CAPTAIN AYUSHERH..5

4 1 0
                                    

•…  💕 *CAPTAIN AYUSHERH*🥷 *
                                       🍂🎀
(_The ShieldMaiden._)
                                  
        https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20

BY - Nainarh KD.... 𝒩𝓀𝒹'𝓈❦♡

Don't Forget To Follow My Both Accounts;
Nainarhkd3 @Wattpad.
Nkds @Arewabooks.
..

Episode 5.
_Note: Ku gane wani abu. Ba waɗan da suka kashe mahaifiyar Ayusherh ba ne suka dawo ƙauyen domin kashe Ayusherh. A'a. Su waɗan nan wasu ne daban ƴan ta'addan da suka kawo farmakin._

.
Cikin dauriya Ayusherh ta ce. “Ba komai Tata, domin ka bani hoton da zan iya ceton Rayuwata da kaina. Duk da ƙananun shekaruna.”
Ta kai maganar tana jijjiga kai. Ali ne ya dubeta a ɗan firgice domin baya ma a hayyacinsa sam, ya ce. “Mamman! Ina Mamman yake?.”
Tambayar nasa da saida tasa zuciyar Ayusherh harbawa da sauri, ta kasa magana, har sai da ya maimaita tambayar, da kyar ta sama zarafin faɗin.
“Sun kashesa, waɗan can azzaluman ƴan ta'addan sun kashe mana Mamman ɗin mu, ni a ka zo harba amma ya kareni harbin ya samesa a ƙirji, sanadin haka ya faɗa cikin teku ya mutu, ina ji ina gani na kasa ceton Rayuwarsa..” Ta ƙare maganar tana sakin wani kuka da bata sama damar yi ba sai yanzu. Da sauri Ali yaron da bai haure shekaru bakwai ba, domin ƴan biyu ne shi da Yayankaka, ya dafe kafaɗar Yayartasu Ayusherh shima hawaye yake yi yana tuna Mamman.
“Shikenan rayuwarmu ta rushe sun kashe mana mutane da yawa yayin da wasu suka gudu domin ceton Rayuwarsu, a halin yanzu kam bamu da wani madogara ko kuma wurin zuwa dan nasan kafin gari ya waye sai sun lalubo inda muke, muma su kashe mu ko kuma su tafi da mu can wata ƙasar su siyar matsayin bayi.” Yâ tâ, kakarsu ita ce take wannan maganar yayin da ta ɗaura hannu a ka, abin ka da tsufa ga kuma tashin hankali da ta tsinci kanta ciki rana tsaka.
Duk shiru suka yi suna sauraren ta ba tare da sun iya cewa komai ba, sai ma Tata ya ɗan nisa kana ya ce.
“Zaman mu anan ba tsaro domin waɗan nan azzaluman zasu iya lalubomu ko su kashe mun ko kuma su siyar damu. Kamar yadda Yâ tâ ta faɗa.”
Ya yi maganar yana tunanin abin yi, domin ba zai yiwu su ci gaba da zama a wurin na tsawon lokaci ba, dan ba tsaro.
“Wannann ƙauyen shi ne garin mu anan muka taso bamu saba da kowa ba bayan mutanen ƙauyen, kuma a halin yanzu bamu da wani wurin zuwa.”
Cewar Ayusherh.
Girgiza kai Tata ya yi. Kana ya ce.
“Tabbas akwai, ina nufin muna da wurin zuwa.”
“Ina ne?.”
Suka yi masa tambayar a tare.
Tata ya jijjiga kai ba tare da ya ce komai ba, yana tabbatar da wurin da ya Kamata suje ɗin nan ne kawai mafita a gare su, kuma zai yi amfani da wannan lamarin da ya faru wurin cusa muradin zama nagartacciya jami'ar soja a zuciyar Ayusherh ko dan ta kare ƙasarta da al'ummar ta daga farmakin ƴan ta'adda.
“A halin yanzu ba zamu iya wani tafiya ba, mu bari sai gobe sai mu kama hanya domin tafiya ce miƙaƙiya zamuyi.”
Tata ya ƙara faɗa.
“Ƙasar zamu bari.”
Ali ya tambaya.
Yayin da Yâ tâ ta ce.
“Ina ne inda zamuje ɗin.”
Ayusherh kuwa shiru kawai ta yi ba tare da ta iya furta komai ba.
“Nigeria zamu tafi. Mu fara wata sabuwar Rayuwar a can?.”
Tata ya basu amsa.
Lumshe ido Ayusherh ta yi, haka kawai batasan dalilin ba, amma taji sauyin bugun zuciyarta ya canza lokacin da Tata ya ambaci ƙasar da za su koma.
Ba wanda ya ƙara magana a cikin su, kowa dai da abin da yake saƙawa a ransa, shi kuwa Tata a nasa ɓangaren tunanin can baya yake yi, abin da ya faru bayan barinsa ƙauyen su. Ya sha matuƙar wahala sosai, yasha gwagwarmaya ya tsinci kansa a wuri wuri cikin mutane kala kala daban daban masu banbancin ɗabi'a, al'ada da kuma addini har Allah ya nufesa da sauka a ƙasar Nigeria ƙasar da rayuwarsa gaba ɗaya ta sauya a ciki domin sanadin zuwansa ƙasar ne ya fita daga duhun jahilci ya karɓa addini na Muslunci kuma cikin yardar Allah a lokaci ƙanƙani ya san abubuwa da dama da suka shafi addinin, kwarai sai a lokacin ya san cewar ya shiga addini na gaskiya, Jakadi ya matuƙar ƙoƙari a wancan lokaci wurin ganin ya sama ilmin addini dai dai gwargwado kuma lamarin kam sai godiya, ana a haka ne Jakadi yana ci gaba da gudanar da Rayuwa duk ta yadda tazo masa a ƙasar Nigeria, kuma bai taɓa tunanin ya yi aure ba domin a lokacin sam Aure baya gabansa yafi mayar da hankali ne wurin neman ilimi da kuma sana'a domin tsira da mutunci, ana a haka ne wata rana Ubangiji ya nufa ya sama aiki a gidan wani hamshaƙin mai kuɗi. Ba da ɓata lokaci ba kuma ya fara aikin a gidan,  kuma ba laifi yana samu sosai kuma akwai fahimtar juna da girmama juna tsakaninsa da Matar gidan da ta kasance soja, za'a iya cewa yana zaune ƙalau da kowa a gidan amma ban da mace ɗaya wato Ƙanwar Matar gidan da ta kasance bata da abin wulaƙanta wa sai talaka wanda ba shi da komai, kuma yayar nata tana matuƙar ƙoƙari wurin ganin ta dena wannan ɗabi'ar amma abu ya cutura.
