•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
*🔥Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 13.
Bayan ta nuna hoton dake jikin allon majigin. “Wannan sunansa Haisam kuma ɗa ne a wurin Mr President Dawud Nasamu, a daren jiya masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da shi a hanyarsa na dawowa daga Lagos zuwa Abuja a mota.”
Ta ɗan yi shiru bayan ta faɗa haka, yayin da duk suka nutsu suna sauraren ta, hankalinsu kacokan a kan bayanin da take yi. A hankali kuma ƙasa ƙasa Jasmine ta ce ma Ayusherh cikin raɗa. “Shi Mr President ɗin mijinta that's why she's so uncomfortable kuma ta damu sosai a kan lamarin.”
Ci gaba da bayani General ta yi da faɗin.
“A halin yanzu mun gano inda waɗan nan masu garkuwar suka kaisa, a halin yanzu suna a wani daji ne dake tsakanin Abuja da kuma wani ƙauye, ba tare da taɓa lokaci ba zamu shirya tawaga domin kai hari ga waɗan nan ƴan ta'adda, lastly kuyi iyakar ƙoƙarin ku wurin ganin an dawo da Haisam gida cikin ƙoshin lafiya ba tare da wani abu ya sameshi ba.”
Ta faɗa tana ƙara jajjadawa a gare su, daga haka kuma a ka shiga shirya tawaga da za su kai sumamen ga ƴan ta'addan a domin kwato Haisam, Captain Ayusherh ita ce da tawagarta za su jagoranci kai harin, cikin ƙanƙanin lokaci sun gama duk wani abu da ya dace sun shirya tsaf sannan suka shishshiga attack helicopter suna bin map har suka ƙari sa dajin da ƴan ta'addan suke, nan kuma kowannensu ya shiga gyara bindigar dake hannunsa a sa'ilin da attack helicopter ɗin nasu ya shiga dajin, yayin da Captain take duba dajin tare da nazarinsa ta hanyar amfani da abin hangen nesa. Juyawa ta yi tare da duban sauran sojojin, da hannu ta yi musu alama dai dai wurin da take zargin ƴan ta'addan sun ɓuya, hakan ya sa suka sai ta makaman su, sannan biyar daga cikinsu suka sauka daga helicoptern dake zagaye dajin, cikinsu har da Ayusherh, cikin tafiyar sanɗa da bi ta cikin ciyayi, suka fara tafiya yayin da wasun su suke duba abin hangen nesa dake jikin bindigar hannunsu.
Da Hannu ta yi musu alama da wani keɓantaccen wuri kamar gidan gona dake a dajin kuma da alama nanne ƴan ta'addan suka ɓuya, sannan ta yi musu alama da ita zata fara gaba sannan subi bayanta. Da sauri ta ɗan miƙe da ɗan gudu kuma ta ƙari sa wurin wani daga cikin ƴan ta'addan dake kewaye wurin hannunsa riƙe da wata jibgegiyar bindiga. Saitin wuyansa ta damƙa tare da murɗawa, take a wurin ya sume, bindigar hannunsa ta ɗauka tare da miƙa wa sojan dake biye da ita, sannan ta yi masa alama da ya bi wata hanyar, sannan ita ma tabi wata hanyar.
“Boss an sama matsala, sojoji sun kawo farmaki.”
Cewar wani daga cikin ƴan ta'addan da ya shiga cikin Ɗakin da shugabansu yake, ya yi maganar hankalinsa a ɗan tashe.
“What!! amma garin ya ya sojoji suka gano maɓoyarmu.”
Wanda yake tare da shugaban nasu ya faɗa yana miƙe wa tsaye daga zaunen da yake, tare da ƙari sawa wurin da ya a je bindigarsa sannan ya ɗauka.
Dirowa ta yi daga ƙaramin katangar sannan cikin azama ta yi ƙasa tare da ci gaba da tafiya hannunta riƙe da bindigarta yayin da rabin fuskarta ke rufe da hular kanta, a ka sin sauran sojojin da wasun su da wani Green ɗin abu suka shafe fuskokinsu yayin da wasunsu kuma suka rufe fuskokinsu da mask mai haɗe da hular kansu irin mai kare harsashin nan.
Da sauri ta ɓuya jikin wani ɗan corridor ganin ɗaya daga cikin ƴan ta'addan yana tunkaro wurin, har sai da ta dai dai ta ya kusan ƙari sowa inda take sannan ta fito tare da shammatarsa ta sakar masa harsashi a ƙirji, da sauri sojojin da suka biyo bayanta suka ƙari sa tare da janye sa daga wurin, sannan ita kuma ta yi gaba, Ɗakin da suke zargin nan ƴan ta'addan suke a tare da Haisam ta ƙari sa, sai dai ƙofar a garƙame take kuma irin ƙofar nan ne mai girman gaske da security na musamman muddun bata ciki a ka buɗe ba, to fa sai dai bomb ne kawai zai iya fasa ta.
