•… 💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡
Nainarhkd3 @Wattpad.
*🔥 Perfectly Pen's (P.P✍️*
Episode 14.
“Yusra! ke nan dai kece kika ɗaukota? Domin bata faɗa wa kowa zata dawo ba. To amma me ya sa baki faɗa mana ba? Bakya tsoron abin da ya faru da Haisam ya faru ne a kan ku, tun da ba da Guard kika tafi ba, shima kanshi da yake da tarin masu tsaron ba uwar amfanin da suka yi masa ai.”
Aunty Dawha wato mahaifiyar Nusra da Yusra ita ke wannan maganar tana duban Yusra da alama ranta ya ɗan ɓaci domin tana gudun abin da ya faru da Haisam su ya same tilon ƴaƴan nata biyu rak.
Ita ko Nusra bata bi ta kanta ba, tana ji Yusra na bata haƙuri ita kam ko'a a gefen kyalenta, ƙari sawa ta yi wurin gadon da yake kwance sannan ta zauna a gefen gadon idanunta a kan sa ta fara magana cikin sanyin murya kamar ba ita ba, da alama dai abin da ya samesa ya masifar ɗa ga ma ta Hankali.
“Haisam! Kana lafiya? Gaba ɗaya duk na shiga damuwa. Ya jikin naka?.”
Ta jero masa tambayar a lokacin da Likitan ya taimaka masa ya tashi zaune, bayan ya buƙaci hakan. Bai yi magana ba sai kallon ta kawai da ya yi, sannan ya mayar da kallon sa ga Daddyn sa Mr President da kuma Mom ɗin sa. “Ina take?.” Abin da ya faɗa ke nan.
“Ita wa ke nan?.”
Suka haɗa baki wurin tambayarsa.
“Battle Angel.”
Ya faɗa yana ƙoƙarin tashi tsaye.
Gaba ɗaya kansu ya kulle da sunan da ya kira.
Wani irin bugawa ƙirjin Nusra ya yi, amma ta daure ta ce. “Wacece haka?.”
Haisam bai bata amsa ba ya duba Daddy yana faɗin.
“Daddy ba zan iya jira ba zan je na ganta.”
“But... Son kana buƙatar hutu fa, ka koma ka kwanta zan kawo maka ita ɗin ko wacece.”
Mom ɗin sa ta katsesa da faɗin hakan, duk da har zuwa yanzu bata fahimci wacca yake nufi ba.
“No, Mom ba zan iya jira ba, kuma lafiya ta qlau babu abin da ya sameni saboda ita, ta ceci Rayuwata dole naje na ganta.”
Ya yi maganar tare da zarar makullin mota dake hannun Daddy sannan ya yi waje. Gaba ɗaya suka bi bayansa har Doctor sai dai ban da Nusra da take jin nan Duniya ba'a taɓa cisgata irin haka ba, kuma wai Haisam ɗin ta ne ya yi ma ta haka, a kan wata ko wacece?.
Kasancewar da sassarfa yake tafiyar domin da gaske ba wani sauran ciwo a tare da shi dama Mom ɗin sa ce ta matsa sai an kawo sa asibiti an dubasa a lokacin da Sojojin suka dawo da shi, kasancewar ya suma tun a cikin helicopter domin Haisam yana da wata cuta da baya iya jure hawa wuri mai tsawo ko kuma hawa bene take kansa zai fara juyawa kuma hakan ya samo asali ne tun yana yaro, shi ya sa ko Jirgi a kan dole yake shiga amma ba shi da nutsuwa har sai jirgin ya yi landing.
Ƙari sawa wurin motar ya yi tare da buɗe wa ya bata key, bai saurari kiran da Mom ɗin sa ke masa ba, ya ja motar da gudu ya fi ce daga asibitin gaba ɗaya.
“Ya Rabb! Ko me ke damun Haisam, wai kuma wacece wannan Battle Angel ɗin ne da yake ta faɗa ne?.”
Mom ɗin sa ta yi maganar tana danne ɓacin ranta.
“Kar ki damu soyayya ce ba komai ba, ke dai zo muje gida da kansa zai nememu bayan ya ganta.”
Cewar Mr President yana dafa kafaɗarta, sai kawai Mom ta bisa da kallo cike da mamakin kalamansa, yayin da Aunty Dawha ta girgiza kai kurum, ita ko Yusra dama bata fito ba ta tsaya wurin Nusra ne.
