17

6 0 0
                                        

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)

                                   https://chat.whatsapp.com/IV4urJf4kuL7656LTR8Zj5

        BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.


*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*

Episode 17.

Da ƙari sawarsu Barrack ɗin fitowa suka yi bayan kowannen su ya yi parking a wurin da ya dace. Lieutenant Hammad ne ya tasa ƙeyar Sa'idu zuwa ciki. Yayin da Ayusherh ta juya baya tana amsa kiran waya da ya shigo ma ta,  ita kuma Jasmine tana tsaye daga gefanta jira take ta amsa wayar su ƙari sa ciki.
Kammala wayar Ayusherh keda wuya ta juya domin tayima Jasmine magana shi kuma a dai dai lokacin ya ƙari so wurin, tun shigowarsu cikin Barrack ɗin yake tsaye yana kallonsu har ta fara wayar da kuma zuwa yanzu da ta gama ta juya kai tsaye idanunta suka faɗa cikin nasa idanun ya yi tsaye yana kallon ta tare da sakar ma ta wani tattausan murmushi, ita ko Ayusherh da abin ya zo ma ta a bazata sai ta yi zuru ta kuma kasa cire idanunta cikin nasa sai ƙif-ƙifta idanun take, Lieutenant Hammad da ya dawo wurin ya buɗe baki yana shirin magana sai ya fasa ya tsaya ganin ikon Allah kamar yadda ita ma Jasmine ta maƙale cike da mamaki.
Ayusherh ƙoƙari take ta tuna inda tasan wannan fuskar amma kafe ta da ido da ya yi yasa ta rasa ta inda zata fara tunanin.
“I like you.”
Ya faɗa ba tare da ya cire idanunsa a cikin nata ba.
Sai idanunta suka ƙara girma jin kalmar da ta fito daga bakinsa, kafin ta yi wani yunƙuri ya ƙara faɗin.
“Yes! Da gaske nake ina son ki.”
Ya faɗa tare da ɗan ja baya, sai kawai Ayusherh ta tsinci kanta da galla masa harara sannan ta yi gaba, da sauri Jasmine ta bi bayanta dan tun kallon farko da ta yi masa ta gane Haisam ne, sai dai mamakinta bai wuce na ganinsa da uniform na soji ba.
“Hararar ma kyau take ƙara ma ta, ya Ubangiji ina ƙaunar wannan Baiwar taka.”
Ya faɗa yana ɗan shafa ƙeyarsa fuskarsa tab da annuri.
Sun fito daga elevator Jasmine tana shirin yin magana suka ji wata murya a ta bayansu an yi magana.
“Captain ko?.”
Jin abin da a ka faɗa ne ya sa su duka suka juya da mamaki don ganin wanene, idanunsu ya sauka a kan wani ƙyamurarren Mutum sai dai kana ganinsa kaga ƙaƙarfa uniform ne na soji a jikinsa.
“..shi ne fa Lieutenant General (LT GEN) mataimakin General Lamrat.”
Jasmine ta faɗa ma Ayusherh ƙasa ƙasa. Jinjina kai Ayusherh ta yi tare da faɗin.
“Hello Sir.”
Bai yi magana ba sai ido da ya zuba musu na ƴan sakanni sannan ya jinjina kai tare da faɗin. “Hello Captain ya fama?”
Ayusherh suka kalli juna sai ta amsa da faɗin. “Alhamdullilah.” Duk da cewar ta ga sunan shi ba musulmi ba ne. Ka ɗa kai ya yi sannan ya zagaye su ya wuce duk suka bi shi da kallo.
“Lieutenant General Daniyal Adeola.”
