•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Wattpad @Nainarhkd3.
..Episode 7.
“Am nace ba, wai wacece ke ɗin? Kuma mene ne kike faɗa ne, ni sam bana fahimta.”
Ya faɗa yana dubanta cikin rashin gane inda ta dosa da kalamanta da kuma yanayinta, nuna wa take tamkar ta sansa a baya.
Cikin harshen fulatanci ya yi maganar, saboda haka ta fahimta, lokaci guda murmushin dake ɗauke saman fuskarta ya gushe, da jin kalamansa. Ita ma cikin harshen fulatanci ta ce.
“Mamman! Baka gane ni ba da gaske Ayusherh ce fa?.”
Ta yi maganar cikin sanyin murya idanunta kafe a kan sa.
Shi kuwa cikin rashin fahimta yake dubanta, ya ɗan yi shiru kamar mai tunani, a nufinsa wata ƙila ya tuno inda ya santa, sai dai ya kasa tunawa domin bai santa ɗin ba.
“Abyaz! Shi ne sunana Am not a Mamman hasali ma ban shi ba.”
Ya yi maganar yana jinjina ma ta kai alamar dai da gaske bai san wani Mamman ba kuma ba sunansa Mamman ba.
Zuba masa ido Aysherh ta yi tana yi masa wani irin duba cikin rashin yarda da kalamansa duk da ba duka take ganewa ba dan yana haɗa wa da wani yaren da ba fulatanci ba.
“Waye kai.”
Ta faɗa tana ƙoƙarin saita kibiyarta a kansa.
Abyaz ya ƙara zaro ido ganin abin da take shirin yi.
“Na faɗa Miki Abyaz! Sunana.”
Ya faɗa yana ɗa ga hannu sama.
A dake ta ƙara tambayarsa da faɗin.
“Mene ya kawo ka nan, kuma me ya sa kake bibiyata tun ɗazu ina lura da kai?.”
Da sauri ya ce.
“Motarmu ce ta sama matsala a hanyar mu na shigowa shi ne a ka tsaya gyara ni kuma na fara kewaye dajin shi ne na hango ki, na tsaya ganin yadda kike ke kaɗai kuma mace a irin dajin kinata training kamar...”
“Mene ne training?.”
Ta katsesa da faɗin hakan, bayan ta ɗan yi ƙasa da doguwar kibiyar nata mai yanayi da Bow, ɗabi'arta ce in zata fita daji ɗayan biyu ne kodai ka ganta da row and bow ko kuma wannan doguwar kibiya.
“Ina nufin horo.”
“Me ya sa kake kama da Mamman ɗina?.”
Ya zaro ido jin tambayar da ta yi masa.
“I don't know.”
Ya faɗa yana taɓe baki tare da ɗage kafaɗa.
A harzuƙe Ayusherh ta ƙara ɗa ga kibiyar zata saita shi. Da sauri ya ce.
“Mi anda, Mi andani.”
A yanzun ya maimaita abin da ya faɗa cikin harshen fulatancin kamar yadda ya fahimci harshen kaɗai takeji.
Jinjina kai ta yi tare da mayar da kibiyar ta soke ta a ƙugunta jikin doguwar rigar jikinta.
Sannan ta kai hannu ta damƙo kwalarsa ta juya tare da fara taku da shi a haka. Abyaz cikin mamaki yake faɗin.
“Hey! Hey!! Ina ne zaki kaini haka, ki dakata mana.”
Ya yi maganar yana biye da ita tamkar raƙumi da akala. Sai dai Ayusherh taƙi kulasa haka nan taƙi sakinsa.
Shiru ya yi yana biye da ita, yana kuma jinjina ƙarfin hali irin na wannan Yarinyar daji, ko ina zata kaisa? Allahu Aalamu. Ba wai dan ba zai iya gwacewa ba ne ya barta ta ci gaba da tafiya dashi a haka. A'a kawai nishaɗi hakan ya saka shi.
