17

3.9K 147 4
                                    

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*38-40*

"Mahaifiyarki na da gata a inda ta fito,iyayenta sanannu ne a wajen kauyen nan, kaddara ya sa ta baro iyayenta kunyar abunda ta aikata kuma ya hanata komawa, shiyasa Khairi har yau kikaga ummarki ta kasa rabuwa da abbanki dan bata da inda zata in ta rabu da shi dan tayi alkawarin bazata sake komawa ga iyayenta ba sabida abun kunyar da ta aikata" cike da mamaki Khairatee ke kallon Nanna, da kyar ta iya bude bakinta tace "Nanna ban gane iyayenta sanannu ne ba, tanada wata uwace bayan ke Nanna? Ta karashe bakinta na rawa, lumshe ido Nanna tayi a hankali sannan ta sake budesu ta zubasu kan Khairi, "zan fada miki ko ni wacece sai dai bana so ki riki ummanki ko ki mata bahaguwar fahimta ko ki mata muguwar fassara akan abunda ta aikata, abunda ya faru ya farune cikin kuriciya da kuma gigin soyayya, abbanki ya kasance driver a gidan kakanninki kuma shi aka sa matsayin mai kaita duk inda zata, a haka soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu batareda kowa ya sani ba, in aka dauke ni bawanda ya san da wannan soyayyar sabida shakuwar da ke tsakanina da ummarki, tun haihuwarta ni ke kula da ita hakan ya sa mukayi shakuwar da bata shakkan gaya mun ko wani damu tata kuma nakan yi iya kokarin bata shawarwari, koh da naji labarin soyayyarta da abbanki na so nuna mata abun ba mai yiwuba bane sabida yanda tsarin gidansu yake amma ina tayi nisa, ana haka wani abokin abbanta yazo nemawa dansa aurenta, ba tareda anji ta bakinta ba aka fara shirye shiryen biki dan haka al'adar gidan take matan gidan basa zabawa kansu miji kuma duk wanda aka zaba miki shi zaki aura, tunda ummarki ta samu wannan labari ta fara karewa,lokaci daya tabi ta zube ta shiga tashin hankali, a wannan lokaci kowa ya dauka zancen rabuwa da gida ya sata hakan sai dai ni da ita mun san asalin dalilin ramar nata" ajiyar zucia tayi sannan ta cigaba "bazan iya fada miki ko anyi auren ko ba a yi ba dan wannan abune wanda na barshi dan kiji daga bakin ummarki sai dai bayan shekara da faruwar hakan ummarki ta yanke shawarar barin komai dan ta gudu da masoyinta wato abbanki, shakuwar da mukayi da son da nake mata tamkar yar da na haifa ya sa nima na tattara kayana na bita sabida ba amfanin zamana a can tunda na yi iya bakin kokarina na hanata tafia taki ji, kuma muddun aka wayi gari bata nan toh zan iya rasa raina, dafarko anyi zaman lafia cike da son juna tsakanin iyayen naki amma daga baya da ya samu kansa shima ya zama wani abu a dunia sai ya juya mata baya ya kawota nan ya aje inda sai ya ga dama yake juyo mu, mahaifiyarki ta zabi ta bar kowa da komai nata ta bar rayuwar jin dadi da gata ta zabi soyayya akan 'yan uwa da iyayenta karshe taga sakamakon bijirewa iyayenta da tayi"

