•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
I'm on Instagram as @thenainarh. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/thenainarh?igsh=YzljYTk1ODg3Zg==
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 11.
Sosai Ayusherh taji daɗin wannan bazata da Tata ya yi ma ta, kuma motar ta yi ma ta ɗari bisa ɗari, sun daɗe suna kewayen yayin ɗa na motar sannan daga bisani suka koma gida cike da nishaɗi.
*- 100, Adeola Odeku Street, Victoria Island, Lagos, Lagos State, Nigeria*
Daga yanayin yadda mutanen dake tsai-tsaye a compound na gidan suke, da kuma shigar da kowannensu ya yi, zai tabbatar maka da shirin film suke yi.
Ƴan mata ne wurin su shida sanye cikin shiga kala guda wato doguwar Gown har ƙasa da taji ado ta yi kyau, kana ganinsu dai kaga waɗan da suka yi shiga irin na biki, yayin da gefe guda kuma maza ne suma sanye cikin suit Black sai dai banda mutum ɗaya, dake zaune saman wata tulip chair ya harɗe ƙafa yana karkaɗata a hankali, idanunsa a lumshe da alama shi ne jarumi a shirin.
Can gefe kuma Amarya ce da angon a zaune sannan sai Iyaye daga gefe.
Director ne ya tashi daga kujerarsa tare da ƙari sawa wurin Camera man yana gyara masa yadda zai saita Camera yayin ɗauka, sai da komai ya daidai ta sannan Director ya bada umarni ta hanyar faɗin. “In three two one, rolling Action.” Ya faɗa tare da alama da hannu.
A yadda shirin yake shi ne Amarya da ango ne za su jefa flower idan Amarya ce ta jefa, to fa duk Macen da ta yi nasarar cafewa ita ce zata zama Amarya ta gaba a cikin shirin domin haka tsarin familyn yake, yayin da in ango ma ya jefa to fa duk namijin da ya yi nasarar cafewa shi ne zai zama ango na gaba a tsarin familyn ke nan tun fil-azal.
Da sauri Amarya da angon suka tashi daga inda suke tare da ƙari sawa wurin, flower abokin ango ya basa. Juyawa angon ya yi tare da sai tawa sannan ya jefa flower ta bayansa, kowa ya zuba ido domin gani mai rabo da zai yi nasarar ca fe flower. Wani irin zaro ido ƴan matan suka yi gaba ɗaya ganin flower ta faɗa a jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya zubawa flower da ta faɗo saman laps ɗin sa, sai kuma ya ɗauki flower tare da riƙe wa a hannu ya miƙe tsaye. Kamar yadda tsarin shirin yake, hakan ya sa ita ma Amarya ta karɓa nata flower tare da juyawa sannan ta jefa flower, haba ai nan dukkanin ƴan matan kowannensu ta daka tsalle tare da ƙoƙarin ganin wannan flower ya zo hannunta, ai kuwa cikin sa'a wacce ta kasance tafi sauran ƴan matan kyau kuma ita ce jarumar labarin ta sama nasarar ca fe flower ai nan da nan daɗi ya kusan karta, dama burinta ke nan ai tuni ta a je batun wani shirin film a gefe tana riƙe da flower ta ƙari sa wurin da yake tsaye a guje ba jira ta wani rungume sa tare da shigewa jikinsa.
Gaba ɗaya mutanen wurin suka kwalalo ido domin su ba haka suka karanta a script ba, shi kuwa Director hannu ya ɗaura a kai kamar zai fasa ihu tsaban takaici, shikenan kuma ta ɓata komai, daɓas Director ya zauna saman kujerarsa yana goge gumi da hularsa.
A hankali ya ɓanɓare ta daga jikinsa tare da zuba ma ta lafiyayyen mari, yana karkaɗa ma ta hannu alamar warning, ya tsittar da yawu cikin wani irin ɓacin rai, tare da cire farar rigar yadi dake jikinsa ya jefar cike da kyankyami, rai a ɓace ya bar wurin, shigewa ciki ya yi tare da ƙari sawa masaukin sa da a ka tanadar masa, da gudu shima Personal Assister nasa yabi bayansa haka ma Director yana fata ba fasa shirin gaba ɗaya ya yi ba domin ya san wane ne Haisam wannan kaɗan daga cikin rashin mutunci nasa ya ce ya fasa shirin gaba ɗaya.