Ayusherh bata sakesa ba har sai da suka shiga cikin ƙauyen kowa da mamaki yake dubansu sai dai ko'a jikinta shi kuwa bata su yake ba, ta iya yake, yana cikin wannan shauƙi ne da ya ɗibesa yaji ta wancakalar da shi gefe, bayan ta saki kwalar nasa.
Sai a lokacin ya lura da inda suka shigo wani gida ne na kara da ɗakunan suke na bukkoki.
Zuba ma laɓɓanta ido ya yi yayin da ita kuma ta dage sai kiran sunayen mutanen gidan take yi, faɗi take.
“Yâ tâ! Ali, Yayankaka, duk kuna ina ne Tata! Tata!!.”
Harɗe hannu Abyaz ya yi a ƙirji tare da zuba ma ta ido dan shi ko'a jikinsa.
Yâ tâ ce tare da Ali suka fito daga ɗaki yana ɗan taimaka ma ta domin bata iya tafiya sosai.
“Mene ne ya faru kike mana wannan kira?.”Yâ tâ ce ta yi ma ta tambayar lokacin da suka ƙari sa fitowa daga ita har Ali basu lura da Abyaz dake tsaye ba.
“Mamman!.”
Ayusherh ta faɗa tana yi musu nuni da saitin da Abyaz yake.
Cikin rashin fahimta suke dubanta jin sunan da ta kira, kafin su kai dubansu ga saitin da take nunawan, Yâ tâ faɗi take.
“Ke ƴar nan me kika sha yau kuma da Mamman kika tuna Allah Sarki maragayi...”
Sauran maganar nata ya maƙale a harshen ta sakamakon fuskar wannan saurayin da ta gani.
Shi Ali ba wani wayo ne da shi ba, saboda haka bai wani tsorata ba amma jikinsa rawa yake saboda yasan dai wanda ya mutu baya dawowa, amma yau gashi ƙiri-ƙiri rana tsaka Mamman ya dawo kuma dariya ma yake yi musu.
Yadda kasan mazari haka jikin Yâ tâ ya ɗauki rawa, bakinta ma kansa rawa yake yi na tsaban tashin hankali da tsoro, kawai sai ta saka kuka ta fara goge hawaye jikinta bai bar rawa ba ta kama salati kan ta kai wancan ta saki ta ɗauki wani faɗi take.
“Allahumma Anta.. La'ilahaillah..” Sai kuma ta saki ƙara tana kiran Fatalwa. Dai dai lokacin ita na Yayankaka ta fito daga bayan gida, sakamakon sunanta da taji Yayartasu Ayusherh na kira.
Sai a lokacin Ali ya sama damar motsa wa ai kuwa ɗaki ya nufa direct yayin da Yayankaka ta mara masa baya dan a ɗan taƙin ta fahimci abin da yake faruwa, haba sai ga Yâ tâ ta taka ƙafarta wurin gudu a ka shiga tsere na neman wurin ɓuya tsakanin ita da su Ali. Ɗaki suka faɗa tare da garƙamo ƙofar katakon garam.
Sakin baki Ayusherh ta yi tana kallon ikon Allah. “To mene ne abin tsoron kuma?.” Ta tambayi kanta sai dai babu mai bata amsa.
Shi kuwa Abyaz tsananin mamaki ne ya hana shi motsawa, sai kuma ganin reacted na mutanen gidan ya saka shi darawa, domin abin nasu ba ƙaramin dariya ya ba shi ba. Briefly dai ya fahimci kama yake yi da wani ɗan uwansu wanda ya mutu, shi ne ganinsa a yanzu da irin fuskar ɗan uwan nasu ya firgita su, sai dai yana mamakin yadda ita wannan Yarinyar dajin ko'a jikinta, ba wani tsoro a tare da ita.
Dariyar da yake yi ne ya dawo da Ayusherh cikin hayyacinta. Ta dubesa a kufule, dama dab suke da juna, ai kuwa a harzuƙe ta kai masa kyakkyawan naushi a ciki. Ai kuwa ya yi ƙasa yana riƙe ciki dan ba ƙarya yaji zafi kuma shammatarsa ta yi.
Ƙari sawa bakin ƙofar ɗakin da suka shiga Ayusherh ta yi, cikin kwantar da murya ta fara faɗin.
