20

9 1 0
                                        

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)

                                  
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.


*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*

Episode;20

Tura ƙofar ta yi tare da shiga Ɗakin da sallama. Anty Dawha dake zaune gaban mirror ta ɗan dubeta tare da amsa sallamar. Ƙari sa shiga Ɗakin Yusra ta yi, ta ƙari sa wurin Mahaifiyartasu fuska tab da murmushi ta ce.
“Aunty! Wai kuwa kin yi ma Uncle maganar ina fata dai bai fita ba?.”
Ta ƙare maganar tana dafa dressing mirror idanunta ƙur a kan Mahaifiyar nata.
“E nayi masa, amma da kyar ya yarda fa, ina fata kin faɗa ma shi yaron a kan yazo da wuri?, kafin haƙurin Uncle ɗin naki ya ƙare.”
Da sauri Yusra ta gyaɗa kai tana kuma murmushi ta ce.
“Amma kuwa na gode sosai Anty ke ɗin ta daban ce.”
Anty Dawha ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai.
“to menene kuma na godiyar da alama bakyaso nan gaba na ci gaba da taimaka miki ta wasu fannin muddun zakike min godiya.”
“Na tuba Aunty bani ƙara wa kawai dama tsaban farin ciki ne.”
Yusra ta faɗa da sauri, kafin Aunty ta sama abin faɗa, Nusra ta shigo Ɗakin da sassarfa ta ƙari sa tare da faɗa wa saman Bed ta kwanta rigingine tana kallon ceiling.
“Nusra lafiya kuwa?.”
Yusra ta tambaya cikin kulawa.
“Haisam ne! So yake na mutu a kan son shi, ya zama dole nasan abin yi na kuma san wacece wancan sojar da ya haukace a kan son ta.”
Ta yi maganar tana dafe kanta da duka hannayenta, tare da rumtse ido, tana motsa red lip's ɗin a hankali.
“Ki kula da kyau Nusra kar kije haukan kishi ya sa ki aika abin da zaki zo kina danasani daga baya.”
“A halin yanzu bani da lokacin tsayawa nazari a kan abin da zan aikata domin ni kaina ban tantance mai zan yi ba.”
Nusra ta bawa Yusra amsa tana tashi zaune, ta ɗauki wayar da ta cillar gefe lokacin da ta hau Bed ɗin, ta fara laluben lamba.
“Nusra! Mai zaki aikata ne?.”
Yusra ta faɗa da sauri domin tasan wacece ‘yar uwar nata.
“Ki yarda dani mana Sisty ba abin da zan aikata, idan ma zan aikata wani abu zaku gani a aikata ce.”
Cewar Nusra tana ɗan bubbuga wayar hannunta a saman laɓɓanta.
“Idan kina da buƙatar taimaka wa ki sanar dani zan taimaka miki.”
Anty Dawha ta yi maganar ba tare da ta duba inda Nusra take ba.
“Bana buƙata kuma ba zan taɓa buƙata ba har abada.”
“Why Nusra? Nifa Mahaifiyarki ce!.”
Anty Dawha ta sake faɗa cikin ɗacin rai, da abin da Nusra take ma ta, ta gaji da halin ko'in kula da ‘yar nata ke ma ta.
“E, na sa ni, shi ya sa bana buƙatar taimakon naki, muddun nima ba zaki sanar dani wanene ainihin mahaifinmu ba, kuma ki bani hotonsa mu gani.”
Nusra ta faɗa tana miƙe wa tsaye.
“Nusra ki gyara kalaman ki kin manta wacece a gabanki ne Mahaifiyarki ce fa.”
Yusra da bata jin daɗin rashin fahimtar juna dake tsakanin ‘yar uwan nata da Mahaifiyar tasu ta faɗa.
“Kin sanni kin san halina ban iya ƙarya ba, iyakar abin da ke raina nake faɗa, saboda haka ba zan taɓa neman taimakon ta ba muddun bata faɗa min wanenen Mahaifin ba kuma ta kai mu Wurin danginsa.”
Nusra ta faɗa rai a ɓace tana nufar ƙofa.
Sai kawai Anty Dawha ta saka kuka. Yusra ta yi saurin riƙe ta tana faman bata haƙuri. Ɗan jim Nusra ta yi bata juyo ba amma ta tsaya da tafiyar da take yi, sai kawai ta ƙari sa da sassarfa ta bar Ɗakin zuciyarta ba daɗi sai dai a duk wannan bata hango laifinta a ciki ba, duka laifin Mahaifiyar tasu ce da taƙi faɗa musu ainihinsu. Ai ko shege ma yana da Asali balle kuma su da ta tabbatar musu ba ‘yan gaba da fatiha ba ne, to mai zai saka taƙi kaisu wurin Dangin mahaifinsu?.

“Mun iso.”
Arham ya faɗa lokacin da ya fa ka motar a ɗan gefe kaɗan da katafaren gidan Mr President a katafariyar anguwan.
“Tohm Babban Yaya Bara na shiga ciki a taya mu da fatan Khairan.”
Cewar Kamasho yana ƙoƙarin fita daga motar.
“Da yardar Allah koda yake ai nasan zaka iya fatan nasara Abaan.”
Arham ya faɗa lokacin da Kamasho ya fito daga motar.
“Godiya nake Babban Yaya.”
“Yi sauri kaje kar lokaci ya ƙure.”
Arham ya yi shiru zaune a motar ya ɗan zubawa katafaren gidan na Mr President ido yana nazari. Tun bayan da Kamasho ya shiga ciki bayan tarin security's sun gama bincike shi tsaf sannan suka barsa ya shiga ciki. Hakan ma dan sun san shi ne.
Tada motar ya yi ya bar Anguwan da sauri domin shi kanshi bai san mene zai faru ba idan ya ci gaba da tsayawa a wurin. Gudu yake santalawa a titin tamkar zai tashi sama kuma hakan ya sa cikin ƙanƙanin lokaci ya iso inda zashi.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now