Ita kuwa wannan Budurwar duk da marin da ta kuma ya shige ta amma wallahi ko'a jikinta domin burinta ya cika ta haɗa jiki da Haisam Dawud Nasamu.
Yaro Matashi haɗaɗɗe kuma ɗan kwalisa Burin kowace mace kuma gashi ɗa ɗaya tilo a wurin Alhaji Dawud Nasamu. Wato President mai ci a yanzu. Haisam sanannen jarumin film ne lamba ɗaya da ba a iya Nigeria ya tsaya da acting nasa ba, hatta ƙasashen ƙetare ɗaukar sa suke yi yana musu acting cikin fina-finan su, shi ya sa ko'ina ya shahara baga nan bama shi ɗin kyakkyawa ne ajin farko sai dai fa Haisam bai san wani abu wai shi mutunci da kara ba, ba ruwansa ko waye kai bai ƙi ya taka ka ya yi gaba ba, yana da matuƙar kyankyami shi ya sa a yanzu ma ransa ya yi masifar ɓaci da abin da wannan Budurwar ta yi masa haushin kansa ma yakeji da ya ɗaura hannu a jikinta.
Haisam ke nan matashin billionaire sannan Actor, Kuma Dancer, and International Model.
Yana shiga bai zame ko'ina ba sai bathroom ya sakarma kansa ruwa idanunsa a lumshe har yanzu ransa a ɓace yake kuma bai dena kyamar kansa ba na abin da Yarinyar ta yi masa.
Ƙyazama ce ita a wurinsa kai bama ita ba hatta sauran matan kallon ƙazamai yake musu a to mai za'ayi da baƙar fata shi ya sa yafi ƙaunar rayuwa a waje ba takura.
Sai da ya ɗauki aƙalla minti talatin a bathroom ɗin sannan ya fito yana ɗan jan tsaki, yayin da yake ɗaure da towel ga kuma ƙarami yana goge sumar kansa mai tsayi da a ka yi masa wani irin aski yayin da kaɗan ya zubo ya rufe masa fuska.
Kar fa duk wannan abu ya sa kuyi tunanin Haisam babu ruwansa da mata!.
Yana kula su sai dai ba irin baƙaƙe na nan da ya raina ba, cikakken ɗan soyayya ne sai dai duk da hakan bai taɓa wani abu da sunan haɗa shimfiɗa da wata mace ba iyaka sai dai a yi romance a tashi. Wannan kuma ra'ayinsa ne kuma ba mai take masa burki a matsayinsa na ɗan gata kuma Shalele a wurin iyayensa da basa ganin laifinsa a komai da zai yi sannan ba sa take masa burki a komai shi ya sa ya taso da wata iriyar halayya ta ganin kowa a ƙasa yake da shi. Haisam akwai ji da kai.
Director da P.A suna tsai-tsaye curko curko a palon kowa da abin da yake saƙawa shi dai Director fatansa bai wuce kar Haisam ya ce ya fasa shirin ba, domin ya san hakan ba ƙaramin asara zai haifar masa ba, duba da irin manyan kuɗaɗe da ya kashe ma film ɗin. Yayin da P.A sai faman harara yake watsa ma Director ƙasa ƙasa domin shima an ja ma sa wani bala'in ne dama ya ya lafiyar kura.
Daddaɗan ƙamshinsa ne ya fara isa gare su kafin ya bayyana yana taku ɗai-ɗai cikin shiga casually wata kalar Stylish riga a jikinsa mara dogon hannu da kuma buɗaɗɗen gaba, hakan ya sai ya bada damar bayyanar Thickchesk ɗin sa yayin da still yake sanye da wani Fitted Jean's, kai idan baka sani ba sai kayi tunanin yayyaga Jean's ɗin a ka yi, ta wurin gwiwa ganin yadda wurin yake a yayyage sai dai fa duk a cikin gayu ne a haka Jean's ɗin yake, zakuyi mamakin tsadarsa. Ƙafafunsa rufe cikin wani expensive comfortable sneakers yayin da fuskarsa dake a murtuke sanye cikin wani makeken Space da ya yi matuƙar dacewa da fuskar nasa mara hayaniya.
