CAPTAIN AYUSHERH...3

4 1 0
                                    

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
                                   https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
       
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡

Don't Forget To Follow My Both Accounts;
Nainarhkd3 @Wattpad.
Nkds @Arewabooks.
..

Episode 3.

Yau ma kamar kullum tana sanye ne da kayanta na saƙi irin na shiga farauta.
..
Doguwar rigar mai dogon hannu mai launin ash mai duhu, ta ɗaura dogon mayafi ta rufe kanta, yayin da dogon baƙin gashinta da a ka yi masa kitso silli ɗaya. Da sauri ta sa hannu tare da dawo da gashin ta gaba, yadda zata ji daɗin ɗaukar ɗaya daga cikin baka nata da suke cikin ƴar jakar farauta dake saƙale a bayanta.
Ƙasa ta yi da sauri dai dai ta ɗauki baka guda biyu, sannan ta haɗa da kwari dake hannunta. Ƙoƙari take sai ta harba barewa da take ma ta wasa da hankali, ɗan rage girman idanunta ta yi tare da sai ta dai dai bayan barewar sannan ta saki bakar, ai kuwa cikin sa'a ta sama barewar a inda take so.
Sai a lokacin ta saki kyakkyawan murmushi tana miƙe wa tsaye tare da yaye mayafin dake kanta ta yi baya da shi, mayar da kwarin hannun hagunta ta yi, tana kuma nufar inda barewar take kwance, tsugunna wa ta yi gaban barewar, dai dai ta kai hannu zata taɓa ta ke nan, kaifafan kunnuwanta suka jiyo ma ta wani sauti da alama ita a ke tunkaro wa. A wani irin zafafe ta miƙe tsaye tare da ciwo takobin ta dake saƙale jikinta, ta yi saurin tare takobin da a ka kawo ma ta sara da nata takobin. Baya ta ɗan yi tare da ɗa go idanunta suka shige cikin na Samarin majiya ƙarfi da kowannensu yake riƙe da nasa takobin su huɗu sun zagaye ta.
A karo na biyu ta ƙara murmusa wa tare da yin baya da takobin ta, da hannu ta yi ma matashin saurayin da fuskarsa yake lulluɓe da wani kyalle, ta yi masa alama da yatsunta biyu, alamar su fara.
Karkace kai ya yi, dan ya fahimci abin da take nufi, ƙoƙarin shammatarta ya yi ta hanyar sake kawo ma ta wani harin da takobin dake hannunsa cikin sa'a a kuma zafafe ta tare da nata takobin, nan fa suka shiga wasa da takobin suna kai ma juna farmaki, sai dai kowannen su yana kare kansa da nasa takobin, ganin da sauran samarin suka yi a kan Ayusherh tana dab da ta yi nasara a kan ɗan uwansu ne ya sa suma su duka shiga sunayin faɗar tare sai dai fa duk yawansu da kuma horo da kwarewar da suke taƙamar suna da shi a ɓangaren wasan takobin, basu samu sun yi nasara a kan Ayusherh ba, sai ma ita da lokaci guda ta yi nasara a kan su gaba ɗaya ba kuma tare da gajiya wa ba, su kam zuwa yanzu sun gaji, dan sun fahimci Yarinyar ta fi su.
Ƙasa suka yi gaba ɗaya alamar saranda dai dai ta kai takobinta da shirin kai farmaki gare su. Ganin haka ya sa ta sauke takobin, tana jijjiga kai. Ta mayar da takobin inda yake ta buɗe baki da niyyar magana suka jiyo tafi raf-raf a ta gefansu, da sauri su duka suka kai dubansu zuwa saitin da suka jiyo tafin.
Wani farin mutum ne dogo da kai tsaye za'a kira da matashin dattijo, shi ne yake tafin yayin da yake ƙari sawa wurin da suke.
Murmushi mai bayyana haƙora Ayusherh ta saki tana faɗin.
“Tata!.”
Yayin da take ƙoƙarin ƙari sawa gare sa. Miƙe wa samarin suka yi suma da ɗan murmushi, saurayin mai rufe da wani kyalle a fuskarsa ya cire kyallen, ta ke kyakkyawar fuskarsa mai cike da ƙuruciya ta bayyana, ɗauke da murmushi ya fara magana cikin harshensu da faɗin.