BAYAN WANI LOKACI! A wata safiya ce kuma lokacin Jakadi ya gama yanke shawarar komawa gida can Asalinsa wurin Ahalinsa, domin bai manta da su ba. Ya je ya sama  Matar gidan da suke kira da General dama haka muƙamin ta yake a soji, ya je ne domin ya yi ma ta magana a kan zai koma ƙasar sa domin duba Ahalinsa, sai dai da yaje ya tarar da saɓani ya shiga tsakanin yaya da Ƙanwar da har ta kai su ga cacar baki, kuma abin da ya gani da kuma maganganun da yaji Ƙanwar na faɗa ma yayartata abin ya matuƙar gigitasa. Sai dai da yake lamarin bai shafe sa ba, shi ya sa bai shiga zancen ba, iya ka dai ya nema izinin tafiya a wurin Madam kuma ta yarje masa har kuɗaɗe masu kauri ta basa a cewarta ya yi kuɗin mota, ai kuwa a ranar ya fara shiri, washe gari kuma ya musu sallama da niyyar tafiya, wuraren yammaci. A lokacin ba zai manta ba har General take zolayarsa da faɗin. _“Gashi  kuma zai tafi ba tare da ta haihu ba. Balle yaga wani irin ƙani ɗan ta zai sama mace ko Namiji.”_ Domin a lokacin tana da ɗa ƙarami sannan ba shi da wata magana sai a kan kalar ƙani ko Ƙanwar da Mommynsa zata haifa masa. Shi kuma Jakadi a lokacin sai ya yi ta biyewa yaron.
A lokacin da ta faɗa haka, murmushi kawai Jakadi ya yi sannan ya ce ma ta. Ai ba daɗe wa zai yi ba zai dawo. Maganar su ke nan ta ƙarshe, kafin ya musu sallama da niyyar komawa ƙasarsa Cameroon.
A wancan lokaci da yammaci ya kama hanya kuma sai an yi tafiya mai nisa zai isa wurin da zai shiga mota. Hakan ya sa tafiyar tasa ya kai sa har dare ba tare da ya ƙari sa wurin shiga mota ba. Hakan ya sa shi yanke shawarar samun wuri ya kwana kawai in ya so da sassafiya ya ci gaba da tafiya.
Ya ɗan shiga cikin daji a ta wurin da ya yanke shawarar kwana. Hakan ya sa shi ci gaba da tafiya a daren domin samun wurin kwana.
To a wannan dare komai ya wakana. Tun daga kan haɗuwa da uwar ɗakinsa wato General da ya yi da mutane da ke bin ta domin su kasheta, har zuwa taimaka ma ta da ya yi da haihuwa da ta yi, washe gari kuma ya samu ya kai ta ƙauyen dake kusa da dajin, da biyo bayansu da waɗan nan mutane dake bin ta suka yi har buɗe wa ƙauyen wuta da suka yi da hakan ya yi silar rayuwarta yayin da shi kuma ya sha da kyar da kuma wahalhalu da ya sha kafin ya samu ya iya, isa ƙasarsu zuwa ƙauyensu dake dab da border dake tsakanin Nigeria da Cameroon. Komai ya faru ne cikin ƙanƙanin lokaci. Kuma ba tare da tsammani ba.
WANNAN KE NAN.
Dai dai nan kuma Tata ya farka a gigice daga baccin da ya ɗauke sa, har ya yi wani mummunar mafarki, Addu'o'i kawai yake jerowa. A lokacin ma gari ya ɗan waye haske ya karaɗe ko'ina.
Ya kai dubansa ga Ahalin nasa da suka yi masa saura. Ali ne da Yayankaka ƙanƙame da Kakarsu Yâ tâ, suna kwasar baccin wahala. Ɗan kauda idanunsa ya yi domin ganin ta inda Ayusherh take sai dai sama ko ƙasa bai ga alamarta ba. Hakan kuma ba ƙaramin ɗa ga masa hankali ya yi ba, da sauri ya yi ƙoƙarin miƙe wa tsaye yana kwala kiran sunanta hankalin sa a ɗan tashe, sai dai ya kasa miƙe wan sakamakon ƙafarsa wurin da a ka harba ta yi tsami, dan ma a jiya da daren kafin su yi bacci Ayusherh ta matsa har sai da ya cire harsashin da kansa domin cewa ta yi ita zata cire masa, hakan ya sa cikin dabara ya cire amma ya sha matuƙar azaba ba kaɗan ba.
Da sauri Ayusherh da take ɗan kewaye wurin domin ta ri ga kowa tashi, ƙari sowa wurin ta yi tana kiran sunansa da tambayar abin da ke faruwa a ɗan ruɗe. Zaro ido ta yi ganin gwiwar nasa yana fitar da jini, da sauƙi ta tsuguna a gabansa tare da kama rigar jikinta ta yaga, kana ta shiga ɗaure masa wurin da kyallen da ta yaga tana faɗin.
“Sannu Tata.”
Bai amsa ma ta ba, sai zuba ma ta ido da ya yi yana dubanta. Allah ya sa ni yana matuƙar son ta fiye da yaran da ya haifa a cikinsa kuma yana ma ta fatan nasara a Rayuwa, kuma zai dage da ƙarfinsa ya tsaya ma ta wurin ganin ta kai babban matsayi a rayuwa, domin ta wannan hanyar ne kawai zai biya iyayenta Alkhairai da suka yi masa a rayuwa.
“Na hango alamun ƙauye anan kusa, sai dai kamar ruga ne, ku daure mu ƙari sa domin su taimaka mana muyi jinyar ciwon Tata a can, zuwa muga abin da hali ya yi.”
Cewar Ayusherh a lokacin da ta gama ɗaure masa ciwon, ta yi maganar tana duban ƙannin nata da suka tashi.
Washe baki Ali ya yi ya ce.
“Da gaske.”
Jinjina masa kai ta yi tana duban Tata kana ta ce.
“Tata! Ai hakan ya yi ko?.”
Murmushi ya ɗan ma ta ya ce.
“E .”
Gefe guda kuwa yana kallon fuskarta ne da ta ɗauko sak kamannin Mahaifiyarta babu abin da ta rage sai kalar fata da ta ɗauka irin na mahaifin ta da ya kasance ruwa biyu wato Hausa Fulani, yayin da mahaifiyarta ta kasance asalin cikakkiyar shuwa Arab ce.