Gudu yake santalawa da motar kamar titin an yi ne domin sa, cikin mintina ƙilalan ya ƙari sa Barrack ɗin. Shigowar motarsa cikin Barrack ɗin bayan security's da suka daɗe da sanin kowane ne shi, sun buɗe masa Gate, hakan ya yi dai dai da fitar motar Ayusherh.
Bai gama sai ta parking na motar yadda ya kamata ba, ya fito tare da ɗan yin tafiya kaɗan ya bi ta elevator ya ƙari sa office ɗin General. Ba tare da Kwankwasa wa ba ya shiga ciki yana faman faɗin. “Ammy, where is she?.”
General Lamrat dake tsaye gaban shelf ta juya da mamakin jin murya kamar na Haisam, sakin baki ta yi tana dubansa da mamakin ganinsa a dai dai wannan lokacin, Mutumin dake asibiti.
“Ah Haisam kai ne anan? Ƙari so ciki mana.”
Ta faɗa ganin ya tsaya tsaye tun bayan shigowarsa da abin da ya faɗa.
“No, Ammy wurin ta nazo, please kaini na ganta.”
A matsayin ta na wacca tasan shi ciki da waje ta fahimci wacca yake nufi, amma ta sha re ta nuna kamar bata gane ba ta hanyar faɗin.
“Wacece kuma haka, wai ma ba'a asibiti kake ba, garin ya ya kazo nan?.”
Hannu ya zura a aljihu yana juya kai cike da ƙosawa ya ce.
“Nifa ba abin da yake damuna, please Ammy ki kaini wurinta.”
Tsakani da Allah yake maganar yana roƙonta yadda kasan Ɗa yana neman Mahaifiyarsa.
Ajiyar zuciya General ta sauke tare da kiran sunansa ta ƙara da faɗin.
“Haisam! Ƙari so ciki please.”
Ƙari sawa cikin ya yi tare da zama a kujera yana fuskantar ta.
Cikin nutsuwa ta fara magana da faɗin.
“Wacece haka kakeson ganinta urgency faɗa min zan taimaka maka.”
Ya mutsa fuska ya ɗan yi, domin duk wannan abin da yake ma bai san sunanta ba.
“Hump Ammy na faɗa miki gaskiya? To ni ban san sunanta ba, amma ita dai wacce kuka tura ta taimake ni.”
Gyaɗa kai Ammy ta yi, ta ƙara faɗin.
“Yanzu idan na kira ta mai zaka ma ta ko kuma mai zaka bata?.”
Ya saki kyakkyawan murmushi da ya bayyana two points nasa, sai kuma ya rasa abin faɗa hakan ya sa ya damƙe Hannuwansa duka biyun wuri guda.
“Kana jina ba, ka fara tunanin abin da zaka bata ko kuma zaka faɗa ma ta sannan sai muga abin da zan iya a kan lamarin.”
General ta faɗa tana ɗan sakin murmushi ganin yadda duk ya ruɗe.
Shiru Haisam ya yi tare da nutsuwa yana tunanin abin faɗa da kuma dalilin da ya sa ma yake son ƙara Ganinta, wata zuciyar ke faɗa masa, Soyayya ce, ƙauna ce sila, sune maƙasudin da suka saka ya susuce lokaci guda a kan ta. To amma wannan abin nasa ya wuce iya soyayya kamar fa akwai wani abun daban, sai dai mene ne wannan abun?.
Shi ne tambayar da ya kasa bawa kansa amsarta. Ya sauke ajiyar zuciya tare da miƙe wa tsaye ya zura hannu a aljihu yana faɗin. “Nothing...”
“Ka tabbata?.”
General ta tambaya.
“Ooo Ammy!! Godiya kawai zan yi ma ta bisa ceton Rayuwata da ta yi.”
General ta murmusa tare da faɗin.
“Okay! Sai dai kuma an sama a ka si ta riga ta gama aikin ta na yau sai dai gobe.”
Haisam ya ɗan cije laɓɓansa domin ba haka ya so ba, sai dai ba komai ai gobe ma rana ce.
Juyawa ya yi zai fita. “Dakata mu tafi tare nima gidan na nufa.”