Suka faɗa sunan nasa kusan a tare. Sai kuma Ayusherh ta girgiza kai domin ita tun zuwanta Barrack ɗin bata taɓa haɗu wa da shi ba sai yau, office ɗin General Lamrat suka shiga bayan sun nema iznin shiga an basu.
Tsaye suka hangota gaban wasu frames masu ɗauke da hotunan sojoji iri iri ta zuba musu ido, tana duban kowanne kamar tanason gano wani abu a tattare da pictures ɗin. Shigowarsu ne ya sa ta juya tare da komawa mazaunin ta ta zauna tattaunawa suka ɗan yi kaɗan game da aiki sannan General Lamrat ta ƙare maganar da faɗin.
“Akwai Lieutenant General Daniyal Adeola yau ya dawo bakin aiki bayan shafe watanni bayan dakatar da shi da a ka yi bisa wani al'amari da ya faru, to in anjima idan za'ayi meeting zai gabatar da kansa a gareku.”
“Okay tohm Allah ya kai mu.”
Ayusherh ta faɗa suna miƙe wa, sannan suka nema izinin fita kana suka baro office ɗin suka koma na Ayusherh. Jasmine da kamar jira take su shiga office ɗin ta fara faɗin.
“Woww Haɗaɗɗen Handsome haka amma nayi mamakin kasancewar sa soja.”
Ta faɗa tana ɗaura hannu a fuskarta cike da zumuɗi.
“Wanene kuma haka?.”
Ayusherh ta faɗa a fizge tamkar bata gane wanda Jasmine take magana a kai ba.
Jasmine ta juya tana fuskantar Ayusherh da ta zauna a kujerarta da mamaki.
“Haisam mana.”
Jasmine ta bata amsa sannan ta ƙara da faɗin.“Ai ina baki shawara kyauta Captain muddun da gaske yake yi to fa ki amince kawai dan kuwa samun mutum kamar Haisam data ko'ina ya yi 101% zai yi wahala, shi dai ga kyau ga ilmi kuma sananne gashi daga babban gida, Kai kai abin da yawa fa.”
Jasmine ta kai maganar tare da zama bisa kujerar dake fuskantar Ayusherh har da wani lumshe ido.
Bagarar da zancen Ayusherh ta yi ta hanyar ɗauko wani zancen daban, duk kuwa da yadda Jasmine taso a ci gaba da zancen Haisam.
Ita ko Yusra ko bayan Nusra ta a je ta bank da take aiki, bata fi mintina talatin ba ta fito daga bank ɗin sannan ta hau cab ya kaita can wani restaurant sai kawai ta zauna a can ta ci gaba da aikin da take yi ta cikin Laptop ɗin ta, bata fi mintina goma da zama ba wanda take jira ya ƙari so kamar yadda suka tsara ya bata bayanan da suke a hannunsa, sun kai minti goma suna tattaunawa kafin daga bisani ya tafi... ita kuma sai da ta gama komai sannan ta bar restaurant ɗin kai tsaye gida ta wuce domin su haɗu da Kamasho kamar yadda ta ce ya sameta a gida sannan ta gefe guda wannan binciken da take yi gaba ɗaya ya sakar ma ta da jiki ita kanta bata san ya ya ƙarshen zai kaya ba sai dai jikinta ya yi sanyi da abin da ta fara ganowa dangane da Kawun nata Mr President.
Ayusherh da yammaci lokacin ta fito domin tafiya gida dan ta gama aikinta na yau, ƙari sawarta wurin da ta yi parking motarta sai kawai ganinsa ta yi zaune a kan motar yana sakar ma ta wannan murmushin nasa.
Ɗan dakatawa ta yi da tafiyar cike da mamaki take dubansa sai kuma ta sha re tare da ƙari sawa wurin motar kafin ta ce wani abu ya riga ta da faɗin.
