👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*PRINCE SADIQ*
👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*Na Billy Ladan*
*8-9*
Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, nauyin da yaji a kansa ne ya sashi juyowa tareda bude idanunsa a hankali, wani dogon tsaki ya ja tareda tashi "kai mahaukacin ina ne zaka zo ka tsayawa mutane cirko cirko akai suna bacci" bawan da ke tsaye a kansa russunawa yayi yana "Allah huci zuciyar yarima" harara Sadiq ya watso masa sannan ya fara gyara jikinsa, shi kadai yasan irin dadin da baccin yake mai kan a tada shi, juyowa yayi yaga haryanxu bawan na nan, wani banzan kallo ya mai tareda cewa "meh kuma ka tsaya kake mun bayan ka tadani, bace mun da gani kafun insa a tsare mun kai" jiki na rawa ya tashi yace "a gafarceni ranka shi dade, mahaifiyarka ce ke son ganawa da kai" yana gama fadin hakan ya juya cikin sauri ya bar wajen
Sai da ya shari kusan minti biyar a wajen sannan ya tashi ya nufi side insa, wanka yayi ya shirya cikin jamfa ya fito sai kamshi yake ya nufi sashin Hajia Zinatu
Zaune ya sameta itada Farhana da akayi kicin kicin da fuska, kallo daya yayi mata ya karasa gefen Hajia Zinatu tareda gaisheta, yanayin da ta amsa mai ya nuna ranta a bace yake wanda ya tabbatar mai Farhana ta gaya mata komai, tun da ya zauna bai dago kansa ba, ta gefen ido yake lura da irin kallon da mahaifiyarsa ke mai, gyaran murya tayi tace "Sadiq dago ka kalleni, wani cin mutuncin naji ka yiwa Farhana" harara ya watsawa Farhana sannan ya dubi Hajia Zinatu yace "wani abun tace na mata? Kallon kar ka raina mun wayo ta mai tareda cewa "kai Sadiq ban son rainin hankali, wai ka manta yarinyar nan aurenta zaka yi ne da kaketa yaba mata irin wannan maganganu marasa dadin ji" dan bata rai yayi tareda cewa "kema fa cewa kikayi aurenta zanyi umma amma kuma ake mun fada gabanta kamar yaro, ai sai ta rainani, kuma ita bata fada miki abunda tayi mun bane? Tabe baki Hajja Zinatu tayi tareda cewa "in ta raina kan ma ai kai kaso, da bakayi abun fadan ba bazan tasaka a gaba ina ma fada ba, kuma nasan halinka Sadiq tsaf ka aikata abunda Farhana ta fada, kar ka kuskura in sake jin makamancin hakan ya faru in ba haka ba sai nayi mugun saba ma" takaici ya ma hanasa amsa mata, ta ya zata tsaya tana gaya mai irin wannan maganganu a gaban wanda ake ikirarin zai aura, in ba salon ta rainasa ba, mamaki ma yake da bata ji ta bakinsa ba ta hau balbaleshi da fada, maganar da yaji tana yi ya sashi dagowa, "tunanin meh kakeyi da baka amsa min ba"
"naji umma" kawai ya iya fada, kokarin tashi ya fara yi yaji Farhana tace "Hajia ni inaga ma ba da son ransa yake wani abun ba kamar zugasa Mahmud yake, dan ko da naje tare suke a zaune kafun daga baya ya tashi ya barmu amma sai da ya tsaya gaya mai abu a kunne tukun, na tabbata shi ya zugasa ya mun wannan cin mutuncin" kallon tuhuma Hajja Zinatu ta bishi da shi, yayinda shi kuwa yake watsawa Farhana wani irin kallo, "eh dole kake kallonta kamar zaka hadiyeta, saboda ta taba ma rabin ranka ko, ina rabaka da yaron nan amma sam baka ji, kai a ganinka so na tsakani da Allah yake ma ne, in baka sani ba toh ka sani kujerar ubanka yake hari kuma da zarar ya cimma burinsa daga ni har kai ba mai tsira a hannunsu, gwara ka farka ka san inda dare yama" iya baci ran Sadiq ya baci, wani tsana da haushin Farhana ya rinka ji dan shi sam ya tsani abunda zai shiga tsakaninsa da dan uwan nasa shiyasa sam basa jituwa da mahaifiyar tasa dan tun basu mallaki hankali ba take kokarin rabasu amma har yau Allah bai bata iko ba, rai a bace yace "ni zan wuce umma" kallonsa tayi tareda tabe baki tace "yanxu dan an tabo dan gold in naka shine kake wannan hade ran, ni gani nake ko ni da na haifeka baka mun irin son da kake wa wannan shegen yaro, toh wlhy sunyi kadan komin maitarsu sai sun sake mun d'a........bata ma karasa ba Sadiq ya tashi ya fice dan wani irin suya da zuciyarsa keyi, baki bude Hajja Zinatu ta bishi da kallo, kai ta kada tareda cewa " ah lalle, dole in tashi tsaye dan mutanen nen basu barka a haka ba, kallon Farhana tayi tareda cewa "kema zama bata kamaki ba, dole ki tashi tsaye ki taimaka wa mijin naki dan sun gama shanye shi, dole ki shigo tsakaninsa da Mahmud in ba haka ba kina ji kina gani, sai yanda Mahmud yace yayi zaiyi dake"

YOU ARE READING
Prince Sadiq
FanfictionUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...