Hannu ta saka a cikin aljihun dake wandonta ta wurin gwiwarta ta ciro abin fasa ƙofar tare da manna shi jikin ƙofar, juyawa ta yi tana duban sojojin dake bayanta, sannan ta fara counting from one to three, sannan bayan ta danna wani madanni dake jikin abin fashewar, tana kai three a ƙirgar abin ya fashe tare da ƙofar, da sauri ta danna kanta cikin Ɗakin, dai dai shugaban nasu yana faɗin.
“Kun manta ɗan waye muka sace ai dole sojoji su kawo farmaki sai dai sun ja zan yi abin da ban yi niyya ba...” Bai idda maganar ba suka ji ƙarar fashewar abu dai dai nan kuma ta shigo Ɗakin riƙe da bindigarta ta saitasu duk suka yi tsuru-tsuru domin duk basuyi tsammani ba kasancewar suna daga can cikin Ɗakin ne. Kuma at the same time da bomb ɗin ya fashe da ƙofar ita kuma ta shigo, so basu iya wani yunƙuri ba.
Da sauri ɗaya daga cikinsu ya saita bindigarsa a kan Haisam dake zaune saman wata chair sun ɗaɗɗaure hannunsa da ƙafafunsa a ta bayan chair ɗin, fahimtar abin da yake shirin yi ne ya sa Captain ta yi wani tsalle tare da jifa da bindigar hannunta ta ƙari sa wurin da Haisam yake saman chair ɗin a ɗaɗɗeure tare da sa ƙafa ta ture chair ɗin ya yi ƙasa, sai dai duk da haka harsashin da wannan ɗin ya riga ya saki, fiu ya wuce bayan ya gogi gwiwar Haisam a sakamakon lokacin da Captain ta ture chair ɗin da yake kai ƙasa chair ta yi, wannan ya sa harsashin ya shafi gwiwarsa sannan harsashin ya bugi jikin bangon Ɗakin.
Tim chair ɗin da Haisam yake kai ta yi ƙasa, da sauri Captain ta sa ƙafa tare da shure Bindigar dake a hannun wannan Kidnapper ɗin da yake ƙara ƙoƙarin sakin wani harsashin a saitin ta.
Ca fe Bindigar nasa da ta yi sama Captain ta yi, tare da saitawa bata jira komai ba ta sakar masa lafiyayyen harbi a gwiwa, ganin haka ya sa kidnapper ɗin da ya shigo Ɗakin a ɗazu ya sanar dasu game da sojojin, ya nufa ƙofa zai gudu, sai dai kafin ya kai ƙofar Captain ta sakar ma sa nasa harsashin a kafaɗa.
Shugaban Kidnapper's da babu bindiga a hannunsa da sauri ya fakaici idanunta tare da yin crawling ya ɗauki bindigarta da ta ƴar, sannan ya miƙe tsaye tare da saita Haisam da jikinsa gaba ɗaya ya mutu ya kasa koda kwakwaran motsi tun bayan lokacin da ya faɗi, a sakamakon gwiwarsa dake masa wata iriyar zugi na bala'i.
“Ko ki a je bindigar hannunki ko kuma na fasa kansa da alburushi.”
Cewar Shugaban kidnapper's ya faɗa haka yana ma ta nuni da Haisam dake kwance ido a lumshe, maganar da ya yi ne ya sa Haisam buɗe ido da sauri sai a lokacin ya lura da shugaban Kidnapper's da yake tsaye a kansa ya kuma nunasa da bindigar dake hannunsa.
“No! Karka harbesa faɗa min mai kakeso nayi?.”
Ta faɗa cikin sanyin muryar tanayin baya tare da yin alama da hannunta shi kuma hamagon ya ɗauka surrender ta yi. Hakan ha sa ya saki dariya yana faɗin.
“Da fari ki a je Bindigar dake hannunki sannan sai ki ɗauki wancan wayar ki kira domin a kawo Miliyan hamsin da na buƙata ko kuma yanzu na fasa kanshi.”
Ya ƙare maganar yana ma ta nuni da wata landline dake jikin side wall na Ɗakin. Sannan ya tayar da Haisam zaune, yana ƙara sai ta Bindigar a saitin kan Haisam.