“Lallai na yarda shekaru kawai lamba ne amma kwarewa yana ga jajircewa domin kuwa Captain ta bamu mamaki gaba ɗaya mun kasa nasara a kan ta. Ûná (Uncle) ya kamata a bar Captain ta shiga gasar takobi da za'a gabatar nan bada jimawa ba.”
Ya ƙare maganar da kallon Ayusherh da ta kwaɓe fuska, domin bataso ya faɗa ba, taso a ce ita da kanta ta faɗa wa Tata ɗin nata, dan bata da tabbacin zai barta ta shiga, murmushi matashin ya yi ma ta, tare da ɗa ga ma ta gira, Ayusherh ta ƙara kwaɓe fuska tana ɗan hararar sa shi kuma ya yi murmushi kawai.
“Ni kaina na yaba da kwarewarta domin na ɗan jima anan ina kallon ku, sai dai fa bani da labari a kan tanason shiga gasar takobi.”
Mutumin wato Jakadi ya ƙare maganar tare da duban Ayusherh da ta ɗan yi ƙasa da kanta tana warware kitson silli ɗaya, da a ka ma gashin kanta, sannan cikin muryarta mai daɗin saurare yadda kasan ana raira busar sarewa ta ce.
“Banaso ka hanani shiga Gasar ne, shi ya sa ban faɗa maka ba, amma ina ta neman hanyar faɗa ma ka ne.”
Ayusherh ta faɗa hakan ta ɗan ɗa go manyan idanunta ta dubi Tata ɗin nata.
Ga mamakinta murmushi ya yi ma ta. Ba kuma tare da ya ce Komai ba.
“Laa! Tata ka amince na shiga?.”
Ayusherh ta tambaya da sauri. Jinjina ma ta kai ya yi. Zai yi Magana suka jiyo sautin gudu ana tunkaro su, kafin wata yarinya da bata haure shekaru bakwai ba, da ita ce mai gudun, ta bayyana a gabansu tana sauke ajiyar zuciya da haki na gudun da ta sha.
“Yayankaka! Wannan gudun na lafiya?.”
Ayusherh ta tambaya da mamaki.
Sam Yarinyar ta kasa magana sai ma dafe gwiwa da ta yi da hannu ɗaya bayan ga durƙusa, nuni take musu daga inda ta fito cikin rarrabewar murya ta ke faman faɗin.
“Baána! Baána!!.”
A ɗan ruɗe wannan matashin saurayin da yake yaron Ƙanwar Jakadi da ta rasu, ya duba Yarinyar da Ayusherh ta kira da Yayankaka ya ce.
“Mene ne ya sama Baána ɗin kardai kice ciwon sa ne ya tashi?.”
Ya tambaya Hankali a ɗan tashe domin kuwa Arɗo wato mahaifin Jakadi shi suke kira da Baána (Grandfather) to yana fama da ciwo ne matsananci, kwana biyu dai an samu abin ya lafa kaɗan.
Girgiza kai Yayankaka ta yi sannan. Ta ce.
“O máyi.” (He is Died)
Maganar nata ya daki dodon kunnensu tamkar saukar aradu, domin basu tsammaci hakan ba duk da cewar yana jin jiki lokaci kawai a ke jira.
Da wani irin gudu Ayusherh ta nufa hanyar da Yayankaka ta fito ba tare da ta iya furta komai ba, yayin da Yayankaka da Tata da ma wannan saurayi suka mara ma ta baya, hankalin su a tashe, ɗaya daga cikin sauran samarin ya tsaya ya ɗauki barewar da Ayusherh ta harba, sannan suma suka mara musu baya.
Tabbas mutuwa gaskiya ce domin ta tabbata Arɗo ya riga mu gidan gaskiya, mutuwarsa ta daki mutane da yawa musamman ma iyalansa kowa ya yi kuka da rashin sa, Musamman Ayusherh da suka yi matuƙar shaƙuwa da shi, haka suka dangana suka bisa da addu'a, bayan wasu watanni kuma zuwa lokacin Ayusherh ta mayar da hankali wurin koyon wasan takobi tare da taimakon Tatan ta da kuma Mamman wato wannan saurayi da suka yi faɗan takobi, Ayusherh ta ƙara zama kwararriya ta ɓangaren, kuma bada jimawa ba, a ka gudanar da Gasar takobi na shekarar tsakanin Ayusherh da take jagorantar mutanen ƙauyen su da kuma Samari na ƙauyen da ke makwabtaka da nasu.
An fafata, a filin gasa kuma Ayusherh ta bawa kowa mamaki ganin ta da ƙananan Shekaru sai kwarewa domin duk kwarewar waɗan nan Samari sun gaza yin nasara a kan ta daga ƙarshe dai an tashi gasar kuma Ayusherh ita ta yi nasarar lashe wannan Gasar. Abin mamaki ke nan da kuma farin ciki ga mutanen ƙauyen ai kuwa sanadin haka Ayusherh ta ƙara shiga ransu matuƙa, kuma har gwarya-gwaryar shagali suka haɗa domin murna a kan nasara da Aysherh ta yi.