Cewar General tana miƙe wa tsaye ta tattara abin da zata ɗauka sannan suka fito tare, motar da ya zo da ita suka shiga, ba tare da security guards ɗin ta suka tafi ba. A hanya ma ba maganar dake fitowa daga bakin Haisam sai a kan Captain da ya raɗa ma suna zuwa Battle Angel. Ita dai General sai mamaki take yi, koda yake wata ƙila lokacin shiriyar Haisam daga duk wasu abubuwan da basu kamata ba ne ya yi, ta silar soyayya, to amma ita Captain da batasan ma yana yi ba, ta ya zai shawo kanta ke nan.
Fitowa suka yi daga motar a tare bayan Haisam ya dai dai ta parking motar a wurin adana motoci na gidan.
Da gudu Mom ɗin sa dake zaune a main Palo ta miƙe lokacin da suka shigo palon, tare da ƙari sawa garesa cikin damuwa take faɗin.
“Haisam! My son ka dawo, babu abin da ya sameka. Alhamdullilah na gode Allah.”
Ta yi maganar tana ƙoƙarin rungumo sa. Ɗan baya ya yi yana ƴar dariya ya ce.
“Mom! Am fine fa baki gani ba ne, kuma ni ba yaro ba ne ki dena damun kanki a kai na, banason wani abu ya saman min ke, by the way ni zan shiga ciki.”
Ya ƙare maganar yana nufar Staircases cikin hanzari aka sin baya da a hankali yake bin stairs ɗin idan zai haura sama ko zai sauko ƙasa, amma yau da sassarfa yake taka stairs ɗin kuma da bibbiyu, ba komai ne sila ba sai ita, tunanin ta ne ya sa bai ma san yana hakan ba.
Dawo da kallon ta a kan General da tabi Haisam da kallo tana ɗan murmushi Mom ta yi, tare da faɗin.
“Lamrat ki fita harkar ɗa na na faɗa miki idan kuma ba haka ba.”
Sai kawai taja gwada tare da kaɗa kanta ta koma ta zauna a inda suka su sameta.
Ko ta kanta General bata bi ba, ta bi ta ɗayan staircases ɗin dake gefan wanda Haisam yabi ta wuce zuwa part ɗin ta.
A palo ta zubar a tarkacen dake hannunta sannan ta ƙari Bedroom tare da zubewa saman gado tana lumshe ido. A hankali kalmar ta fito daga bakinta.
“Wacece ni.”
Ta faɗa ƙasa ƙasa cikin wata kalar murya mai cike da rauni da bata nunawa a gaban kowa. Tun shekaru sama da ashirin a kullum kwana nan duniya sai ta yi ma kanta wannan tambayar. Shekaru Ashirin da ɗauriya baya, farkawa ta yi a tsinci kanta a gadon asibiti, sai dai ta manta gaba ɗaya memory nata, ba zata iya tuna wacece ita ko kuma abin da ya faru har ta kasance a gadon asibiti ba, kawai abin da zata iya tunawa shi ne ita ɗin soja ce a wancan lokacin muƙamin ta shi ne; Major General daga haka bata iya tuna komai. Kasancewar koda mutum ya sama shafe war tunani ma'ana ya manta komai nasa, to fa fasaha ko kuma ilimin da yake da shi baya goge wa, a yadda bincike ya nuna ke nan.
Likitoci ne a wancan lokacin suka sanar da ita cewar Alhaji Dawud shi ne mijinta sai dai bata taɓa haihuwa ba.
Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe da kanta da take ji kamar zai rabe gida biyu saboda ta kurawa kanta da ta yi da tunani....
*No. 20, Kubuwa Road, Gwagwalada Abuja.*
“Tata!”
Ayusherh ta faɗa lokacin da suka fito daga motarta bayan ta faka motar a tsakiyar compound na gidan kasancewar ba daɗewa zatayi ba.
Da sauri ta ƙari sa wurin Tata dake tsaye yana bawa flowers ruwa.
Murmushi ne ɗauke saman fuskar Tata a lokacin da Ayusherh ta ƙari so wurin da yake tsaye.
“Tata nace ka dena wahalar da kanka wurin bawa flowers ruwa mene ne amfanin jibga-jibgan samarin da muke da su a gidan muddun za'a ce kaine zakake bawa flowers ruwa?, kuma ma wai ina security guard ɗin da na a je muku ne a gidan.”
Ayusherh ta ƙare maganar tana ɗan ɓata fuska tare da karɓar abin bawa flowers ruwan dake a hannun Tatan tana faɗin. “Kawo na tayaka.”
Ta faɗa tana karɓa tare da ci gaba da bawa flowers ɗin ruwa, yayin da Tata ya zuba ma ta ido yana ɗan murmushi. Komai nata sak na mahaifiyarta, sam Mahaifiyarta bata taɓa yarda taga ma'aikatan ta suna wahala.
