*PRINCE SADIQ*
*Na Billy Ladan*
*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO 🦅*
*29-30*
_wannan shafin nakune kawayen arziki *Maryam Chiroma* da *Hafsat Abuja*, we've never met but still u guys have always bn dia for me, supporting n encouraging me, u guys r rare gems,ina sonku har cikin qalbina,Allah ya hada fuskokinmu nan kusa, ina yinku sosai kawayen arziki_😘❤
A hankali Sadiq ya bude idonsa, abunda ya faru daren jiyane ya fado ransa ya juyo da sauri dan ganin halinda Khairi take ciki, ganin bata gadon ya sashi durowa ya shiga dube dube, kirjinsa sai da ya amsa ganinta da yayi zube a bakin kofar toilet, da gudu ya karasa ya dagota ya kwantar da ita a jikinsa ya shiga bubbugata, jin shiru ya sashi mikewa ya debo ruwa a toilet ya shafe fuskanta da shi, wani irin numfashi ta ja tareda yin ajiyar zuci sannan ta bude idonta a hankali, suna hada ido ta shiga turesa tana kuka amma rashin karfin da takeda shi ya sa bata iya wani turesa ba. Lallashinta ya shiga yi amma ina kamar yace ta kara ne ma, dagata ya fara yi dan ya maidata kan gado amma sam taki, cikin kuka tace "ni Hajjo nakeso, ka kiramun Hajjo" tashi yayi dan zuwa kiran Hajjon dan bayida wani option, idonsa na sauka akan bed sheet in ya nufi gadon ya yaye bedsheet in ya bude wardrobe inta ya canza wani ya kai dayan toilet, dagata yayi cak duk da tana wani zillewa ya daurata kan gadon sannan ya fita dan kiran Hajjo. Tana zaune kan sallayarta taji ana buga mata kofar daki,aje carbin da ke hannunta tayi ta nufi kofar ta bude, mamaki tayi ganin Sadiq ne a tsaye "lafia Ababakari kake buga mun kofa da sanyin asubar nan, ba dai nan ka kwana ba ko? Sosa keya ya shiga yi yace "Hajjo dama Khairi ce ba lafia kuma taki yadda in taimaka mata" yanda yake wani sussunne kai ya sa Hajjo dago abunda ya faru, salati ta shigayi yayinda ta nufi dakin Khairi cikin sauri, ganinta kwance a kan gadon ya sata yin wajenta da sauri tana dafata, ba karamin bugawa zuciyarta yayi ba ganin yanda idanun Khairi ya kumbura, cike da tausayawa tace "sannu Khairi, tashi muje kiyi wanka kizo ki sha magani" cikin kuka tace "Hajjo bazan iya tafia ba, gashi inaso in shiga bayi" kallon Sadiq tayi dake tsaye bakin kofar, shigowa yayi ya nufi inda take ya dagata cak yayi toilet da ita, ganin Hajjo ya sa bata mai gardama ba amma suna shigewa toilet in ta fara kokarin sauka daga jikinsa, ajeta yayi ta taka a hankali ta nufi wajen fitsarin, juyowa tayi ta gansa tsaye, kawar da kanta tayi tareda cewa "ka fita mana toh" juyawa yayi cikin sauri ya fice, tana ganin ya fice ta ida zama kan bayan gidan, ihun da ta saka shi yasa Sadiq banko kofar ya shigo, ganinta yayi tana yarfa hannu tana hawaye, karasaw yayi gunta yana tambayar abunda ya faru, Hajjo ma tuni ta shigo bandakin dan ganin koh lafia, kokarin tayar da ita Sadiq ya shiga yi amma ta hau ture hannunsa, ganin haka ya sa Hajjo karasowa tareda cewa "ka ga Ababakari jeka kawai ka barni da ita, fita ka barmu" cikin sanyin jiki ya fita ya je ya zauna bakin gadon tareda doka tagumi. Yana jin anbude kofar toilet in ya dago tareda mikewa ya nufesa, hannu ya sa dan ya dan tallabo Khairatee ita kuwa ta noke, harara Hajjo ta mai tareda cewa "Ababakari ka rabu da yarinyar nan, ka fice ma daga dakin tunda bata son ganinka" sumsum ya juya ya fice ya koma falo.
Can Hajjo ta fito bata ko bi ta kansa ba tayi dakinta ta dauko wayarta tayo kiran Dr Sufyan, Sadiq na zaune a falo kawai ya gansa ya shigo rike da kayan aikinsa, hannu ya mika mai suka gaisa sannan ya tambayesa dakin mara lafiyar, zumbur ya mike daidai lokacin da Hajjo ke shigowa falon, kallonta yayi tareda cewa "Hajjo wa zai duba haka? Harara ta mai tareda cewa "gidanku zai duba kaji, nace gidanku zai duba" bata rai yayi tareda cewa "gaskia Hajjo ni bazai dubata ba ina laifin a samo mace yar uwarta ta dubata amma wannan ba yi bane ace namiji godo godo yana duba matar wani, baiyi ba gaskia sam ba tsari" harararsa tayi tareda cewa "ai da kayi tunanin hakan tun farko kafun ka jefata halinda take ciki yanxu, koh ka ki ko ka so dole ya dubatan dan gyara tabargazar da kayi dan baza bar yarinya cikin ciwo ba" Dr Sufyan ne yayi gyaran murya yace "Hajia ai yana da gaskia kuma ba matsala sai in koma in turo matata tunda itama aikinta kenan" ta so kin yarda amma ganin yanda Sadiq duk yawani canja ya sata amincewa. Dakin Zali ta nufa ta sata daura ruwa a heater sannan ta koma dakin Khairi, ganin Sadiq a bakin kofar ya sata dage mai keya tana cewa "wato kai baka ji ko Ababakari, bance ka rabu da yarinyar nan ba, duk ma ka bi ka sa tana tsoronka, banda abunka Ababakari wa yake ma yar yarinya irin wannan afkawar haka" sosa keyarsa ya shiga yi dan duk ta sashi jin kunya, shi kansa baiso hakan ba but sam ya kasa controlling in kansa ne, yana tsaye a gun ta bude kofar ta shige, yana kokarin shiga ta turo kofar ta rufe, bubbuga kofar ya shiga yi yana rokon Hajjo ta bude amma ko ta kansa bata bi ba dole ya koma falo yayi zamansa
Yana jiyo sallamar matar Dr Sufyan ya tashi tareda amsa mata, shaida mai tayi ko ita waye yamata iso har zuwa kofar dakin Khairatee, bubbuga kofar ya shiga yi ganin Hajjo ba tashi zatayi ta bude ba ya sashi daga murya yace "Hajjo ga likitar ta zo" juyowa yayi ya dubi matar Dr Sufyan yana dan sosa keya yace "dan Allah Dr in ya kama harda dinki a mata allurar kashe zafi pls" bai jira amsarta ba ya wuce falo.
YOU ARE READING
Prince Sadiq
FanficUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...