Babi na Shauku

4.5K 144 0
                                        

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO 🦅*

*27-28*

_wannan shafin na baku shi kyauta members in *Zama Na Amana* facebook group_


Ganin Mahmoud tsaye gefen motar da yagani dazu ya sashi parking ya fito ya nufesa, wani irin kallo ya mai tareda cewa "lafia kake bina ko dai zaka ida mugun nufinka a kaina ne" dan murmushi Mahmoud yayi tareda cewa "am not here to fight u, gani nayi ka dauki mota ka fita ganin daren yayi nisa gashi kuma ana farautar ranka shi yasa na biyoka dan da hatsari fitarka warhakan kai daya" hannunsa daya ya sa saitin zuciyansa yace "aww bro am touched, ban san ka damu dani haka ba" kawar da kansa yayi sabida yasan gatse Sadiq ke masa, ganin Sadiq ya juya zai shiga motarsa ya sa shi cewa "Sadiq ka san in dai zargin da ke a kaina gaskia ne da bazaka bar nan da rai ba ko, i have tried ol i culd dan in wanke kaina daga zargin da kake mun but it sims zuciyarka ta gama yarjema akan cewa ni Mahmoud zan iya kasheka, ban taba tsintar kaina a irin wannan situation in ba, fadar yanda nakeji cikin raina is near impossible, i feel hurt, betrayed and insulted, duba da irin zamana da kai har zaka iya zargina Sadiq, kai da kafi kowa sanina da sanin abunda zan aikata da wanda bazan iya ba sai gashi ka rufe idonka ka mun mummunar shaida, bazan taba mantawa da wannan rana ba Sadiq kuma i promise u zakayi dana sani, n from now onwards bazan sake kokarin wanke kaina daga zargin da kake a kaina ba, u can tink wateva u want, n kamar yanda kace ba mai ma katanga da kujerar sarautan Wursama toh nima haka, so d battle is on Allah ya ba mai rabo sa'a" yana gama fadin hakan ya shige motarsa ya bar wajen, cikin sanyin jiki Sadiq ya ja kafarsa ys nufi motarsa shima ya ja yabi bayansa, kusan tare suka shigo masarautar, ko kallon juna basu sake yi ba kowa yayi side insa.

Washegari tun wajen karfe takwas mai martaba ya yo kiransu dan tun shigowarsa aka shaida mai abunda ya faru, ko da ya tambayi Mal Aminu gameda abunda ya samu boye batun kibiyar yayi sabida Sadiq ya sake jaddada mai akan cewa kar ya shaidawa mai martaba dan ya san hakan ba karamin sabani zai kawo ba, sosai abun ya dami mai martaba sabida hakan ne ma yasa a take a ka kara mai dogarai tareda nemawa Sadiq masu tsare lafiyarsa, ya so a daga auren sai dai Sadiq da kansa ya nuna bai son haka ya kuma amince aka cigaba da shirye shirye.

A yau jumma'a dubban mutane suka shaida auren *Prince Sadiq* da Farhana, Zali na jiyo announcement in ta wuce sashin Haj Zinatu dan taje ta ci kukanta, tana shiga ta ga Umma Saude zaune da su Hajjo, da gudu tayi kanta ta fada jikinta ta shiga kuka, a razane Umma Saude ta dago kanta tana cewa "subhanallahi, auta meh kuma ya faru kika shigo da kuka haka" maimakon ta tanka sai ma cigaba da kukan da tayi, rarrashinta umma Saude ta shiga yi har sai da tayi shiru, gyara kwanciyarta tayi a kan cinyar umma Saude sannan tace "Umma nayi kewarku ne shiyasa" shafa kanta tayi tace "muma munyi kewarki Zali musamman ma yayunki, cemun ma sukayi lalle in zan koma in tasoki gaba mu dawo" dan turo baki tayi tace "a'a ni umma bazan biki ba salsar zan koma da Hajjo" Hajjo na jinta tace "a'a ni bazaki kara zuwan mun gida ba ki karasa cinye mun dan abincin nawa" daria umma tayi tareda cewa "toh kinji Hajjo tace bata sonki, sai mu tafi gida ko? sake turo baki tayi tace "wlh umma Hajjo so take, kwanaki ma da nace zan tafi fa harda dan kukarta, toh komawa Salsar kamar nayi Hajjo in kin ga dama in naje kar ki bani abincin naki" haka suka cigaba da yi kamar wasu kishiyoyi su Umma sai daria suke musu, shafa kan Zali umma tayi tana cewa "auta ko dai miji muka samu a Salsar ne da aka dage baza a dawo gida ba? Hannayenta ta sa ta rufe fuskantar tareda cusa kanta jikin ummar tata, daria umman tayi tana cewa "masha Allah, ni dama nayi tunanin hakan" tabe baki Hajjo tayi tareda cewa "wannan da kullum tana like a dakin ne har zata samu miji a Salsar, ga ta da shegen son jiki kamar meh, ai mu yan Salsar bamu son mace haka" tashi Zali tayi ta kalli Hajjo tace "ai Hajjo nima na fi karfin yan Salsar wlh, abu duk mazan ma suna nan wasu yaga yaga ko tsari basuda shi, koh me zaki fada dai kamar na koma Salsar" tana gama fadin hakan ta yi shigewarta ciki dan zuwa ta cigaba da kukarta.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now