Yadda ya so ta yi ta hanyar a je bindigar sannan ta fara taka wa domin ƙari sawa wurin da landline ɗin yake, lankwasa yatsarta manuniya ta yi dai dai lokacin kuma suka ji wani ƙara ta waje, da sauri kidnapper's leader ɗin ya kai dubansa ga window'n Ɗakin yayin da Ayusherh ta yi amfani da hakan ta hanyar yin tsalle ɗaya ta ƙari sa inda yake tare da kwace Bindigar ta saitashi, nan fa ya hau zazzare ido, wani sauti ta fitar daga bakinta da hakan ke nuni da tana kiran sojojin, da sauri suka shigo tare da ƙari sawa wurin kidnapper's leader ɗin, ɗaya daga cikin sojojin ya saka ma sa handcuffs, yayin da Ayusherh ta ƙari sa wurin da Haisam yake tare da kwance sa, sannan ta duba ɗaya daga cikin sojojin kana ta ce, Lieutenant Hammad ka sanar a yi preparing abin da ya kamata domin ya sama rauni a gwiwarsa duk da alburushin bai shiga ba. Jinjina kai Lieutenant ya yi sannan ya yi amfani da Communicative device dake kunnensa ya sanar da sauran sojojin dake wurin helicoptern abin da Captain ta faɗa.
Taimaka masa ta yi ya miƙe tsaye.
“Zaka iya tafiya kuwa?.”
Ta faɗa a karo na farko tana ɗa gowa ta dubi fuskarsa shi dama already itan yake duba duk da halin da yake cikin hakan bai hanasa furta. “Battle Angel ba.” a lokacin da idanunsu suka haɗu wuri guda, yadda kasan tafiyar masadar lantarki haka suka ji a tare wani abu ya fito daga idon kowannensu ya shiga na ɗan uwansa.
“Oh Bara na taimaka maka.”
Ta ƙara faɗa ganin ya buɗe baki sai dai bataji abin da ya faɗa ba.
Hannunsa ta ɗaura a kan kafaɗarta sannan ta taimaka masa suka fara taka wa suka fito daga ƙaramin gidan gonar still idanunsa a kanta, ƙari sawa da shi wurin helicoptern nasu ta yi tare da taimaka masa ya shiga ciki sannan ya hau saman madaidaicin treatment Stretcher ɗin sannan ita ma ta shiga cikin helicoptern bayan sauran sojojin sun shiga ne helicoptern ta bar wurin yayin da ɗayan helicoptern da ya zo kuma wasu sojojin ne suka shiga tare da kidnapper's ɗin da suka ji rauni. Da waɗan da basu ji ba har ma da leader nasu.
BAYAN AWA UKU.
*Aguyi-Ironsi Barracks Cantonment ¹, Asokoro, Abuja.*
“Good job, Captain aiki ya yi kyau, fatan nasara, and yanzu Haisam yana can asibiti yana samun kulawar da ta dace su kuma kidnapper's ɗin za su sama hukunci dai dai da abin da suka aikata dan wannan karon sun taɓo ɗan manya, yawwa Mr President ya ce na miƙa masa godiya zuwa gareki keda tawagarki na ceto ɗan sa da kukayi.”
General ta ƙare maganar tana miƙe wa tsaye daga kan kujerar office ɗin ta sannan ta duba Captain Ayusherh dake tsaye ta ci gaba da faɗin.
“Nima kuma a matsayina da nake tamkar mahaifiya a wurin Haisam na gode bisa ceton Rayuwarsa da kika yi.”
Ta ƙari sa maganar tana dafa kafaɗar Ayusherh.
“Ba komai Sir wannan ai shi ne aikin namu.”
Cewar Ayusherh.
“Good.” General ta faɗa.
“Permission to leave sir.”
Captain Ayusherh ta ƙara faɗa tana sara ma ta.
“Okay, You can go.”
General ta amsa ma ta fuskarta ɗauke da bayyanannen murmushi.
Fitowa daga office ɗin Ayusherh ta yi sannan ta fara tafiya domin ƙari sawa office ɗin ta, ai kuwa da shigarta taga Jasmine zaune, tana waya.
Ƙari sa shiga ciki ta yi tare da tsayawa gaban desk ɗin tana tattara wasu files. Bayan ta gama ta miƙa wa Jasmine key na office ɗin tana ma ta nuni da idan ta gama ta rufe office ɗin.
Da sauri Jasmine ta katse kiran cikin murmushi ta miƙe tsaye tare da saita tsayuwarta ta wani yi saluting Ayusherhn tana faɗin.
“Weldone Captain, you did the good job, gaba ɗaya media ta Hauka ce a kan zancen ki bisa ƙoƙari da kikayi keda tawagarki wurin ganin kun ce to ɗan president.”
Ta ƙare maganar tana sakin murmushi.
Girgiza kai Ayusherh ta yi tana dafa kafaɗarta ta ce. “Jinjinar ai har dake tun da kema kina cikin tawagar kuma kin bada naki gudunmawar da ta dace.”
“Haka ne kam sai dai duka yabon naki ne, saboda badan ke ba da wata ƙila bamu sama nasara a kan ƴan ta'addan ba, by the way naga kina miƙo min key's ba dai gida zaki koma so early haka ba?.”
