19

4.4K 155 5
                                        

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*43-45*

_Dis page is dedicated to my takwaroris, manyan writers, kaf online writers masu sunan nan sunfi yawa, 😜masu gadajen zinarai, Allah ya kareku ya karo muku fasaha_
*Billyn Abdul*😘
*Bilkisu Bilyamin*😍
*Billy Galadanchi*❤
*Billy Tabaco*❣
*Bilkisu Z Yau BK*💞
*Billy Giro*
*Billy S Fari*
_Kai harma dani_ *Billy Ladan*

Jijjigata ya shiga yi yana kiran sunanta amma ko motsi bata yi, cincibarta yayi ya nufi waje da ita, gun motarsa ya nufa ya bude ya sata a ciki sannan ya zagaya ya tada motar, cikin zafin nama ya figeta ya nufi asibiti.

Suna isa ya sake cincibarta yayi hanyar emergency da ita, ana ganinsa akayi saurin karbeta daga hannunsa aka daurata akan trolley akayi side room da ita aka shiga bata taimakon gaggawa.

Sadiq ya kasa zama sai safa da marwa yake, wayarsa ya cire ya kira Mahmoud ya shaida mai, ganin nurse ta fito daga dakin ya sashi katse wayan ya nufeta da sauri "sister pls tell me my wife is still alive, kice mun tana da rai" ya fada cikin tashin hankali da yanayi na nuna tsantsan damuwa, murmushin karfin hali ta mai tareda cewa "insha Allah she will b fn,muna iya bakin kokarinmu" tana gama fadin hakan tayi gaba dan ita bata da tabbas akan Khairatee, ita da ba dun tana tsoron ance Prince nasu bane da sai tayi addressing insa tsab, yana sonta ya barta da yunwa har ya mata illa, kallo daya zaka mata ka gane abunda ke damunta yanda har patar jikinta ya fara wani tattarewa ga lips inta duk yayi dry, yana tsaye ta zo ta sake wucesa batareda ta ko kallesa ba ta koma dakin.

Yana zaune bakin dakin ya dafe kansa da hannunsa ya ji an tabasa,  sai da ya share guntun hawayen da ya gangaro mai sannan ya dago, Mahmoud ya gani zaune gefensa "ya mai jikin? Ya tambayesa cike da damuwa, da kyar ya iya bude bakinsa yace "tun da muka zo ban sake ganinta ba,sun dai ce she wil b fyn insha Allah" ya karashe kamar zaiyi kuka, rufe bakinsa ke da wuya ya hango mai martaba yana takowa a hankali dogarai na mara masa naya, gefensa kuwa su Haj Zinatu ne, "ni na gaya musu bro" cewar Mahmud da ya ga yana kallon su mai martaba, murmushi kawai ya mai tareda daga mai kai. Tashi sukayi suka taro mai martaba tareda bashi wajen zama, zamansa yayi daidai da fitowar nurse na dazu, tana ganin zugarsu ta koma ciki, ba a jima ba kuwa sai ga Dr ya fito, karasawa yayi ya gaida mai martaba cikin girmamawa tareda basu izinin shigowa.

Kwance take akan gado hannunta sanye da drip, duk wanda ya santa a da zai dauka ba ita bace sabida yanda ta dawo, kowa na dakin saida ya tausaya mata, gefenta Sadiq ya je ya tsaya tareda riko hannunta sam ya ma manta gabansu mai martaba yake, mai martaba ne ya yi gyaran murya yace "Dr me ke damun  inlaw nawa ne haka? h zucia Dr yayi sannan yace "ranka shi dade, a yan binciken da mukayi mun gano ciwon yunwa ke damunta wanda daba dun Allah ya tsare ba da ya mata lahani ba wa ita kadai ba harma da abunda ke cikinta" wani irin kallo mai martaba ya mai sannan yace "ban gane ciwon yunwa ba, so kake kace mun bata samun ishesshen abinci or what?  "Allah huci ran sarki, ba nufina kenan ba, zaiyu bata cin abinci ne ko maybe ta tafi hunger strike ko makamancin hakan dan na tabbata ko makocinka bazaiyi kukan yunwa ba balle kuma surukarka guda, mudai binciken mu ya nuna rashin cin abinci ne ya jefata cikin wannan halin

Kowa na dakin mamakin kalaman Dr yake bnda Hajja Zinatu da ido ya raina ya fata, wani irin murda cikinta ya fara dan tasan in har asirinta ya tonu mai martaba bazai mata da kyau ba, Khairatee ce ta shiga fisge fisge a kan gadon, yin kanta suka yo gaba daya ganin tana kokarin cire cannula, danneta Dr da sauran nurses in sukayi amma duk da haka bata bar fisge fisge ba, matsowa Sadiq yayi kaman zaiyi kuka ganin yanda suka danneta, suna hada ido ta bar fisge fisgen da take ta kura mai ido, dauke kanta tayi daga kansa ta shiga bin dakin da kallo, idonta na sauka kan Haj Zinatu jikinta ya hau rawa, nan ta hau fisge fisge tana cewa "kuce mata zan tafi karta kasheni da yunwa, wayyo Ma ki zo ki cece ni, kizo ki daukeni kar ta kasheni" sosai take kuka harda hawayenta, da kyar aka samu aka mata alluran bacci tayi shiru. Haj Zinatu ji tayi kamar ta saki fitsari a wajen dan kallon da  mai martaba ke wurgo mata kadai ya nuna sun fahimci abunda Khairatee ke nufi, sallamar nurses in Dr yayi sannan ya dubi mai martaba yace "tunda tayi bacci yanxu i think a bar mutum daya kawai a kanta har zuwa sanda zata tashi, but til then zamu cigaba da managing inta, sai a dan samo mata ko kunu ne dan in ta tashi zata bukaci abinci sabida maganin da aka bata, sannan please a kula ta ci abincin nan in ta tashi ko dan abunda ke cikinta" yana gama fadin hakan ya fita dan basu damar tattaunawa dan daga gani suna bukatar hakan, yana fita mai martaba ya kalli Haj Zinatu yace "zakiyi mun bayanin abunda ya faru ko kuwa? Cikin rawar jiki tace "Allah huci ran mai martaba, wlh sharrin shaid'an ne" kasa yayi da kansa yana kadawa "yanxu Zinatu meh yarinyar nan ta miki da zaki mata horon yunwa, koh ke da girmanki baki jure yunwa balle yar karamar yarinya mai juna biyu for dat matter, wallahi muddin wani abu ya samu yarinyar nan ko d'an da ke cikinta kiyi kuka da kanki, wannan ai rashin imani ne, in ma laifi ta miki ki mata wani horon daban mana, balle na tabbata yarinyar nan ba wani abun da ta miki, bakin haline kawai irin taki da neman ki tozartani a idon jama'a, kuma burinki ya cika, muddin wannan abu ya fita cikin jama'a laifina za a gani, ni kika tozarta Zinatu sabida haka ki saurari hukunci mai tsanani" yana gama fadin hakan ya fice daga dakin, cikin sanyin jiki ta bi bayan mai martaba aka bar Sadiq da Mahmoud kawai a dakin.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now