Ganin dai kamar bai lura da su ba ya sa kai zai fi ce ne, ya sa da gudu suka bi bayansa Director sai faman basa haƙuri yake tare da alƙawarin zai ɗauki mummunar mataki a kan yarinyar Amma please kar ya ce masa ya fasa.
Shi kuwa P.A faɗi yake.
“Ya Yallaɓai Abuja zamu tafi ne?.”
Bai kula su ba har sai da ya ƙari sa wurin jerin motocin sa dake a fake guda takwas cir. Ya shiga ta tsakiyar da tafi kyau da kuma tsada.
Sai a lokacin ya dubesu sannan ya yi magana a taƙaice.
“Director James ba zan iya wannan aikin ba, ka nemi wani, ina nufin na fasa.” Sannan ya dubi P.A ya ce a taƙaice. “Abuja.”
P.A ya gane mai yake nufin cikin sauri da rawar baki ya ce.
“Ya Yallaɓai na bincika babu Flight da zai tashi zuwa Abuja a dai dai wannan lokacin saboda yanayin weather na garin kuma yanzu yamma ta yi kuma...”
Bai ƙari sa ba ya tsinkayi muryarsa yana faɗin.
“Mu tafi a mota.”
Yana faɗin hakan ya jingina bayansa jikin kujerar motar tare da lumshe ido bayajin zai iya ko ƙara awa guda ne a Lagos.
Muƙut P.A ya haɗiye yawu yayin da Drivern ya rufe motar. Shi kuwa Director kasa koda motsi a wurin ya yi. A haka motocin a jere suka fita daga gidan harda baɗe shi da ƙura dan yaƙi ya matsa wa.
Ƙasa ya yi zai zube Mataimakin sa ya yi saurin taro sa shima ransa ba daɗi haka ma sauran mutanen dake wurin tun daga masu ɗaukar shirin da sauran ƴan wasan.
**
P.A sai kallon Agogo yake yi hankali a tashe tabbas akwai kasada tafiyar su a wannan daren, gashi daga Lagos zuwa Abuja ba nan kusa ba. Gashi Haisam yaƙi ya haƙura koda a hotel ne su kwana ko kuma su bari zuwa lokacin da za'a sama jirgin da zai tashi zuwa Abujan. A haka dai suka ci gaba da tafiyar. Gashi Yamma ta yi dan a lokacin wuraren biyar da rabi ne na yamma.
*
A hankali ya buɗe fararen idanunta sakamakon sautin shigowar kira da wayarsa ta yi, sunan Nusra ya bayyana saman screen na wayar.
“Haisam!.”
Nusra ta kira sunansa a lokacin da ya ɗa ga kiran, bata jira ya amsa ba ta ƙara faɗin.
“Kana lafiya kuwa?.”
“Yeah, what's up?.”
Ya faɗa cikin taushin murya.
“Tun da na tafi baka kirani ba shi ya sa nayi tunanin ko ba lafiya ba, sai dai kuma naji daɗi da ya kasance kana lafiya, ba ma wannan ba kasan wani abu kuwa?.”
Ta yi masa tambayar cikin muryar da take nuna zallar zumuɗi da take ciki.
“Nayi nasara Haisam ina nufin nayi nasarar zama ta ɗaya a fashion championship da a ka gabatar a Dubai, kaga hakan yana nufin nima na zama International Model.”
Ta ƙare maganar cikin wata kalar murya mai cike da annashuwa tsaban farin ciki kamar ba Nusra da ya sa ni ba, koda yake Nusra Nusra ce sai dai Nusra daban take zama idan ta kasance tare da shi she was so caring and loving a kan sa, ya san hakan amma yake sharewa.
“Nice to You, Congratulations and All the best.”
Ya faɗa domin tayata murna. Nusra ta ɗan yi murmushi tana faɗin.
“Thank you.”
Sai kuma ta ɗan yi shiru shima hakan.
“Zan katse kiran, ka kula da kanka, and I Love you.”