“Tata! Kanajina kuwa? an ya zaka iya tafiyar ma kuwa?.” ko dai na ɗauke ka?.”
Ayusherh ta ƙara yi masa tambayar in serious tana dubansa.
Ba Tata kaɗai ba hatta Yâ tâ da Ali har da Yayankaka maganar da Ayusherh ta yi ta matuƙar basu dariya.
“Wai wa? Tata ɗin namu zaki ɗauka?.”
Cewar Ali.
Ayusherh ta ɗan dubesa cikin rashin fahimta ta ce.
“E mana ko kana kokwanto ne?.”
Gimtse dariya ya yi yana ɗa ga hannu ya ce.
“A'a! Ni ban ce ba.”
Ayusherh ta ja gwafa, dan ita bataga aibun abin da ta faɗa ba sam.
Tata ya ɗan dara yana faɗin. “Na hutaceki da yardar Allah ma zan iya taka wa.”
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙe wa tsaye.
Ayusherh ta rungume hannu a ƙirji kana ta ce. “To gwada tafiyar mu gani. Amma ni...”
Ta kasa ƙari sawa ganin Tata ya yi baya zai faɗi. Da sauri ta taro sa tana faɗin.
“Ni dama na sa ni ba zaka iya ba, kawai Tata ka bari na goya ka ai zan iya.”
Shi dai Tata bai ce komai ba. Ganin haka ya sa Ayusherh fara kici kici ita a dole goya sa zatayi, ta wani tsaya a gabansa tare da durƙusa wa tana faɗin.
“Hau muje Tata.”
Tata bai hau ba, dan ya san ba zata iya ba.
“Tata ka taimaka ka hau, ko dan mu ƙure mai taurin kai da kafiya.”
Yâ tâ ce ta yi maganar a yanzu.
“E Tata ka hau mu gani.”
Yanzu kuma Ali da Yayankaka ne suka haɗa baki wurin faɗa.
Girgiza kai kurum Tata ya yi dan shi ya sani Ayusherh ba zata iya ba! Ina ai da sauran ta, ƙarfinta bai kai nan ba....FOLLOW MY ACCOUNT NKDS @ AREWABOOKS APP.

CAPTAIN AYUSHERH!Where stories live. Discover now