“Tata kana jina kuwa?.”
Ayusherh ta ƙara faɗa ganin kamar hankalinsa baya a tare da ita.
“Shalelen Tata ya aikin dan na san kuna fama, magana kike a kan sojan da kika a je domin yake tsaron gida ko, ai kuwa Ali da Ma'az sun ɗauke sa sun tafi kasuwa, saboda neman suna.”
Dariya Ayusherh ta yi tana ɗan girgiza kai ta ce.
“Lallai ma Ali na lura yaron nan zai yi kauɗi.”
Tata ya yi dariya kurum.
“Oh Tata ga Jasmine fa Abokiyar aikina a soji.”
Ayusherh ta faɗa tana nuna Jasmine dake tsaye gefe ta ɗan basu tazara.
Kallon Jasmine Tata ya yi yana ɗan murmushi ya ce.
“Sannunki Soja fatan kina kular min da Captain ɗin yadda ya kamata.”
Jasmine ta yi dariya tana amsa masa da faɗin.
“Ai Yallaɓai Captain ɗin mu ta daban ce domin ita ke kula damu ba mu ke kula da ita ba.”
Ɗan shiru Tata ya yi shi fa sai yanzu yake ɗan fargaba na abin da zai biyo baya da shigar Ayusherh Soja, gata sak mahaifiyarta a lokacin da take da shekarunta.
“Ki kirani da Tata kamar Captain domin kema kin zama ƴar gida.”
Cewar Tata yana duban Jasmine.
“Woww Thank you Tata I really appreciate.”
Jasmine ta faɗa cike da farin ciki tana ƙari sawa inda suke tsaye.
“Naji gidan shiru da alama ba kowa ke nan?.”
Ayusherh ta faɗa.
“E to Kakarku ce kawai a ciki kinsan halin ta batason fitowa waje tana can duƙunƙune a ɗaki. Su kuma Yayankaka da Chanchal sun fita wai salon.”
Tata ya bata amsa. Yana girgiza kai. Ayusherh ta ɗan yi murmushi yana mamakin kakartasu ta ce.
“Lallai kam Bara to mu shiga ciki wurin mai tsoron mutuwa.”
“Ao har dake ko?.”
Tata ya faɗa yana ɗan ɓata fuska.
“Oh sorry Tata amma Yâ tâ ɗin ce abin nata ba dama.”
Ayusherh ta faɗa tana ɓoye dariya.
Ita ko Jasmine cike da burgewa take duban ƴa da uban, ta lura akwai shaƙuwa da ƙauna mai tsanani, tsakanin su. Girgiza kai ta yi tana tunanin tana Mahaifin da bata san ma Kalarsa ba. Abin da ta sani shi ne ta taso tare da mahaifiyarta dake auren wani mutum daban wanda ba shi ne ya haife ta ba.
*National Muslim Orphanage, Plot 135, Cadastral Zone B02, Wuse II, Abuja.*
“Abaan!.”
Arham ya kwala ma matashin da ba zai haure shekaru goma sha tara ba, dake tsaye yana duban yara maza na gidan marayun da suke gudanar da wasan ƙwallon ƙafan cike da kwarewa.
Juyowa matashin ya yi yana duban Arham da ya ƙari so wurin.
“Laa Babban yaya kai ne ta samu ne a ke nema na ko wani abun zan yi a bani Kamasho?.”
Ya faɗa yana ƴar dariya.
Arham ya ce.
“Kai kam dole ma jama'a su saka maka suna Kamasho wannan son kuɗi haka kamar ɗan siyasa.”
Arham ya ƙare maganar yana baza sumar kan Abaan dake barbaje mai kyau ga ɗan tsayi, dama ya saba masa haka duk in zasu haɗu sai ya yi ta baza masa gashi, acewar Abaan kuma ɓata masa gyaran gashi Arham ɗin yake.
YOU ARE READING
CAPTAIN AYUSHERH!
Romance# Hatred, #Envy, #Grudge, # Blackmoney Against The Perfect Exceptional Love!! ......!! ** Rayuwa Cike Da Take Da K'alubale Mabanbanta Da Kuma Mutane Masu Banbanci D'abi'a Da Halaye. Akwai Na Kirki Haka Za Akwai Na Banza Da Sune Suka Fi Yawa A Wanna...
