👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*PRINCE SADIQ*
👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*Na Billy Ladan*
*6-7*
_wannan shafin nakune *Hausa Novel Lovers Group*, a gaskia ba group da nake jin dadin zama dasu kamar wanga group, kuna sani nishadi sosai musamman *Hauwa DY*, *Ashwal* da *Khairateena*, ina sonku sosai sosai,Allah ya barmu tare ya kuma kara dankon zumunci_
*Ana Mugun Tare*🤝
Tunda abbanta ya koma take kulle kanta a daki, ba abunda ke fita da ita sai cin abinci. Ba yanda Ma da Nanna basuyi ba amma sam taki saukowa dole suka hakura suka barta.
Tana zaune a daki tana karanta daya daga cikin novel da abbanta ya kawo mata Ma ta turo kofar dakinta ta shigo, zama tayi a bakin gadon tareda rufe takaddar da Ummul Khairi ke karantawa tareda fadin "Khairatee ki fito kici abinci sai in aikeki gidansu Shamawilu"
"Toh Ma" kawai tace sannan ta tashi ta canza kayarta tareda rataya gyalenta a gefen kafadarta ta bi bayan Ma. Tana gama cin abincin ta dauki plates in ta kai kicin ta wankesu sannan ta fito ta daure kanta ta karasa gun Ma dan karban sakon,kallonda Ma ke mata ya sata bin jikinta da kallo,dan turo baki tayi sanin cewa Ma maganar kayan jikinta zatayi, tabe baki Ma tayi tareda cewa "jeki ba sai kin turo mun baki ba nima na gaji da miki magana akan wannan shigar taki, yarinya Allah yayiki mace amma ke ki ce dole sai kin maida kanki namiji" ganin inta cigaba bata bakinta kawai zatayi ya sa ta mika mata sakon tareda cewa "karki jima"
Khairatee na fita ta dauko gorarta ta fice tana yar wakenta. Wasu samari biyu dake zaune suna hangota dayan yace "gafa can mata maza" sannan suka tsuntsire da dariya, kallon gefensu Khairatee tayi taga sun sake kwashewa da daria, hawaye ne ta ji yana kokarin zubo mata tayi sauri ta wucesu.
Tafia kadan ne tsakanin gidansu da na shamawilun, kai tsaye ta kutsa kai ta shige, ta budi baki zatayi sallama taji kamar ana ambatarta hakan ya sa ta ja bakinta tayi shiru tareda rakubewa dan jin hirar da Shamawilu da mahaifiyar tasa ke yi, muryar innar shamawilu ta fara jiyowa tace "yanxu Shamawilu ka rasa wanda zaka kwallafa ranka sai wancan kwailar, yarinya sai bakin muni da yin abu kamar maza, ni wallahi tsabar muninta ko hada hanya banso inyi da ita, na tabbata muninta shi ya jefa mu cikin wannan bala'i da muke ciki a kauyen nan tamu, yarinyar da ko uban da ya haifeta ba sonta yake ba ai kasan wannan annobace" daria Shamawilun yayi sannan yace "toh ai Inna baki sani ba, nifa ba wai wani sonta nake ba kudin ubanta kawai nakeso, na tabbata in na rabasa da ita ba karamin alheri zan samu wajensa ba"
Hawayen da Khairatee ke dannewa ne suka fara zarya a fuskarta, kalamansa ba karamin sosa mata rai yayi ba duk da itama ba wai sonsa take ba, pasa aikan tayi ta fice da gudunta ta bar gidan, bakin wani bishiya ta zauna ta hada kai da gwiwa ta hau rusa kuka, tausayin kanta ne ya mamaye zuciyarta, ta rasa gane irin tsanar da ake mata a kauyen, ko da yake bata ga laifinsu ba tunda uban da ya haifeta ma ba sonta yake ba, sai da ta sha kukarta mai isarta ta tashi ta kade kayanta ta nufi gida, koda ta isa gida ledar ta aje gaban Ma ta wuce dakinta ta kulle kanta a ciki.
Cike da mamaki Nanna da Ma suka bita da kallo, duba ledar Nanna tayi taga abunda ta bata ta sake dawowa da shi, tashi tayi ta bi bayanta a zuciyarta tana tunanin koh me ya hanata kai sakon.
Sheshekar kukarta da ta jiyo tun daga bakin kofar ya sata juyowa ta koma falo ta zauna dan bata son abunda zai sake tada hankalin tilon yar tata
Kallonta Nanna tayi tareda cewa "lafia dai ko" ajiyar zucia tayi sannan tace "Nanna kuka take kuma bazai wuci maganganun mutane bane ya sata kukan nan, na sha gaya mata ta aje wannan shiga ta maza da take amma sam bata ji, toh ya zanyi Nanna, kauyen nan baka yi bama ba a barka ba ina kuma ga ka basu abun magana
Tashi Nanna tayi ta nufi dakin jikartata, a hankali ta turo kofar dakin ta hango Khairatee tana rakube kan gadonta ta hada kai da gwiwa tanata sharban kuka, karasawa tayi ta zauna a gefenta tareda jawota jikinta ta shiga rarrashinta, cikin kuka khairatee ta dago ta dubi Nanna tace "Nanna meh aibuna, meh na tsarewa kowa da aka bi aka tsaneni, shin laifina ne da Allah ya yini baka, ko son kai nane da na fito mummuna, shin dagaske ni annobace a wannan kauyen tamu, is dt y evryyone hates me" ta karashe tana kuka mai cin rai
Jijjigata Nanna ta cigaba dayi sannan ta dago tace "koh daya khairatee, bakida laifin komai kuma ke ba annoba bace, ke Rahamace Khairatee kuma wataran zaki fahimci hakan kuma yan wannan kauyen ma zasu gane cewa ke Rahama ce a garemu baki daya, ki daina barin kalaman mutane yana shiga kanki har yayi tasiri a xuciyarki sannan kuma ki daina nunawa kamar maganganunsu na damunki dan hakan shi zai basu damar cigaba da musguna miki, sannan ina so ki sani ke ba mummuna bace kina da kyau kyawun da ba kowa Allah ya bawa idon gani ba, kin tuna hirar mu na kwanakin baya da kike cewa wani pirins ne ko menene zai zo" dariane ya kufcewa Khairatee jin yanda Nanna ke kiran Prince, sai da ta yi mai isarta sannan tace "Nanna Prince ake cewa" tabe baki Nanna tayi tareda cewa "koma menene, toh nima a jikina naji Allah zai kawo miki mai share miki hawayenki, wanda zai so ki so na tsakani da Allah ba dan wani abu naki ba, ke dai ki dage da addu'a kuma nima xan tayaki" Ma da ke tsaye bakin kofar dakin ne ta share guntun hawayenta tareda shigowa itama ta kwantar mata da hankali, ganin bawanda ya tambayeta takamamman abunda ya faru ya sata yin shiru amma a zuciyarta ta gama yankewa akan cewa ko sama zata hade baxata auri shamawilu ba.
YOU ARE READING
Prince Sadiq
FanficUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...