“Yâ tâ, Ali, Yayankaka, Dan Allah ku fito mana, wannan fa ba Mamman ba ne wani ne fa dan shi daga birni ma ya zo yace ma sunansa Ab... Aby..”
Ganin ta kasa ƙari sawa ne. Ya sa Abyaz ƙari sa ma ta da faɗin. “Abyaz.”
“E Abyaz sunansa dan Allah ku bar jin tsoron nan ku fito.”
Duk yadda Ayusherh taso ta lallaɓasu su fito abin ya cutura, sai ma ce ma ta Yâ tâ da ta yi.
“Ƴar nan ki barmu kawai muddun ba ce mana kikayi ya tafi ba to fa ba inda zamu fito, kema ina mai baki shawara da ki yi gaggawan neman wurin ɓuya, ki a je wannan taurin zuciyar a gefe domin ba'a nunawa Fatalwa da aljanu wannan in ba haka ba labari ya sauya.”
Ɗan tausayi tsohuwar ta bawa Abyaz jin yadda take maganar da alama har lokacin a firgice take. Ƙari sawa wurin ƙofar shiga ya yi, sannan ya fara magana da faɗin.
“Grannny ki fito nayi miki bayani ba Fatalwa ba ne, ni mutum ne sunana Abyaz kuma ba zan cutar daku ba.”
Ai kuwa a maimakon jin kalamansa ya saka tsoron dake tare da su ya ragu, ai sai ƙara firgicewa da suka yi musamman ma yaran.
“Ƙaryar yaudara...”
Yâ tâ ta faɗa tana shirin afkawa ƙarƙashin gadon ta mai rumfa.
A fusace Ayusherh ta juya garesa, ta kamo kwalar nasa ta yi waje. Domin ta fahimci muddun ba gidan ya bari ba to fa babu wani irin lallashi da zai sa su Yâ tâ su fito.
“Da alama ke jaruma ce sai dai kina da zafin kai...”
Abyaz ya faɗa dai dai lokacin da ta yo waje da shi tare da sakin kwalar nasa ta juya zata koma gida.
Sai dai maganarsa ta dakatar da ita. A hankali ta juya tare da yi masa duba ɗaya ta watsar tana shirin tafiya ne ta ji amon wata murya a gefensu tana faɗin.
“Alhamdulillah My Son, ashe ba ɓata kayi ba, baka ga yadda hankulanmu ni da Daddynka ba yadda ya tashi ganin mun nemeka an rasa.”
Matar da duba ɗaya zakayi ma ta kasan cewa cikakkiyar ƴar gayu ce kuma wayyayyiya da boko ya gama ratsa ta ga Naira, ita ke wannan maganar yayin da ta ƙari sa wurin Abyaz tare da rungumo sa tana goge kwalla dan ba ƙarya hankalinta ya matuƙar tashi da basu gansa ba, tana son yaronta da yake ɗaya tilo a gare su ita kanta batasan adadin son da take yi masa ba.
“Ayusherh.”
Ayusherh da ta saki baki tana kallon ikon Allah taji an kira sunanta juyawa ta yi cikin sakin murmushi dan Muryar ta zauna a kunnenta.
“Na'am Tata..”
Ayusherh ta amsa tana duban Tatan nata sai kuma idanunta ya sauka a kan Mutumin dake tare da shi, da yake sanye cikin suit Black da suka yi bala'in karɓarsa, kamanni sosai taga mutumin yake yi da Abyaz, kuma hakan ya matuƙar bata mamaki ta tabbata dai wannan ba shi ne Mamman ɗin ta ba.
“Mom, Dad! Wannan ita ce Ayusherh kuma ita ce ta taimaka min domin makuwa nayi.”
Cewar Abyaz da sauri Ayusherh ta dubesa shi kuwa ya sakar ma ta murmushi, sai taji ba daɗi na abin da ta yi masa.
Alama ta yi masa da ya yi haƙuri, tana ɗan rau da ido. Dariya ma taso basa, amma sai ya girgiza ma ta kai alamar ba komai, Ayusherh ta yi murmushi.
