15

6 0 0
                                        

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)

                                   https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20

        BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.

_Masoya da masu bibiyar wannan littafi na CAPTAIN AYUSHERH ina ganin saƙonnin fatan Alkhairi daga gare ku kuma ina matuƙar godiya ga ƙaunar da kuke wa CAPTAIN AYUSHERH. THANKS ALOT Dearest..👍🪄✨💞_

*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 15..

Abaan ya yi ƴar dariya at the same time yana ɓata fuska na abin da Arham ke masa da gashi.
“Ai dole na nema kuɗi muddun ina so na ci gaba da zama ɗan Nigeria domin na lura gaba kaɗan za'a koma masu kuɗin su ne sarakai talakawa kuma bayi.”
“Wato haka kake mana fata ke nan?.”
“Ah no kawai hasashe nake.”
“Okay, saƙo Yusra ta bani na faɗa maka.”
Da sauri Abaan Kamasho ya ce.
“Allah ya sa na samun kuɗi ne.”
Ya yi maganar yana washe baki.
Sai da ya sa Arham ya yi ɗan murmushi,  wato dai shi Abaan bashi da wani zance sai a kan kuɗi kuma hakan ya samo asali ne tun yana ƙaramin sa ya taso yaro ne mai zafin nema, kuma baya taɓa bari a wulaƙanta shi zai dage ya nema na kansa, kuma shi ɗin Maraya ne gaba da baya, domin a gidan marayun ya girma har ya san kansa bayan ya gama secondary ma bai ƙara shiga wata makaranta ba, acewarsa ya fiye masa ya nema kuɗi kawai, shi ya sa mutane da dama da suka sansa suke kiransa da Abaan Kamasho.
“Nima ban sa ni ba, amma ta ce ka sameta a gidansu koma mene ne kaji.”
Cewar Arham.
“To shikenan an gama babban yaya.”
Kamasho ya faɗa yana janye kansa baya, tare da ci gaba faɗin.
“woo Babban yaya shikenan kuma ka lalata min gyaran gashin yanzu dole gobe kafin naje wurin Yusra sai na biya na sake wani.”
.
Washe Gari Ayusherh ce tsaye ita da  Lieutenant Hammad a office ɗin General Lamrat Jabir Junaid a dalilin neman gaggawa da ta yi musu sakamakon wani aiki na gaggawa da ya ta so.
“Ku zauna mana.”
Cewar General tana nuna musu kujerar dake jikin desk da na ta kujerar ke fuskanta, zaman suka yi suna sauraren ta yayin da ta ci gaba da faɗin.
“Tun sati kan baya abin yake gudana to ƴan sanda sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su wurin ganin sun magance matsalar sai dai abin ya cutura shi ne dalilin da ya sa a ka ɗamka lamarin a hannun mu. Lamarin shi ne an sama rabewar kai ta wurin wasu Matasa masu banbancin ƙabila da har hakan ya zama Babban faɗa kuma har ya jawo ɗayan matashin ɗan wata ƙabilar ya kashe ɗayan ɗan wata ƙabilar daban, to yanzu shi wannan matashin zakuje ku kawo, abin ba sauƙi ne da shi ba, domin shi matashin mugun Tantiri ne ya fasa kan jami'an ƴan sanda biyu a lokacin da suka je kamosa to kubi a hankali.”
Ta ƙare maganar tana ɗan damƙe hannunta wuri guda ta ɗaura saman desk ɗin idanunta a kan su.
Ajiyar zuciya suka sauke dukkanin su sannan Ayusherh ta ce.
“To amma naji kince faɗar ya samo asali ne a kan banbancin ƙabila da suke da har hakan ya kawo rabuwar kai har ya zama silar da ɗan wata ƙabilar ya kashe Abokin rigimar nasa ɗan wata ƙabilar ba, haka ne?.”
General ta yi Nodding kai tana faɗin. “Yeah, haka ne.” Jinjina kai Ayusherh ta yi tana ɗan ɗaura hannunta a ɗaya saman desk ɗin ta ce. “To amma a kan wata ƙabila ce duk suke hakan? Ina nufin shi wanda ya yi kisan a wata ƙabila yake sannan shima wanda a ka kashen ɗan wata ƙabila ce?.”
General Lamrat ta ɗan yi shiru tana nazarin amsar da zata bawa Ayusherh, baya ta ɗan yi tare da jingina da kujerar da take kai, sannan ta ce.
“Da fari ban so na sanar daku gaskiyar lamarin ba amma ya zama dole, a zahirin gaskiya faɗar nasu ba a kan ƙabilanci ba ne sai dai ya yi kama da hakan.”
“Kamar ya ya? To amma kuma a kan mene ne?.”
Lieutenant Hammad shi ne ya yi ma ta tambayar a yanzu. Ajiyar zuciya General ta sauke kana ta amsa masa da faɗin. “A wannan zamanin rashin ilimi musamman ma na addini ya yi ƙaranci ta ko'ina da hakan shi ne ya zama mussababi ko kuma sila na faruwar wasu abubuwan to kamar hakan take a yanzu shi wannan matashi mai suna Sa'idu ya kasance a yadda bincike ya nuna mana shi ne, ba shi da wani ilimi na addini na a zo a gani shi ne silar da ya sa ya dilmiya kogin ɓata da har ya shiga cikin jerin wasu mutane da suka ware kansu sam babu Allah a zuciyarsu kuma wai a hakan su Musulmai ne a yadda bincike ya nuna hatta salloli ma ware lokacin su suke daban kuma basu taɓa yarda a faɗa musu gaskiya idan ma a ka yi ƙoƙarin hakan sai su fusata, a koda yaushe basu da abin ambata misali bisa tsautsayi wani abu ya samesu a maimakon su kira sunan Allah a'a sai dai aji suna faɗin, 'Shehu, ko kuma Shehu ka taimake mu, a haka suka ɗaura turbar Rayuwarsu kuma suke janyo mutane musamman matasa a ciki an kai ƙorafi zuwa office na ƴan sanda a kan sai dai a na cikin bacci ko kuma an daɗe da yin salar isha'i wuraren tara sai a ji su sai lokacin suke nasu sallar babu ko tsoron Allah. In taƙaice muku wannan suna da suke kira sun ɗauke shi ne tamkar shi ne Allah'n... Astagfurullah...”
General ta ƙare maganar tana jan kalmar Astagfurullah domin ita kanta abin wani banbara kwai yake ma ta.
Sannan ta ci gaba da faɗin. “To a dalilin hakan ne an sama wani da ya yi musu magana a kan wannan ɓatacciyar hanya da suka ɗauko shi ɗin Malami ne shi ne dalilin da ya sa har abin ya zama faɗa kuma daga ƙarshe Sa'idu ya kashe shi Sannan yaƙi yarda a kama sa domin a yi masa hukunci.”
General ta ƙare maganar tare da yin shiru.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now