Jasmine ta yi ma ta tambayar tana duban Ayusherh dake tsaye tana saurarenta.
“Kwana biyu ban leƙa gida ba, to ina so na biya naga halin da suke ciki ne.”
“Okay tohm muje na rakaki in ya so na dawo dan kin san ni a Barrack nake zaune.”
Cewar Jasmine sannan ta ƙara da faɗin.
“Wata ƙila ma a hanya na sama nishaɗi da zai fitar dani daga bad mood da wancan matar ta sakani.”
“Ookay ba damuwa. Wacece haka?.”
Ayusherh ta tambaya lokacin da suke ƙoƙarin fitowa daga office ɗin.
“Mom ɗita mana, ta nace a kan sai nayi aure a kwanan nan, sam na rasa gane kan ta.”
“Ayya, ai hakan ya kamata kiyi auren mana.”
Ayusherh ta faɗa tana ƴar dariya. “Lallai ma Captain wato har dake ko?.”
Cewar Jasmine tana ɗan kwaɓe fuska. “Ah to naga gaskiya ne.”
“Hump kedai bar gaskiyar nan Indai haka take to fa bana buƙatar ta.”
....✨✨
*Nnamdi Azikiwe International Airport*
Tsaye take jingine da motarta ƙirar Mercedes-AMG One, waya ce kare a kunnenta yayin da ta ci gaba da faɗin.
“Okay ba damuwa, yawwa Arham please ka sanarwa ABAAN Kamasho ya sameni a gidanmu domin bazata nakeso nayi masa.”
Ɗan shiru ta yi alamar tana sauraren abin da zai faɗa, sannan ta gyaɗa kai tare da katse kiran bayan sun yi sallama, dai dai kuma ta hango fitowarta, kyakkyawar budurwa ce irin First class ɗin nan tana da kyau irin sosai ɗin nan, sanye take cikin wata iriyar Fitted Gown mai launin ja da kuma adon stones, kafaɗarta kuwa tana rufe ne cikin wani knee high boots, yayin da idanunta ke maƙale da wani arnen round glass, make-up mara hayaniya ne a saman kyakkyawar fuskarta, kusan gaba ɗaya Long straight hair nata a waje yake, a domin yalolon Mayafin da ta yafa wanda da shi kwara babu, bai wani rufe kanta ba.
A hankali take taka wa kamar bata taka kasa ba, yayin da take yanje da ɗan madaidaicin suitcase nata da shima launin ja ne, kusan gaba ɗaya shigar jikinta banda gashinta da kuma baƙin Glass ɗin da ta saka kusan komai launin ja ne da shi.
Da sauri Yusra ta ƙari sa gare ta tare da yi ma ta side hug tana faɗin.
“Oyoyo sister na I missed so much, ina fata kin dawo lafiya?.”
Ta ƙare maganar bayan sun saki juna daga rungumar da ta yi ma ta.
Ya mutsa fuska budurwar ta yi tana amsa ma ta da faɗin.
“Missed You too dear, ki kaini Asibitin.”
Ajiyar zuciya Yusra ta sauke jin abin da Nusra ta faɗa, karɓar akwatin nata ta yi, sannan ta a je a back seat na motar, yayin da Nusra ta shiga gaban motar, ita kuma Yusra ta zagaya ta shiga driver seat, sannan ta ja motar suka bar wurin.
“Ki kwantar da hankalin ki, Haisam yana lafiya ba wani abu ba ne Babba ya sameshi.”
Yusra ta faɗa a yayin da take tuƙin tana ɗan kallon Nusra.
Shiru Nusra ta yi dan batajin zata iya furta komai ba tare da taga halin da Haisam yake ciki ba.
Ganin haka ya sa ita ma Yusra taja bakinta ta yi gum, suka ci gaba da tafiya.
*Nizamiye Hospital: Plot 113, Sector S. Cadastral Zone, Life Camp Abuja, Nigeria.*
“Barka Malam Haisam kana iya ganina da kyau kuwa? Ya jikin naka kuma, daure ka tashi zaune.”
Doctor ke maganar yayin da yake tsaye gaban gadon da Haisam ke kwance.
A hankali yake buɗe idanunsa da suka ɗan yi nauyi sakamakon baccin da ya yi, har ya gama ware su tar a kan fuskar Doctor, ɗaya bayan ɗaya yake duban mutanen dake a room ɗin, yana ƙoƙarin tashi zaunen a ka turó ƙofar Nusra ta shigo tare da ƙari sawa wurin sa da hanzari, gaba ɗaya mutanen room ɗin kallon mamaki suke bin ta da shi domin ba wanda ya san ta dawo Nigeria. Yusra ce ita ma ta shigo da sallama.
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