"Khairi nasan zakiji kamar bamu kyauta miki ba amma na dau alkawarin cewa zan rike sirrin mahaifiyarki, da ba dun wanna ciwo da nake ji kamar bazan tashi daga ita ba da ba abunda zai saki jin wannan batu amma yanxu na ji na sauke nauyin da ta jima tana addabata zan tafi cikin kwanciyar hankali sai dai Khairi, ki bi ummarki cikin hikima da dabaru har ki gano iyayenta ki sadasu hakan ne kadai zai sa taji zata iya fita daga cikin wannan auren da bai kareta da komai ba sai tarin wahala, sannan ke kuma Khairi ko bayan babu ni ban yadda ki nuna fuskarki a wannan kauye ba har sai kin shirya fuskantarsu wanda inaso hakan ya kasance bayan kin sadu da kakanninki dan nasan haduwa dasu zai baki karfin gwiwar fuskantarsu tareda gyara abubuwa da dama da kika jima kina mafarkin gyarawa a kauyen nan" tana kaiwa nan tayi wani ajiyar zucia tace "tashi kije nasan mijin naki na jiranki" gaba daya ji tayi komai ya tsaya mata, mesa ummarta zata boye wannan muhimmin abu daga gareta, ko kadan bata ji zafin abunda ummartata tayi ba dan bazata taba fushi da ita ba dan son da take mata kuma bayan Nanna bata da tamkarta kuma tasan itama Ma na sonta fiye da komai, ta san what it's like to b lost in someone's luv sabida haka she won't judge her, sai da Nanna ta sake magana ta dago fuskarta tace "Nanna ki barni in kwana dake dan Allah" turo kofar da akayi ya sa su maida hankalinsu wajen, Ma ce ta shigo dakin tareda zama a gefen Nanna, kallon Khairatee tayi tace "maza tashi kije yana jiranki, dakin nan na BQ a gyare an tanada muku komai abincinku ma na can" dan turo baki tayi tana mai kallon Nanna, murmushin karfin hali Nanna tayi tace "tashi kije Khairi gobe in Allah ya kaimu sai mu kwana tare koh" tana guna guni ta wuce ta fice, a falo ta gansa yana danna wayarsa, kallo daya ta mai ta kau da kai a zuciyarta tana cewa "yanxu wannan ko dan kunyan surukai ai sai yace a barta ta kwana cikin gida, koh da yake bata ga laifinsa ba tunda Ma da kanta tayi hakan, ita kam da ta ita ne ba abunda zaisa su kebe ko dan kunyarsu Ma" gyaran murya tayi da ta karaso gefensa tace "muje ko" murmushi ya mata tareda tashi yana gyara rigarsa yace "after u BB" tabe baki tayi tareda yin gaba yayinda yake biye da ita.
Wani kamshi mai dadine ya bugesu da suka shige dakin, hannu ta sa ta kunna switch haske ya gauraye dakin, komai tsaf yake, hanya ta basa ya shige sannan ta rufo kofar, kujerar da ke dakin ya zauna a kai ita kuwa ta karasa ta zuba mai abincin ta daura mai a kan stool da ke gabansa sannan ta koma itama ta zuba nata, tafi minti biyar tana ta jujjuya spoon in a hannunta amma ko loma daya bata yi ba har Sadiq ya gama nasa ya zo ya zauna gefenta sam bata sani ba dan tayi zurfi cikin tunani, hannu ya sa ya karbe spoon in, sai sannan ta dan firgita ta dago suka hada ido, wani tausayinta yaji ganin damuwa fal a kwayar idanunta, maganganun Nanna ne ya fara zuwa mai, diba abincin yayi a spoon ya kai bakinta ta kawar da kanta, hannu ya sa ya juyo da fuskarta yace "please ki daure kici Khairi" yanda ya kira sunanta sai ta ji bazata iya mai musu ba, a hankali ta bude bakinta ya fara bata abincin, sai da ya tabbatar ta koshi sannan yace ta tashi ta kimtsa zai shigo musu da kayansu, tana ganin fitarsa tayi saurin tattara kayan ta aje gefe ta fada toilet, watsa ruwa tayi da sauri ta fito ta nufi kan gado dan dauka hijabinta, jin karar bude kofa ya sata daskarewa dan gaba daya towel in ko gama rufe cinyarta baiyi ba, tana jinsa har ya tako zuwa bakin gadon ya aje