18

3.8K 161 15
                                    

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*41-42*

_Dis page is dedicated to SaadatuSaee, tnx for ur comments n d name match *SadiKhair*_😘

Maido hankalinsu sukayi zuwa kan mai martaba, cikin sauri Hajja Zinatu ta karasa zuwa wajensa yayinda Sadiq ya kasa motsi, ya ma rasa meh zaiyi, yayi murnan farfadowan da yayi sai dai baiyi a lokacin da ya dace ba, cike da kulawa Hajja Zinatu tace "Alhamdulillah ranka shi dade bara ayi maza a kira mal Aminu" kallon Sadiq tayi sannan ta mai umarnin zuwa kirawo Mal Aminu, cikin sanyin jiki ya tashi ya fice, ba a jima ba ya dawo shida Mal Aminu, da murnansa ya karasa ga mai martaba yana mai sannu sannan ya shiga dubashi, ajiyar zucia yayi tareda cewa "Alhamdulillah ranka shi dade tunda an samu ka farfado, yanxu za a barka ka huta zuwa gobe sai mu je can asibiti a sake dubaka" godia mai martaba yayi mishi, hada kayansa yayi ya tashi zai fice mai martaba ya dakatar da shi, "Mal Aminu baka fada mun abunda ya jefani wannan halin ba" murmushi ya mai tareda cewa "ka dan huta mai martaba in yaso daga baya mayi maganar" murmushin karfin hali mai martaba yayi tareda cewa "ba sai ka mun boye boye ba Mal Aminu, tun kan inci tuffan nan jikina ya bani amma kawai Allah ne yayi zanci, kuma ba yau aka fara farautan rayuwata ba, kawai ina shirune dan kar in tayarwa da iyalina hankulansu, amma koma wanene ina dab da kamosa insha Allah, sannan ban son zancen nan ya fita ko yayi tsanani, a ma manta shi tamkar bai faru ba" shiru sukayi suna mai jinjina kalaman mai martaba yayinda kowa ke sake sake a ransa. Mal Aminu ne ya musu sallama ya fice, Sadiq da tun shigowarsa ya kasa dago kansa sabida gudun kar mai martaba ya sake tada tambayar, ji yayi mai martaba yayi gyaran murya tareda cewa "wa zai mun bayanin abunda naji dazun? Hajja Zinatu ce ta budi baki zatayi magana amma ganin ya dakatar da ita ya sata jan bakinta tayi shiru, "barshi ya fadamun da bakinsa" cikin sanyin jiki Sadiq ya fara magana "Allah huci zuciyarka ranka shi dade, batun auren da kaji yazo ne da kaddara, banyi dan bata muku ba" tsaresa da ido mai martaba yayi sannan yace "ban gane kaddara ba, dole aka maka koh yaya? Ajiyar zucia Sadiq yayi sannan ya kwashi komai ya fada mai "ai ga irinta nan" cewar mai martaba "garin son nuna mana bamu isa da kai ba kaje ka hadu da *AUREN KADDARA*, kuma da yake baka daukemu bakin komai ba da ka dawo ka kasa fada mana koh, ko dai ummartaka ta sani ne? Kallon ummansa yayi ta watso mai kallon "in ka kasa da ni zaka gane ne" dauke kansa yayi daga gareta yace "ayi hakuri ranka shi dade gudun bacin ranku ya sa na kaita wani wajen har zuwa lokacin da zan iya tunkararku" shiru mai martaba yayi na 'yan wasu dakikai sannan yace "gaskia Sadiq am very disappointed in u, in nace baka batamun ba nayi karya, bazance ka saketa ba ko dan yanda ka bani labarinta, babban kuskurenka shine rashin sanar da ni dakayi tun farko da komai zai zo da sauki, ni zaka maida karamin mutum yanxu tunda da aurenka har ka bari na aura ma yar aminina batareda an san kanada wani auren ba,yanxu ya kake son na tunkari uban Farhana da wannan batu" sosai jikinsa yayi sanyi amma dia is notin he can do, hakurin nan dai shi yayi ta bawa mai martaba, yama yi mamakin yanda mai martaba bai dau abun da zafi sosai ba, shirune ya biyo baya na dan wani lokaci sannan mai martaba ya sallamesa.