“Amma na gode miki sosai Yarinyata Ayusherh Allah ya yi miki Albarka.”
Cewar Matar da Ayusherh taji Abyaz ya kira da Mom, kuma ta fahimci Mahaifiyarsa ce.
Shima Mahaifin godiya ya yi ma ta, ita dai Ayusherh tana tsaye. Tata ne ya ce.
“To Alhaji muje na nuna muku masaukin naku. Zuwa kafin a gama gyara motar taku Moddibo ya kawo muku.”
Amsa wa suka yi sannan suka yi gaba, ganin haka ita ma Ayusherh tabi bayansu saboda Tata ɗin ta. Sun ɗan yi nisa da tafiyar Abyaz da ya lura tana bin su, ya ɗan yo baya suna jerawa tare da ita.
“Ɗazu kin yi tambaya a kan me ya sa nake kama da Brother naki da ya mutu ba?.”
Kallon sa Ayusherh ta yi ba kuma tare da ta dakata da tafiyar ba. Sai dai batace komai ba. Bai damu ba, ya ci gaba da faɗin.
“Doppelganger! Ta yiwu shi ɗin Doppelganger na ne.”
Ayusherh ta ce.
“Mene ne shi wannan abun.”
Ta tambaya dan ba za ta iya maimaita kalmar ba.
“Idan ya kasance an sama wani mutum da yake Rayuwa a wani wurin kuma a ka ƙara samun wani mai tsananin kamanni da shi wanda shima Rayuwa yake yi a wani wurin daban, kuma basu haɗa duk wata alaƙa ta jini ba, hasali ma ba yarensu ɗaya ba, ba kuma ƙasa ɗaya suke ba, ya kasance kowannen su a mabanbantan sassa na duniya yake Rayuwa. Wannan shi a ke kira da Doppelganger.”
Jinjina kai Ayusherh ta yi cikin fahimta da kalamansa, sai a lokacin ta yi masa kallon nutsuwa.
Shi wannan Abyaz ɗin ya kasance kyakkyawa ne ajin farko ga fatarsa da take jajur, dogo ne, bashi da jikin mara, sannan ya yi shiga ne in casually, Graphic T-shirt da kuma Fitted Jean's ya ɗaura Hoodie na gayu saman T-shirt ɗin, yayin da ƙafafunsa ke rufe cikin wasu expensive sneakers, a kansa kuwa wata Baseball cap ce da ya saka a wani karkace, ga wani expensive wrist dake hannunsa kana ganinsa dai kaga Cikakken wayayye kuma ɗan gayu da yake bawa gayu haƙƙinsa. Wani irin ƙamshi mai daɗi yake fitarwa.
Ayusherh ta ɗan lumshe ido bayan ta gama ƙare masa kallo a sace, bata san me ya hanata ganin wannan kyan nasa a ɗazu ba.
“Ya ne Yarinyar daji?.”
Maganar da ya yi ne ya sa ta dubesa, ta ɗan harare sa.
A taƙaice dai wannan shi ne dalilin haɗuwar Abyaz da Ayusherh.
Mahaifin Abyaz ya kasance Silviculturist ne wato dai Ma'aikacin gwamnati mai kula da Daji da mutanen cikinsa har ma da ci gaban dajin, to wannan karon aikinsa ne ya biyo ta ƙauyen Mayo-Danay sati guda zai yi shi ya sa ya taho familynsa domin su ne suka buƙaci hakan, domin Abyaz cewa ya yi ai suma sa buɗe ido a dajin.
