👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*PRINCE SADIQ*
👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*Na Billy Ladan*
*23-24*
_Wannan shafin nakine Anty Queen Mermue,words can tell u how much i appreciate, adore and luv u, Allah ya kara daukaka mun ke Anty Na, i luv u so much😘_
A hankali ta bude idonta, kamshin turaren Sadiq da taji a dakin ya shaida mata ya shigo dakin, murmushi tayi tareda tashi tana kallon agogon da ke dakin, mamaki tayi ganin har karfe uku tayi, da sauri ta fada toilet ta watsa ruwa tareda dauro alwala, sai da ta idar da sallah tukun ta shirya ta fito, Zali kawai ta tarar a falon bata ko bi ta kanta ba ta wuce kitchen ta debo abinci ta zo ta zauna tana ci sam bata lura da hararar da Zali ke jeho mata ba, Zali kuwa dabarace ta fado mata, murmushi tayi tareda daukar wayarta tayi dialing number Sadiq amma bai daga ba, sai da ta kira na uku sannan ya daga, cikin kashe murya tace "Ya Sadiq ka sauka lafia? daga can gefen ya amsa mata da lafia a takaice dan shi sam bawai son magana da ita yake ba, yanxun ma ba yanda ya iya ne ya sa ya dauki kol inta, sake kashe murya tayi tana cewa "har ma mun fara missing inka wlh ya Sadiq" diff taji ya kashe wayar amma da yake Zali yar dunia ce sai ta cigaba da hirar ita kadai harda su kyalkyalewa da daria duk dan ta kular da Khairatee, Khairatee kuwa duk da abun yana taba mata zucia sam bazaka gani a fuskarta ba cos if dia is anything she learnt in lyf is neva show d ppl who want to hurt u dt they have got to u, kome Zali zatayi dan bakanta mata bazata taba nunawa cewa abun ya dameta ba, cikin nutsuwa ta gama cin abincin nata ta tashi ta wuce kitchen ta aje plate in sannan ta dawo parlorn dan tayi kallo, ganin Zali na danne danne a wayarta ya shaida mata sun gama wayar tasu.
Bata jima da zama ba Hajjo ta fito itama ta zauna, barka da fitowa Khairatee ta mata ta amsa cikin sakin fuska, sosai Hajjo ke son Khairatee dan yarinyar akwai nutsuwa da sanin ya kamata, kallon Zali tayi tace "Zali dauko mun reading glass ina da newspaper akan gadona" tashi Zali tayi dan zuwa aiwatar da sakon Hajjo, tana fita Hajjo ta kalli Khairatee tace "angon namu yace in tayasa miki sallama, ya shiga dan kuyi sallama sai ya tarar kina bacci kuma in yace zai jira har ki tashi zaiyi dare, ya ma ce in gaisheki kuma in ce miki ya isa lafia, kuma sannan anjima za a turo da bayinki daga can cikin fada wayanda zasu na kula da ke tareda debe miki kewa" godia tayi wa Hajjo sannan suka shiga hira, fitowar Zaline ya katse musu hirar tasu, Hajjo ta karbi jaridar tata ta fara karantawa yayinda Khairatee ta cigaba da kallonta.Washegari kamar yanda Hajjo ta fada aka kawo wa Khairatee bayi mata guda biyu, yan mata ne da zasuyi sa'anni da Khairatee dan Hajjo tana ganin zata fi sakewa da su. Yanxu komai nata yi mata ake, daidai da ruwan wankanta sai sun hada mata duk da tana hanasu sauran abubuwan amma ina sai sunyi. Cikin sati guda Khairatee ta fara sabawa da su, in ba dai tana tareda Hajjo ba toh zaka sameta da bayinta Fure da Hinde a garden na bayan dakinta dan sosai take jin dadin labarai da suke mata dan dama ita akwaita da son stories ko ma wace irice.
Tafiyar Sadiq da sati daya Hajjo suka fara shirin zuwa Wursama bikinsa, bata so tafia da Zali ba dan bataso a bar Khairatee ita daya amma sam Zali ta nace dole Hajjo ta yarda zasu tafi tare amma sai da ta ja kunnenta kan cewa ta iya bakinta banda fadi ba a tambayeta ba, muddun ta karya doka to sawa zatayi a maidota, dole ta yarda dan sosai take son ganin masoyin nata, ranar da zasu tafi Khairatee har da yar hawayenta dan tasan sam zaman gidan bazai mata dadi ba duk da ma akwai bayinta amma tafi sabawa da Hajjo, sai da taga motarsa ta fice ta koma ta shige dakinta ta shiga rusa kuka, a haka su Fure suka zo suka sameta, lallashinta suka shiga yi suna bata baki, da kyar ta iya tsaida kukan nata ta dago tana kallonsu tace "yanxu shikenan in yayi aurensa ni kuma sai ya sakeni ko tunda ya samu wacce yakeso" ta karashe ta share hawayen da ya gangaro a fuskarta, Hinde ce tace "Yarima bazai sakeki ba insha Allah, ke da shi zaku rayu tare har zuwa lokacin da Allah ya diban muku a dunia" kallonsu tayi sannan tace "Hinde aurena da Yarima fa na dan lokacine da zaran kuma lokacin yayi zai sallemeni, zuciyata kuma da karambani ta je ta kamu da sonsa, ta kamu da son wanda yafi karfinta, wanda bazai taba sonta ba ko mata sun kare, wannan kuka da kuka ga inayi na tausayawa kaina ne dan nasan Yarima bazai taba sona ba" Fure ce ta dan dafata tace "Wlh kina da komai da zaisa Yarima ya soki kuma insha Allah ma zai sokin, addu'a kadai zamu cigaba da yi, kuma kema dole ki daure ki gaya masa abunda ke cikin ranki, watakil shima yana jin yanda kike ji, in dai har kika fallasa mai sirrin zuciyarki ina ganin za a yi dace, sannan duk sanda ya sake juyomu akwai shiri na musamman da zamuyi miki wanda na tabbata zamuyi nasara zai ma manta da wani batun saki" ajiyar zucia Khairatee tayi tareda yi musu godia sannan suka fara tattauna shirin da zasuyi.

YOU ARE READING
Prince Sadiq
FanfictionUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...