“Barka da ƙari sowa Battle Angel a taimaka a kula wannan ƙaramin masoyin da soyayya ta gama wujijjiga zuciyarsa da ruhinsa.”
Ya yi maganar yana dai dai ta tsayuwarsa bayan ya sauka daga motar sai ya zamana a halin yanzu suna fuskantar juna shi da ita.
“Zan iya wuce wa?.”
Ayusherh ta faɗa tana ɗan kauda idonta daga gare shi ta lura kunya bai ishi wannan Guy ɗin ba, banda haka ai ba zai ke yin wannan abu har haka ba.
“Ayi min alfarma na kai Battle Angel zuwa inda take da muradi.”
Ya ƙara faɗar hakan a maimakon ya bata amsa.
Dafe goshi ta yi tana ɗan shuke baki tare da girgiza kai ta lura da gaske bashi da aikin yi ita kam tana da abin yi. Raɓa wa ta yi ta gefansa ta wuce, ta kai hannu zata buɗe motar ya ƙara. “Please!! Domin ta hakan ne kawai zan nuna Godiyata a gareki bisa ceton Rayuwata da kika yi.”
Ta sauke masa ajiyar zuciya ba tare da ta dubesa ba. Ta je key na motar a ta saman motar sannan ta je ta buɗe gidan baya na motar har zata zauna ya ce.
“Woww ai kuwa zan so na zama drivern ki kuwa.”
Fasawa ta yi, sai kawai ta buɗe gaban motar ta zauna.
Haisam ya ɓoye dariya, daman haka yake so, ƙari sawa ya yi tare da shiga motar tare da bata wuta ya tayar, ba mai um bare um uhm suka fito daga Barrack ɗin ya ɗauki titi shantal.
Ayusherh ta ɗan lumshe ido fuskarta na saitin window, yayin da shi kuwa Haisam sai murmushi yake zabgawa, yana masifar son ta Abin har mamaki yake bashi, domin wannan shi ne karo na farko da ya yi ma wata mace kalar wannan so haka, hasali ma bai taɓa wani abu wai shi dating da wata ba.
Ayusherh ta kasa kunne tana jira ya tambaya address ɗin ta, sai dai taji shiru ga mamakinta kuwa Anguwan da gidan da take zaune ya kawo ta, bata ƙara shan mamaki ba har sai da taga ya yi parking dai dai ƙofar madaidaicin flat home ɗin.
Fitowa ta yi daga motar Ba tare da ta bari ya shiga da motar ciki ba.
“Na gode.”
Ta faɗa a taƙaice tana shirin buɗe Gate ɗin ta shiga ciki taji ya ce.
“Battle Angel ba za'a yimin koda tayin coffee ba.”
Ɗan dakatawa ta yi tare da juyowa tana ɗan dubansa, sai ya langwaɓar da kai kamar maraya, hakan da ya yi kuma ba ƙaramin dariya ya so bata ba, amma ta kame tare da faɗin.
“Okay ba damuwa shigo ciki kafin kayi min kuka.”
Ta faɗa ko'a jikinta tare da shigewa ciki abin ta, Haisam ya yi murmushi mai sauti cike da nishaɗi yabi bayanta zuwa cikin gidan.
Gidan ya tsaru kuma ya haɗu matuƙa duk da kasancewarsa flat kuma ɗan dai dai sai dai ya tsaru. Cikin madaidaicin palon suka shiga, Ayusherh ta a je Jacket da scarf ɗin ta a saman Hannun sofa tana faɗin.
“Barka da zuwa fadar Captain Ayusherh.”
Haisam ya yi murmushi yana jinjina kai, ai kuwa dai gashi nan kamar ƙaramin fada duk da ɗan dai dai ne kuma ba'a cika shi da tarkace ba amma ya haɗu, ya hakaito hakan a ransa domin shi kanshi palon ya tafi da shi.