WANNAN KE NAN
Kwanakin da suka biyo baya sun kasance Unforgettable ne a wurin Ayusherh, domin tun bata biye wa Abyaz amma nacinsa a gare ta ya sa ta saki jiki sosai da shi, har wasu ranakun take raka sa cikin ƙauyen ta zagaya da shi ko kuma su shiga daji ta yi ta nuna masa abubuwa iri iri, a wannan taƙin ne ya fahimce ta da kuma gaba ɗaya Rayuwarta a yadda ya fahimta mahaifinta wato Tata yana da wani kyakkyawan buri a kanta da yakeso ta cimma a Rayuwarta. Duba da yadda a duk ranakun duniya yake ware lokaci sau biyu a rana da safe da kuma yammaci yake bata horo na musamman. Abin yana matuƙar ɗaurewa Abyaz kai ganin yadda Tata ya iya bada horo tamkar a makarantar sojoji ko ƴan sanda, bai ƙara shan mamaki ba sai ganin kwarewar Yarinyar ƙwaƙwalwarta yana matuƙar ja, kuma gefe guda ta nace sai ya koya ma ta yaren da yake yawan yi wato Turanci, to a hakan yake koya ma ta ƙananan abubuwan da ba'a rasa ba, kuma dalilin hakan ya gano Burin Mahaifin nata a kan ta na zama Soja. A yadda ya fahimta kamar ita hakan bai kwanta ma ta ba, saboda tana ganin ba zata iya ba.
Amma da dabara Abyaz yake cusa ma ta ƙaunar abin a ranta har yake faɗa ma ta cewar ta hanyar zama sojan ne kawai zata iya kawo ƙarshen irin azzaluman ƴan ta'addan da suka kai farmaki ƙauyensu, ya ƙara da faɗin gata kuma jaruma ta musamman zama soja ba zai ma ta wahala ba, da irin waɗan nan kalaman Abyaz ya yi amfani wurin taimakawa Tata a kan shawo kan Ayusherh ai kuwa nan da nan kwadayin zama Soja ya shiga ranta, ta ƙara mayar da hankali a kan koyon training iri iri da Tata yake koya ma ta, hatta shi Abyaz ba'a barsa a baya ba, sai dai Ayusherh bata tsayawa idan ma ya ce shi zai yi ma ta training ɗin a cewarta ba abin da ya sani dangane da harkar. Shi kam Abyaz sai dai ya yi dariya. Abin da Ayusherh bata sani ba shi ne Abyaz yana karatu ne a makarantar sojoji a ƙasar waje. Yanzun ma hutu ya dawo shi ne dalilin da ya sa shi da Mom ɗin sa suka biyo Dad ɗin sa wannan tafiyar na aiki.
Cikin kwanaki bakwai kacal wata iriyar shaƙuwa ce mai tsafta da ban mamaki ta shiga tsakanin Ayusherh da Abyaz.
Ta gefe guda kuwa tuni Abyaz ya gama magana da Dad ɗin sa a inda ya roƙe sa da a saka Ayusherh a makarantar sojoji domin ta hakan ne kawai Burin Mahaifinta zai cika. Ya roƙi hakan ne bayan ya basa labarin Ayusherh. To da yake Mahaifin nasa Mutumin Kirki ne ba ɓata lokaci ya sama Tata da maganar har yake sanar da shi ya nema wa Ayusherh gurbin shiga makarantar sojoji dake Abuja, zuwan da zai yi gaba tare zasu tafi gaba ɗaya saboda suga Makarantar ita kuma Ayusherh ta fara karatu.
Tsaban farin ciki Tata har yana hawaye dama burinsa ke nan ganin ya saka Ayusherh a makarantar sojoji, ai kuwa ya yi ta zuba wa Mahaifin Abyaz godiya tamkar bakinsa zai kasu.A yau ne kuma sati ta cika da zuwansu Abyaz ƙauyen Mayo-Danay kuma a yau ɗin sun gama shirya wa tsaf domin komawa inda suka fito. An gama shigar da komai nasu a mota, hatta Mom da Dad sun shiga Abyaz kawai suke jira.
A hankali suke takawa domin ƙari sawa motar kana ganin idon Ayusherh zaka fahimci ta zubar da hawaye karo na biyu ke nan tun da ta yi wayo da ta yi kuka, na farko dai a dalilin rasuwar Mamman ɗin ta na biyu kuma shi ne yanzu saboda Abyaz da suka yi mugun sabo zai koma.
A hakan ma ya samu da kyar ya lallasheta ta haƙura ta dena kukan, shi ne ya samu zata rako sa wurin motar.
