeria kuma a nan na haɗu da Matar da ta kasance da kallo guda ta sace zuciyata wato mahaifiyarki.”
“Uhumph sai mai ya faru Tata ina saurare.”
Ayusherh ta faɗa jin ya yi shiru.
“Daga nan bayan na shawo kanta da kyar ina faɗa Miki muka fara soyayya har na samu na shawo kanta ta bini ƙasar mu bayan an ɗaura mana Aure dama na daɗe da karɓar Addinin gaskiya shikenan bayan fama da kyar su Arɗo iyayena suka amince muka ci gaba da zamanmu shikenan ƙurungus kan ƙusa...”😅
Dariya Ayusherh take yi sosai da jin kalaman Tata da yadda yake bata labarin tamkar yanayi ne sa'arsa dama ya saba musu haka lokuta da dama shi ya sa gaba ɗaya ita da su Yayankaka ba ƙaramin shaƙuwa ba ce tsakaninsu da mahaifin nasu.
“Amma Tata har yau fa baka taɓa faɗa min ya ya sunan mahaifiyata ba, abin da na sani kawai shi ne ta rasu a yayin haihuwata ko?.”
Ta ƙare maganar dai dai Cab ɗin da ta taro ya ƙari so wurin. Sai da suka shiga ciki tare da zama bayan Ayusherh ta yi masa kwatancen inda zai kaisu sannan Tata ya ce.
“Sunanku ɗaya da mahaifiyarki kamar yadda a kamanni da komai naku yake iri ɗaya hatta wannan kunyar da kuma riƙo da gaskiya da son jama'a, kawai yanayin fatar ne ba ɗaya ba kuma ba Irin na mahaifin ki ba ne sannan hancinku ɗaya da Mahaifin ki kuma....”
“Tata dama kai ba fari ba ne?.”
Ayusherh ta jefo masa tambayar. Ai kuwa Tata ya zaro ido ganin sakin bakin da ya yi. Da sauri ya gyara maganar nasa da faɗin.
“Ina nufin ke ɗin yanayin fatar ki ta kasance na daban kuma launin fata mai tsadar gaske domin irin ku ɗai ɗai ku ne a Duniya.”
Ayusherh ta saki murmushi tana faɗin.
“Irin na Queen ce ai.”
“Wacece haka?.”
“Queen of Beauty tamu mana.”
“Kinji ki Captain ni kam ban san wata Queen of beauty ba.”
A cewar Tata.
Ayusherh ta ce.
“Queen of beauty dai wata Baiwar Allah ce da ta gamu da iftila'in Rayuwa iri-iri daga ƙarshe komai ya zamo tarihi duk dai an sha gwagwarmaya.”
“Ikon Allah ita bata da wani suna ne sai Queen of beauty?.”
“Sunanta Afeefah Abubakar Mai Kyau, sai dai jama'a da dama musamman ma masoyanta an fi sani da kuma kiranta da Queen of beauty, domin ta kai a kirata da hakan.”
Ayusherh ta ƙare maganar tana zabga murmushi.
“Allah mai iko to idan kun haɗu ki miƙa min saƙon gaisuwa zuwa wurinta.”
Tata ya faɗa. Ai kuwa Ayusherh ta amsa masa da faɗin.
“Ba damuwa Tata duk da dai har yau Allah bai nufa mun haɗu ba abin da na sani shi ne na karanta Labarin ta mai matuƙar tsayawa a zuciya kuma ina fata mu haɗu da ita ko da zuwa nan gaba ne.”
“Ma sha Allah, to Allah ya sa.”
“Ameen!”
Ayusherh ta amsa dai dai lokacin kuma suka ƙari sa anguwansu fitowa suka yi Ayusherh ta biya mai Cab ɗin kuɗinsa sannan suka shiga ciki suna taɓa fira.
Kamasho.
Wata guda ke nan da fara aikinsa a gidan Mr President ƙarƙashin jagorancin Yusra yana aiki ne a ɓangaren kula da flowers da kuma wasu abu da ba'a rasa ba. Kuma jiya ne Yusra take masa albishir da gobe zai haɗu da Uncle ɗin ta Mr President domin zai ɗauke sa aiki a ɗaya daga cikin companyn sa amma haɗu war a gida zai kasance. Shi ya sa yau ya tashi cikin zumuɗi ya shirya tsaf cikin shiga mai kyau sabon suit Black da ya siya. Shi dai Arham ido ya saka masa, to da yake akwai wuri mai muhimmanci da Arham ɗin zashi shi ya sa Kamasho ya nema da ya rage masa hanya, kuma ya yarda
____
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