Hanyar kitchen ta nufa tana faɗin.
“Bara na haɗo ma baƙo coffee.”
Yayin da Haisam ya jinjina kai tare ɗan ƙari sawa yana duban makeken hotonta sanye da uniform na soji ita da wani mutumi da ya tabbatar Mahaifinta ne dukkansu suna murmushi a ka ɗauki hoton kuma sun yi kyau sosai, Haisam ya shagala da kallon frame ɗin yana sakin murmushi shi kaɗai sai jin muryarta ya yi tana faɗin.
“Gashi ko?.”
Ta faɗa tana miƙa masa madaidaicin cup na coffee dake fitar da daddaɗan ƙamshi da tiriri.
“Thanks Battle Angel.”
Ya faɗa tare da karɓar cup of coffee ɗin yana sakar ma ta murmushi.
Mayar da dubanta ta yi kan frame ɗin da yake kalla, ta ɗan saki murmushi tana kai bottle water da ta buɗe a baki ta ɗan sha.
“Ban ga naki coffee ɗin ba.”
Haisam ya faɗa dan ya rasa abin faɗa kuma so yake suyi fira.
Girgiza kai Ayusherh ta yi tana ɗan shuke baki, ta ce.
“Banashan coffee da duk abin da ya danganci kayan chocolate zaƙi ma ba sosai ba.”
Ai tun kafin ta dure maganar ya yi saurin dawo da cup na coffee dake hannunsa da yake yunƙurin kaiwa baki, sai ya fasa.
Ayusherh ta dubesa da ɗan mamaki tana ɗan ƙara girman Manyan idanunta a kan sa ta ce.
“Wani abun ne ya faru?.”
Haisam ya bata amsa da faɗin.
“Tun da bakyaso nima daga yau na dena sha, amma ai kina shan Black tea ba?.”
Ayusherh ta ɗan saki murmushi a karo na farko tana juya ido sai ta girgiza masa kai alamar a'a.
Haisam ya kwaɓe fuska. Hakan kuma ba ƙaramin dariya ya bata ba.
Murmushin fuskarta bai gushe ba ta ce.
“da wasa nake fa, karka damu ina shan Black tea.”
Murmushi ya yi haɗe da sauke ajiyar zuciya sannan ya a je cup of coffee ɗin a  kan desk dake wurin da suke tsaye da alama tana karatu ne ko wani aikin da shi tun da a ka a je a wurin.
“By the way dai sunana Muhammad Haisam.”
“Na sa ni ai.”
Ayusherh ta faɗa tana bin hannunsa da ya miƙo ma ta da kallo.
“Addinina bai bani damar gaisawa ko taɓa wanda ba hurrramina ba.”
Ya ɗan yi murmushi yana janye hannunsa tare da ƙara faɗin.
“Da gaske nake i really love you for the all my heart.”
Ya faɗa in serious.
“Na sa ni.”
Ta faɗa a taƙaice. Ya yi saurin dubanta, ɗa ga masa gira ta yi.
“Yeah! ba ka faɗa ba a ɗazu.”
“Hump, Battle Angel ke ɗin ta dabance.”
“Na gode.”
Ta faɗa.
Haisam ya ƙara sauke ajiyar zuciya cikin rashin abin faɗa. Ganin haka ya sa Ayusherh ta juya kamar zata koma kitchen shi kuma a dai dai lokacin ya juya zai juyo ke nan ita ma ta juyo sai suka buga karo. Baya ta yi tana ɗan shafe goshinta.
“Am sorry.”
Ya faɗa da sauri.
Shiru ta yi masa sai ma zuba masa ido da ta yi.
“Na gode da tarbata da kikayi zan tafi.”
Ya faɗa. Ayusherh da ta ƙosa ya tafin, ta rakosa har bakin Gate sannan ta ce.
“Na gode da rage hanya.”
“Karki damu ai koma mai nayi kin cancanta ko kin manta kece silar ceton Rayuwata.”
Girgiza kai ta yi. “Aikina ne shi ya sa.”