Ta faɗa da kalar muryar da ta basa magana a garesa, bai amsa ma ta ba ya katse kiran, Nusra tabi wayar da kallo, tana sauke ajiyar zuciya.
*
Zuwa yanzu sun daɗe da fita daga Lagos kuma dare ya yi sosai sai dai shi Haisam ko'a jikinsa idanunsa ma a lumshe suke kamar mai bacci.
Wani irin birki motocin suka ja a sakamakon abin da suka gani, kafin su yi wani yunƙuri lokaci guda ƙarar harba harbe ya cike wurin kafin ƴan fashin da kowannensu hannunsa ɗauke yake da Manyan bindigu masu hatsarin gaske, gaba ɗaya suka zagaye motocin ga kuma fuskokinsu dake a rufe baka iya gani komai sai jajayen idanun kowannensu.
Wannan ke nan....✍️
*Prep-Room, Disclosed Location Abuja.*
Dukkanin su zazzaune suke cikin Ɗakin da ya fi kama da na taro kowannensu zaune saman desk sun ɗaura hannu saman dogon table dake wurin, sanye suke cikin shiga kala ɗaya, baƙaƙen kaya haɗe da ja kaɗan fuskokinsu a rufe yake da hular rigar jikinsu, a haka suka fara taron, wanda ya kasance shi ne shugaba a cikinsu yana tsaye gaban farin allon wanda hasken kwan wutan projector ya haskesa, jiki kuma ɗauke da rubutu da Manyan baƙi. *SECRET OF US*
Da alama sunan ƙungiyar ta su ke nan, magana ya yi kaɗan kafin ya bawa kowannensu damar faɗar damuwarsa.
Ɗaya bayan ɗaya suke tashi kowa yana faɗar damuwarsa ko kuma wani buri nasa su kuma sai su tattauna a kan yadda za su ɓullo wa al'amarin a ka haka har a ka zo kansa.
Alhaji Dawud Nasamu da shima ɗaya ne daga cikin manyan shugabanni na ƙungiyar ta su ta *Secret of Us* kuma mai faɗa a ji, magana ya fara kamar haka.
“Wato Babban abin da ke damu na shi ne a kan zaɓe da ya gabato sam ban yi duk wasu ayyuka da na alƙawarta zan yi ba, gashi zaɓe ya gabato sannan bana da gwarin gwiwa a kan zancin zaɓen wannan karon sakamakon Abokin takarata da yake shiga min hanci da ƙudunduni, kuma na lura talakawa suna ƙaunarsa a yanzu shi ne matsala ta kafin a iso kan mutane ina nufin talakawa dan su wannan nasu mai sauƙi ne.”
Ya ƙare maganar yana kaɗa kai yadda kasan mene ne.
“Wannan ai ƙaramin abu ne Alhaji Dawud ko ka manta ƙarfin iko da wannan ƙungiyar tamu take da shi ne ga ka kuma President guda ai ka saka a ranka ka SAMU kawai kamar yadda inkiyarka take NASAMU.”
Gaba ɗaya suka kece da dariya har da wanda ya yi maganar da shi kansa Alhaji Dawud Nasamu.
Ci gaba da tattaunawa suka yi a tsakaninsu na yadda za su ɓullo wa al'amarin sun daɗe sosai kafin daga bisani suka watse.
Alhaji Dawud Nasamu ya shiga cikin ɗaya daga cikin jerin motocin sa dake fake, alamar jinjina Matar dake zaune a motar ta yi masa tana ɗan murmushi, shima ya mayar mata da murmushin yana faɗin. “Nice to You Dear you're so amazing in all the time.”
Ta ɗan yi murmushi gefe tana faɗin. “It all for you.” Ta yi maganar tare da ɗan kwantar da kanta a kafaɗarsa. A haka suka fara tafiya suka baro wurin Direct gidansa suka nufa da shi bayan shafe kusan minti talatin suna tafiyar sannan ne suka iso.
Daga shiga unguwar zakasan ka shigo wuri na manyan mutane wurin da masu mulki ne kawai ke zaune da iyalansu sunan yanki shi ne The President Area a nan gidan Gwamnati take shi ya sa sunan yankin ya kasance haka.
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