Handkerchief ɗin mai kyau da yake fitar da ƙamshi mai sanyi ya ciro a trouser pocket ɗin sa, tare da miƙa ma ta yana faɗin.
“Take it. Ki goge hawayen, kina ta damuwa tamkar an ce miki mutuwa zan yi, ko kin manta nayi miki alƙawari ne a kan kina shiga Military School nima zan tattaro karatuna na dawo Nigeria mu ci gaba tare ko kin manta hakan ne?.”
Girgiza kai Ayusherh ta yi bata ce komai ba.
Ya ɗan sosa ƙeya lokacin da suka ƙari sa dai dai wurin motar sannan ya dakata da tafiyar tare da dubanta ya ce.
“In sha Allah, one day your dreams will come true...”💖
“Sankiyu.” (Thank you.)
Shi ne abin da Ayusherh ta iya faɗa, ya yi ma ta kyakkyawar murmushi tare da shiga back seat na motar ya zauna.
Wannan shi ne maganar su ta ƙarshe kafin suka yi sallama a ka tada motar suka fara tafiya.
Ayusherh da Tata dama Ali sai kuma wani mutumi wato mai gari na ƙauyen da kuma wani matashi a tare da shi suna nan tsaye har motar ta ɓacewa ganin su.
Gida su Tata suka koma Ayusherh tanajin gaba ɗaya kewa ya rufe ta yadda kasan sun yi Shekaru da sanin juna ita da Abyaz.
UNEXPECTED HAPPENED!!!.
A yammacin Ranar labari ya isa ga ɗaukakin mutanen ƙauyen na wani hatsari da ya afku da Ahalin da suka baro ƙauyen a safiyar Ranar. Lamarin shi ne sun yi wani mummunar hatsari kuma gaba ɗaya sun rasa ransu sakamakon ƙonewa ƙurmus da motar ta yi.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...”
Wannan shi ne kalmar da Ayusherh ta iya faɗa lokacin da taji labarin kafin ta zube ƙasa a sume.
Sosai Ayusherh ta shiga cikin tsananin ruɗu da tashin hankali da kuma damuwa na faruwar wannan al'amari da hakan sai da ya kaita ga ciwo sosai, domin ta matuƙar saka damuwa a ranta. Sai da a ka shafe tsawon wata guda da faruwar hakan sannan a ka samu ta fara dawowa dai dai.
A wannan taƙin ne kuma saƙo daga birni ya zo ma Tata daga hukumar Makarantar da Mahaifin Abyaz ya nema wa Ayusherh. Ashe tun kafin barinsu garin ya yi ma ta komai da komai ta fara zuwa kawai ya rage. Shi ne yanzu suka sama noticing daga hukumar Makarantar a kan lokacin fara zuwanta ya yi hakan kuma ya yi dai dai da aikin Driving da Tata ya samu a birnin cikin garin Abuja. A wani Company.
Sun kuwa yi farin ciki sosai da wannan al'amarin, kuma sun ƙara yima iyayen Abyaz da shi kansa addu'a sosai a kan yadda suke yi dan basu manta da su ba, dama sauran ƴan uwansu da a ka kashe, nan da nan kuwa suka fara shirin komawa birni. Sai dai fa Ayusherh ta ce ita ba inda zata.
Lallashin Duniyar nan Ayusherh taƙi. Sai da Tata a karo na farko da ya yi ma ta jan ido sannan suka samu lokacin da za su tafi ta bisu. A can Birnin ma sai da suka haɗa da tuna ma ta da burin shima Abyaz ɗin ke nan ta zama Sojan, idan ta ce ba zata je makarantar ba, batayi masa adalci ba. To fa da irin waɗan nan kalamai ne suka samu Ayusherh ta dawo musu dai dai kuma cikin ikon Allah ta fara zuwa tsadaddiyar makarantar ta Royal Military Academy, Abuja.BAYAN WASU SHEKARU!
.......❤🔥
*_AYUSHERH! TA GIRMA 💃 TSAMMACI ABIN DA BA'AI TSAMMANI BA!!🔥_*
.......🪄
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...