“Haka ne amma ba zan dena godiya ba.”
Jinjina kai ta yi. Har Haisam ya nufa motar da drivern sa ya ƙari so yana jiransa sai kuma ya yi saurin juyowa yana cewa.
“Ooops! Kamar nayi mantuwa fa.”
Jin abin da ya ce ne ya sa Ayusherh  faɗin.
“Okay Bara na duba.”
Sai ya yi saurin faɗin.
“Ai a tare dake nayi mantuwar.”
Ta ɗan zaro ido tana bin sa da kallon mai kake nufi?.
Haisam ya yi murmushi.
“I love you.”
Cewar sa yana zuba ma ta idanu.
Ayusherh ta ɗan shuke baki.
“Nima haka.”
Ayusherh ta ƙara zaro ido jin abin da ya ƙara faɗa.
Ya ɗan yi murmushi.
“Nasan hakan zaki faɗa amma an tsaya sai an ga sani ko?.”
Gimtse fuska ta yi tana ɗan ƙara shuke baki.
“Okay take care.”
“Oo kin amince kika ce?.”
Ayusherh ta sauke ajiyar zuciya.
“Karki damu bazan ƙosa ba kuma ba zan takuraki ba ki nutsu ki yi tunani da kyau.”
Ya faɗa tare da shiga motar nasa driver yaja, yayin da Ayusherh ta bar nata motar anan waje domin tana so zuwa anjima zata ɗan fita.
Ciki ta koma sai dai ta kasa kataɓus kalaman Haisam kawai take tunawa. “Woo wowo Ayusherh ki nutsu mana! Wai meke damun ki ne?.”
“Wani abu ne mana.”
Gefen zuciyarta ya bata amsa.
Girgiza kai ta yi tana ɗan shuke baki.
Da sauri ta ciro wayarta tare da dannawa Tata kira dan ta yi kewarsa kamar ba jiya suka rabu ba kuma ko ɗazu ma sai da suka yi waya.
  *
Washe gari Ayusherh ce ta fito daga gidanta cikin uniform nata na zuwa aiki, motarta ta ɗan sama matsala ba zata iya zuwa aiki da ita ba, shi ya sa ta fito tana duban agogon hannunta tare da fatan karta makara zuwa wurin aikin domin akwai wani taro mai muhimmanci da za'a gabatar zuwa 9am.
Sam bata lura da motar dake a fa ke ba, da shi kanshi da yake jingine da motar yana dubanta cikin sakin murmushi.
“Battle Angel!.”
Ayusherh ta ɗan tsaya cak jin sunan da aka kira da kuma muryar da taji. A hankali ta fara juyowa ta saitin wurin da ta jiyo muryar nasa.
“Shin zan iya cin alfarma na rage ma Battle Angel hanya?.”
Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi yana yi ma ta nuni da motarsa. Ajiyar zuciya ta sauke tare da gyaɗa kai, bata ce komai ba ta nufa motar tare da buɗe gidan gaba ta zauna. Haisam ya yi murmushi sannan ya zagaya ya shiga motar ya zauna. “Na gode.”
Ayusherh ta faɗa lokacin da ya fara tafiya da motar. “Ba buƙatar kiyi godiya.”
“Saboda me?.”
“Saboda ni ne silar da motar ki taƙi tashi.”
Ayusherh ji ta yi kamar ta bar motar nasa jin abin da ya faɗa domin ta fusata, sai tsintar muryarsa ta yi yana ci gaba da faɗin.
“Wannan ce kaɗai hanya da zan iya sake rage miki hanya har mu sama ƴar shaƙuwar da zamu fahimci juna amma please kiyi haƙuri in kinji ba daɗi.”
Ya ƙare maganar yana wani karyar da kai.
“Ba komai, ya wuce.”
Ayusherh ta faɗa.
Haisam ya yi murmushi cike da jin daɗi. Haka ya yita ƙoƙarin janta da fira wani ta kulasa wani kuma ta yi shiru. Daga haka ma tun daga wannan rana sai dai Haisam yazo ya ɗauke ta zuwa Barrack ɗin, tun bata saba ba har ta fara sabawa da shi kanshi, har takai ta kawo wasu lokutan yana kaita zuwa can gida idan zata je wurin su Tata. Akwai Ranar ma da sai da ya takura ta haka nan ta amince ya shiga gidan suka gaisa da su Tata da yake ma lokacin duk mutanen gidan suna nan, ai kuwa Ali da Ma'az sai murmushi suke zabgawa acewarsu ai kuwa Anty Captain ta dace da saurayin nata 101% dan kuwa sun san wanene mahaifinsa da shi kansa haka ma Yayankaka da Chanchal sai murna suke. Shi kuwa a lokcin Tata da kallon tuhuma kawai yake bin Ayusherh. Ai kuwa suna keɓeta ya tuhumeta a kan alaƙar dake tsakaninta da Haisam. Sai kawai ta ce masa Abokin aikinta ne kuma Abokinta shikenan, Tata bai ƙara ma ta zancen ba. Sai ido da ya zuba musu, to daga nan kusan duk a sati da Haisam a ke cin abinci na dare a gidan. Kuma nacin da yake ma Ayusherh ne ya sa tun bata kulasa har dai ta bada kai bori ya hau.

         ***
BAYAN WATA ƊAYA....✍️

_To! Reader's kun dai ji bayan wata ɗaya, ko mene ya guda na? Da alama fa an zo wurin domin Ayusherh za su fara soyayya da Haisam tun da an ce bayan wata ɗaya. Hummp turka-turka ke nan, me kuke tunanin zai faru? Wai ma mene abin da Yusra take bincike akai kuma ta ce ya shafi Mr President wato uncle ɗin ta bayan kuma ita ɗin ta kasance ma'aikaciyar banki ce?... Muje zuwa kawai._
Nainarh ce ƴar mutan KD na gode. 🥰🪄💝🌷
08081129487 .

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now