..
AYUSHERH
Tsaye take tana kallon yadda ruwan ke ta zubowa daga wani dogon tsauni su na cika makeken wurin da take tsaye kusa shi da a ke kira Gulbi.
Ɗabi'arta ce yin wanka a cikin wurin a wasu lokutan musamman idan ta kasance cikin yanayi mai daɗi, sai dai yau tsaye ta yi kawai ba tare da ta shiga ta yi wanka a cikin ba, kamar yadda ta saba. A kullum da koda yaushe Tata faɗa ma ta yake burinsa ɗaya shi ne ta sama Soja, lokuta da dama in ya faɗa hakan sai dai ta yi murmushi kawai ba tare ta ce komai ba. To yanzu kuma ya fara ma ta magana a kan zasu bar nan ƙauye za su koma can wata ƙasa wai Nigeria domin yanaso ya sakata a Makarantar sojoji dake ƙasar. Ita kuma har ga Allah batason barin wannan ƙauyen domin shi ne mahaifarta kuma marayarta, a yadda Tata ya faɗa ma ta Mahaifiyarta rasuwa ta yi, to ke nan hakan na nufin nan ɗin shi ne mahaifarsu gaba ɗaya. Bata san dalilin da ya sa Tata ya dage a kan sai sun bar marayarsu sun koma wata ƙasa da basu san kowa ba kuma basu da alaƙa da kowa a can.
Wannan damuwar da tunani ya sa taji batajin yin wankan. Daga ƙarshe da ta gaji da tsayuwar sai ma ƙari sa kusa dab da Gulbin da ta yi, kana ta zauna tana zura ƙafafunta ciki, sanyin ruwan kuwa ya ratsa ta, ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe Meadow Green Eyes ɗin ta.
A haka ta kasance ta ɗan daɗe a wurin kasancewar yammaci ne duhu ya fara kunno kai ya sa ta miƙe tare da komawa inda ta fito cikin ƙauyen su. Duk da cewar ba wai tsoron duhun dare take ba, dan kuwa ita sam bata san wani abu wai shi tsoro ba a rayuwarta.
..
Washe gari yau kuma zaune take a can saman makeken dutsen ta yi shiru tana kallon gefe guda, can kuma ta kai hannu tare da ɗaukar sarewar ta dake a je a gefe, ta ɗan saki murmushi domin sarewar tuna ma ta da Baána ta yi.
Ta ke ta fara busa sarewar lokaci guda kuma ta kasance cikin nishaɗi sanadin hakan.
Shi kuwa Mamman da kyar ya samu ya ƙari sa hawowa kan ƙaton Dutsen sannan ya ƙari sa gare ta, tare da zama gefanta.
Ayusherh tana jinsa batace komai ba, kuma bata dena busa sarewar ba, domin tasan ba zai wuce shi ɗin ba.
Ajiyar zuciya da yake saukewa a jejjere ne ya sa ta ɗan dakata tare da dubansa kaɗan, dariya ce ta ɗan kwace ma ta ganin yadda ya dage yana sauke ajiyar zuciya sai kace wanda ya sha tseren gudu.
“Mman! Lafiya kuwa?.”
Ta tambaye sa hakan bayan ta kirasa da sunan da take kiransa da shi tun tana ƙaramar ta har ta kawo i yanzu.
Wata Nannauyar ajiyar zuciya ya ƙara saukewa tare da ɗan dubanta yana kwaɓe fuska yadda kasan yaro mai shekaru uku ba wai Babba kamarsa mai shekaru goma sha shida ba.
“Captain Sannu da ƙoƙari kinji! A ce wannan ƙaton dutse baya yi miki wahalar hawa sam, ni kam da kyar na samu na hawo, domin ina hawa ina komawa na faɗi nayi hakan wurin sau uku amma ban dandara ba sai da na hawo nan.”
Ya ƙare maganar yana yi ma ta alamar jinjina da Babbar yatsarsa.
Ayusherh ta ɗan yi murmushi domin ita dariya ma ya bata, ita fa bata ga abin wahala ba a hawa dutsen nan, wata ƙila saboda ta saba ne, shi kuma bai saba ba, shi ne kawai.
Dubanta ya ƙara yi jin batace komai ba.
Ya ƙara kiran sunanta kamar yadda ya saba da faɗin...FOLLOW NKDS @ AREWABOOKS APP.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now