*PRINCE SADIQ*
*Na Billy Ladan*
*45-50*
_Wannan shafin nakine
*Hafsat M Sheriff*,nagode da kulawarki gareni,Allah ya bar zumunci😘_
*This chapter is unedited, ayi hakuri ayi managing pls*
"A'a abban Zali yau ka barni inyi magana, nagaji da kareni da kake, ban ma cancanci ka kareni ba, yaya yau zan gaya maka gaskiyar al'amarin" share kwallan da suka zubo mata tayi sannan ta cigaba "yaya koh zaka iya tuna driver da aka kawo mun mai suna Bala? Kai ya gyada alamar eh sannan ta cigaba "tun da Allah ya hadamu naji wani abu game da shi, ba a dau lokaci ba kuwa soyayya mai karfi ta shiga tsakanina da shi, in aka dauke Nanna babu wanda ya san da wannan batu dan komai cikin sirri muke yinsa, ana haka mai martaba ya fito da zancen aurena ga abban Zali, sanin dokar gidan nan ya banida zabi sai na zabi mu gudu amma sam Nanna ta bi ta toshe duk wani hanyar da zan gudu, a haka akayi aurena da Abban Zali sai dai har kusan shekara babu wata kyakyawar alaka tsakaninmu, duk da na kasance matar aure banida wani tunani sai na bala, a haka har na haifo Zalihat sam babu wata jituwa tsakanina da abbanta, muna dai sunan ma'aurata amma sam babu wata soyayya ko walwala a gidan wanda kusan duk matsalar daga wajena ne dan yana iya kokarinsa wajen kyautata mun amma sam bana gani, watarana ina daki ina shirya Zaliha sai ga abbanta ya shigo da wayata a hannunsa, nuna mun message na Bala yayi wanda ya shigo wayata ba da jimawa ba, batare da ya ji daga bakina ba yace ya mun saki daya, son da yake mun bazai barshi ya zauna dani alhalin ina tarawa kaina zunubi ta hanyar aikata zina ba, maimakon na kare kaina in nuna mishi ba abunda ke faruwa tsakaninmu sai nayi amfani da wannan damar na tafi dan kasancewa tare da Bala, koh da na tashi tafia ya hanani Zaliha dole na tafi na barta, sanin in na koma gida zan fuskanci kalubale yasa na bi Bala muka bar garin gaba daya mukaje can kauyen Shika sai dai ba a je ko ina ba na fara fuskantar canji daga garesa, wulakancin yau daban na gobe daban, dama wat was i expecting, i was reaping wat i sow, na zabi soyayya, na bijerewa iyayena na zabi kasancewa da shi akan na koma gareku so i couldn't complain, dole na zauna na shanye duk wani wulakancinsa, koh da na samu labarin rasuwarsu mai martaba nayi kuka har nagaji sanin sun tafi da fushina ba tareda na nemi yafiyarsu, koh da na so zuwa Bala ya hanani dole ya sa na zauna, nayi nadamar abubuwan da na aikata yaya, ku yafemun" ta karashe tana kuka mai cin rai, shiru dakin yayi baka jin komai sai kukan Ma,Khairatee da Zali da labarin ya gama rikitasu, Sadiq ma mamaki sosai ya rufeshi jin Khairatee jininsa ce, gyaran murya maimartaba yayi sannan yace "tabbas Aminatu kin tafka kuskure wanda har kinsa na riki aminina akan laifin da bai aikata ba, duk da haka bamu isa mu ja da yin Allah ba, komai yayi daidai ne, hakan ya kaddara a babin rayuwarku ba abunda zamuce sai dai Allah ya yafemu baki daya, batun su maimartaba kuma tun suna raye basu da batu sai naki, kuma sunce du sanda kika dawo a fada miki sun yafe miki dunia da lahira, saura ki cigaba da neman wa kanki gafara wajen ubangaji"
Kallon Abban Zali Ma tayi sanna tace "banida bakin cewa ka yafemun, na ha'ince a zamarmu amma duk da hakan ba ka taba kina ko da na minti daya ba, alhakinka kadai ya isa na tsinci kaina a wannan wahalar, ka yafe mun Abban Zali" murmushi yayi tareda cewa "komai ya wuce Amina,na yafe miki" "toh Alhamdulillah" cewar mai martaba "nayi farin cikin dawowar yar uwata cikinmu, dama tun ranar da nayi tozali da Ummul Khairi naji cewa ita jinina ce sai kuma gashi ya zamto gaskia, babu abunda zamuyi sai dai muyi godia wa Allah, kuskure dai an riga anyi shi sai a yafi juna, ku kuma" ya juyo yana kallon yaran yace "ku kasance masu hakuri da bin iyayenku, duk sanda aka yanke wata hukunci da bai muku ba ku sanar da mu kafun ku dauki mataki da kanku, ke kuma Zali ga ummarki ta dawo gareki, bana so ki riketa da komai, duk abunda ya faru ya farune cikin kuruciya da gigin soyayya, ki bita sau da kafa so dt u mk up on d days you have missed" tashi tayi tana sharar kwalla tace "she wil neva b my mum, ni baba Saude ce mahaifiyata, ba uwar da zata zabi soyayya akan jinjirar 'yarta da batasan komai ba, so bana sonta bana bukatarta a rayuwana, dia is ntn to build up on cos it late so bana bukatarta" mari baba Saude ta dauketa da shi tana cewa "hankalinki daya kuwa Zali, mahaifiyar taki kike fad'awa hakan, maza koma ki bata hakurin kan na sab'a miki" maimakon tayi hakan ta juya ta fice daga fadar tana kuka, zata tashi ta bita abban Zali ya dakatar da ita "barta ta huce tukunna, she nids d space" kai ta gyada mai tareda komawa ta zauna, Farhana da tun da aka fara maganan nan mamaki ya hanata koda motsi ta tashi ta sulale batareda sun lura da hakan ba, Haj Maryama ce ta shigo da sallamarta, ba karamin mamaki tayi ba ganin Ma zaune, cike da girmamawa ta gaida mai martaba tareda cewa "gaskia yaya ba a kyauta mun, yanxu in ba dan jakadiya da taje ta fada mun ba ana taro ma ban sani ba, ace kuma har Amina ta dawo garemu ba wanda ya sanar danu, gaskia wannan wariya da ake mun ta fara isata" murmushi mai martaba yayi tareda bata hakuri sannan ya shiga mata bayanin abunda ya faru, duk da taji haushin dawowar Ma da yartata sam bata nuna ba saj ma wani farin ciki da take yayinda zuciyarta kuwa taf bakin cikine, dole tayi gaggawar daukar mataki tun kan abu ya gagareta, tana ji tana gani sai wannan Sadiq in ya haye kujerar gashi harda mata biyu yayinda Mahmoud ko maganar auren bayayi, hadasu mai martaba yayi ya musu nasiha mai ratsa jiki tareda jaddada musu cewa su so junansu, su guji hassada da kyashi wa junansu, da kyar Haj Maryama ta jira ya kai aya sannan ta fice. Tashi su Ma suma sukayi suka fice dan komawa sashinta aka bar mai martaba da abban Zali da su Mahmoud.
YOU ARE READING
Prince Sadiq
FanfictionUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...