Yana fita side in ummansa yayi can ya tadda su Khairatee suna zaune da flask na abinci a gefensu
Kujerar da ke kallon na Khairatee ya zauna, kallonsa Hajjo tayi tareda cewa "ya jikin mai martaban? Ba tareda ya kalleta ba yace "ai ya ma farfado" wani irin kallo ta mai tareda tashi tana cewa "amma kai wani irine ni Ababakari, yanxu da ban tambaya ba da bazaka fadi ba kenan" tsaki tayi tareda ficewa, tabe baki yayi tareda gyara zamansa, dagowa yayi ya kalli inda Khairatew ke zaune yaga shi take kallo, suna hada ido ta dauke ta kalli coolern abincin sannan ta sake kallonsa, take ya gane abunda take nufi, da kai ya mata alaman ta zubo ta kawo mai, kallon Farhana tayi da ta dage taketa typing a wayanta cikin yanayi na bacin rai sannan ta dauke kanta daga kansu baki daya, gyaran murya Sadiq yayi yace "wato ke haryanxu bakiyi hankali bako, yaushe zaki koyi kula da mijine, koh komai sai an fada miki ne,toh zuba mun abinci? Hadimai ta shiga kira wanda ya sashi daka mata tsawa "in dai su zasu zuba ki barshi kawai asararriya, ni ban ma ga amfaninki ba wlh" tsaki tayi tareda cewa "wannan kuma kai ta shafa, koh gida abincin da zanci kawomun ake, toh meh ma amfanin hadiman ba aikinsu kenan ba, in su bazasu yi ba ai ga karuwarka can ta zubama" ganin yayo kanta ya sata barin falon a guje, juyowa yayi yaga Khairatee na sharar kwalla, ji yayi kaman ya bi Farhana yaje ya lakada mata na jaki amma he wil leave dat for later, gani yayi ta karasa gun cooler ta ja plate ta zuba mai abincin sannan taje ta aje kan stool da ke gaban kujerar da yake sannan ta koma ta zauna kamar ba abunda ke damunta, wayarta ta ciro ta kira Ma tareda shaida mata sun iso, sun dan jima suna waya sannan ta aje. Sadiq baiyi yunkurin mata magana ba dan gani yake kar yayi ta kuma kukan. Suna zaune a haka Zali ta shigo, kallo daya ta musu tayi shigewarta daki dan ita yanzu ta fara gajia da bibiyarsa, Khairatee kuwa  bawai haryanxu tana sonta bane, tun sanda ta kusa mutuwa ta dalilinta ta hakura ta fita sha'aninta.
Tana ganin ya gama cin abincin ta taso dan dauke plate in, tana kai hannunta kan plate in ya rike wanda hakan ya sa ta dagowa suka hada ido, jin alamar ana shigowa ya sashi saketa, cikin sauri ta dauke plate in ta je ta aje sannan ta koma mazauninta. Bata jima da xama ba Hajjo da Haj Zinatu suka shigo tareda zama a falon, kallon Sadiq Hajjo tayi tace "ai sai kaje ka kwanta ko naga dare yanayi ka zauna kanata shirme anan ka bar matarka ita kadai" tabe baki Hajjo tayi tana cewa "da ya zauna yana hira da matarsa inne shirme"
"Hajjo wlh kina biyewa yaron nan dayawa kuma naga kema kina bayar wannan auren nasa wanda ni banyi na'am da ita ba, kuma Hajjo kwanaki da na kira nuna mun kikayi kamar baki san da abun ba ashe ma har kin santa" cewar Haj Zinatu, "kwarai kuwa nasan da ita tunda a wajena take, ai ba kowane mai rashin hankali irin taki ba, yanxu duk labarin yarinyar nan da ya baki bai ci ki tausaya mata ba, ai ko dan ceton rayuwarsa da tayi kya barta nan amma sabida rashin hankali zakisa ya rabu da ita, da kece aka yi wa 'yar cikinki hakan zaki ji dadine, toh wlh bari kiji ko da wasa naji kin sake musgunawa yarinyar nan sai na saba miki" sosai magangunan Hajjo ya bata mata rai yayinda take kara jin tsanar Khairatee a ranta, shiru tayi bata sake ce komai ba har Sadiq ya tashi ya musu sai da safe, ganin ya kasa tafia sai kallon Khairatee yake ya sa Hajjo cewa "Khairatee tashi kije kamar Ababakarin na son baki sako" yana jin haka ya fice daga falon, cikin sanyin jiki ta fice ta bi bayansa, da yake corridor da dan duhu sam bata lura da shi ba, ji tayi an jawota, zata saki ihu yayi saurin rufe bakinta da nasa, sai da ya gama kissing inta son ransa sannan ya rungumeta gam a jikinsa, cikin rada yace mata "BB zanyi missing dumin jikinki" ji tayi kamar tayi kuka dan itama a yan kwanakin nan ta saba da kwanciya a jikinsa, jin bata tanka mishi ba ya sa shi dago da fuskarta ya rike a hannayensa, sun jima suna kallon juna sannan ya sake leaning ya bata light kiss a lips inta  tareda cewa "nyt BB" bata iya cewa komai ba har ya fice daga side in, cikin sanyin jiki ta koma gun su Hajjo.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now