•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 18.
# Captain Ayusherh
# Battle Angel 🥰💋
# Haisam
# Perfect lover🥳😍
# Arham
# Tata
# Nusra
# Yusra
# Alhaji Dawud Nasamu (Mr President)
# Mom Maimuna
# General Lamrat Jabir Junaid
# Anty Dawha
***
BAYAN WATA ƊAYA...
Tata ya yi tsaye gefen titin cikin rashin mafita a sakamakon motarsa da ta ƙage taƙi ci gaba da tafiya, gashi Yamma ta ɗan yi kuma bazata yakeso ya yi ma Captain domin ya yi da ita a kan yau a gida zata kwana, shi ne zai je Barrack ɗin domin tafiya da ita ga kuma mota da ta yi masa tsiya. Titin ya yi shiru yayin da ababen hawa ɗai-ɗai ku ne ke wucewa suma cikin sauri gashi duk wanda Tata ya tsayar basu tsayawa. Yana nan a haka wata baƙar mota tazo wucewa ai ko da sauri ya kai hannu alamar ta tsaya sai dai motar bata tsaya ba, ta yi gaba sai dai kafin Tata ya yi wani yunƙuri motar ta dawo, ajiyar zuciya ya sauke tare da zuba ido a kan motar da mamallakinta ta fa ka a ɗan gefensa. Slowly Tinting Glass na motar ya zuge zuwa ƙasa, take fuskarta ya bayyana, Tata ya ɗan kauda kai yana jan istigfari, a can ƙasan ransa, wata ƙila ma Matar Aure ce, wani sashe na zuciyarsa ya raya hakan, sai dai kafin ya lalubo amsar da zai bawa kansa, ya ji muryarta tana faɗin.
“Assalamu Alaikum! Yallaɓai akwai wani damuwa ne?.”
Ta faɗa bayan ta baro motar ta iso dab da shi.
“Wa'alaiki Salam, e akwai, mota ta ce mai matsalar.”
“Ayya! Okay tohm idan ba damuwa ko zan iya duba motar?.”
Sai Tata ya ɗan bita da kallo jin abin da ta faɗa, haka kawai ya tsinci kansa da gyaɗa ma ta kai, ita kuwa ta yi murmushi tare da ƙari sawa gaban motar dake a buɗe, takai kusan mintoci biyar a haka tana duba-dube a cikin gaban motar sannan ta ɗa go tana faɗin.
“Matsalar Babba ce Yallaɓai shi ne ya sa motar taka ta maƙale taƙi tafiya, amma bari na kira wani bakanike ya gyara matsalar, amma kafin nan taimaka min da tsumma na goge hannuna.”
Ta ƙare maganar bayan ta iso dab da shi, tana ɗan goge zufa da bayan hannunta da ya yi baƙi sakamakon taɓa motar da ta yi.
Ba musu Tata ya buɗe murfin motar sannan ta ciro wani kyalle mai kyau ya miƙa ma ta.
Karɓa ta yi sai da ta goge hannunta da kyau, sannan ta ƙari sa wurin motarta ta ciro bottle water tare da ɓalle murfin ta wanke hannunta fess! ta ƙara da goge wa da tsaftataccen Handkerchief da ta ciro a motar.
Ƙari sowa wurin Tata ta yi kunnenta kare da waya tana kiran bakaniken.
“Na gode sosai har ma ban san da wani kalma zan yi miki godiya ba, yanzu Bara na jira bakaniken yazo sannan muga ta yadda za'a ɓullo wa motar.”
Tata ya ƙare maganar yana ɗan duban agogon hannunsa.
“Ah ba komai Yallaɓai, sai dai bakaniken ya tabbatar min zai ɗan ja lokaci kafin ya iso, shin mai zai hana na ƙari she ladar nawa kawai ta hanyar ƙari sawa da Yallaɓai zuwa wurin da zashi?.”
Tata ya ɗan dubeta yana ɗan gyaran murya ƙasa ƙasa dan ya rasa abin faɗa.
“Karka damu fa babu komai dan naga alamar sauri kake yi da alama abu mai muhimmanci zakaje aiwatarwa, sannan in a kan motar ne karka damu har gida za'a mayar maka idan bakaniken ya gyara nayi maka Alƙawari.”
Ta ƙara faɗa ganin kamar bai aminta da maganar da ta yi ba.
Yayin da Tata ya ƙara riƙe sandar crutches ɗinsa da kyau yana mamakin kirki irin na wannan mata. Ba tare da musu ba ya kulle motar nasa sannan ya ce.
“Ai kuwa ina matuƙar godiya Yallaɓiya Allah ya saka da Alkhairi.”
Ya faɗa kansa tsaye yana nufar wurin motar nata.
Yayin da ta bi bayansa, ya shiga ya zauna kusa da kujerar driver sannan ita ma ta shiga ta zauna kana ta bawa motar key, sai da ta hau titi shantal sannan ta ce.
“Sunana Ummulkhair sai dai an fi kirana da Ummul.”
Jinjina kai Tata ya yi yana faɗin.
“Duba hanya da kyau a Barrack na sojoji dake ɗan gaba zan sauka.”
Ummul ta ɗan dubesa kaɗan. “To kaifa mene sunanka Yallaɓai koda yake Yallaɓai ɗin ma sunane da ya yi matuƙar dacewa da kai.”
“Haka kema Yallaɓiya ya yi masifar dacewa dake.”
Ta yi dariya yayin da Tata ya ɗan murmusa.
“Muhammad sunana sai dai yarana sunfi kirana da Tata.”
“Woww mene ma'anar Tata?.”
“A hausance yana nufin Baba.”
“Tata..” Ta maimaita sunan. “Abin mamaki amma wannan wane yare haka naji alamar zai yi daɗi?.”
“Yaren jama'ar Babur ke nan wato baburawa.”
Tata ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin kame kansa.
“oops sorry ban sanar da kai ba, ai ka saki jiki Yallaɓai domin babu nauyin kowa a kaina.”
Ta faɗa dai dai an buɗe ma ta Gate na Barrack ɗin tana ƙoƙarin cusa hancin motarta ciki.
Shi dai Tata da dabara ya ɗan kalle ta jin abin da ta faɗa. Yana mamaki domin aƙalla zata kai shekaru Talatin da ɗauriya idan bai ɓata ba.
“Ba abin mamaki ba ne dan na kasance a hakan ba tare da aure ba sai dai labarin da tsayi.”
Ta faɗa tamkar taji abin da yake ayyana wa a ransa. Dai dai ta yi parking motar.
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