kayan nasu, hannu ta mika zata ida dauko hijabin ta ji ya riko hannunta tareda juyo da ita, hannunsa ya sa a gefen wuyanta ya shafi kumfan da yake wajen ya nuno mata "yanxu wannan duk saurin kar in ganki ne haka" idanunsa ne ya sauka akan maclean da ke gefen bakinta wanda shima ya tabbata bata san da shi ba, murmushi yayi ya fara leaning, baya itama tayi tace "malam ya dai" daria ce ta so kupce masa "kaman ya kuwa malama, mutum da matarsa" bata ankara ba ta ji sun zube saman gadon yayinda ya mata rumfa da jikinsa, hannu ya sa ya goge toothpaste da ke gefen bakinta yayinda ya kurawa lips inta ido, zuciyartane ya fara bugawa da karfi sanin abunda zai biyo baya amma ga mamakinta sai taji bazata iya hanasa ba kamar ma itama so take (Khairatee an hau online🤣) hade lips insu yayi ya shiga kissing inta yayinda itama take maida martani, ganin towel na jikin Khairatee a fuskana ya sa ni barin dakin ba shiri, koh da na dawo gani nayi Khairatee an tashi ana tutturo baki an nufi toilet
Ganin Sadiq na biyota ya sata shigewa da wuri ta sa key, daria yayi yana cewa "wannan yarinya akwai gulman tsiya in an bibiya kinma fini so fa amma sai can a rinka wani hada rai, kuma akan meh bazamuyi wankar tare ba" ya fada yana ya buga kofar toilet in, batasan sanda murmushi ya kubce mata, sai da ta nutsu sannan tace "toilet in bazai dauke mu ba ka jira in na gama sai kayi" sai da ta ji motsin ya bar wajen ta wuce tayi wankarta cike da nishadi har ta manta da duk wani damuwa nata.
A hankali ta fito daga toilet in taga baya nan tana ida fitowa taji anyi sama da ita, kan gado ya direta yana "yarinya wa na kama" bata san lokacin da daria ya subuce mata ba, kura mata ido yayi yana kallonta yayinda yake jin wani abu a ransa, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sata kau da kanta tareda cewa "kaje kayi wankan kar ruwan yayi sanyi" towel inta ya riko yace "ai ke nake jira ki bani towel in" ganin dagaske yake ya sata cewa "na shiga uku ai akwai wani aciki" "ni na matata nake son using so either ki bani ko in cire" kada kai tayi tana mamakin wannan sabon halin nasa, kan ma ta nemo abunda zata sa kan ta bashi towel in taji ya yaye mata shi, cikin zaro ido ta juyo taga ya kafeta da sexy eyes inshi, cikin sauri ta jawo blanket na kan gadon ta rufe kanta da shi, yana daria ya nufi toilet in, itama sai da ta gama dariyarta ta fito daga cikin blanket in tana mamakin canzawarsa lokaci guda, he was neva dis caring or playful b4.
Shima ko da ya shige toilet mamakin kansa yake yanda ya canza gaba daya, culd it b dat he's in love or what. Da wayannan tunanin ya gama wankansa ya fito yaga har ta shirya ta kwanta. Shiryawa yayi shima yazo dab bayanta ya kwanta, jin yanda jikinta ke dan rawa ya tabbatar mai batayi bacci ba, murmushi yayi a zuciyarsa yace "matsoraciya kawai"
Ba a jima ba bacci ya dauketa ya tashi ya koma suna fuskantar juna, ya jima yana kallonta sannan ya tashi ya dauki wayarsa ya fice, Hajjo ya kira sai da yayi ringing sau biyu ta dauka, basu koh gaisa ba yace "Hajjo nace ba" kan ma ya ida ta katsesa "wato kai Ababakari ka gama rainani ko, ina ka kai mun 'ya? Dariya yayi yace "Hajjo wato yanxu ko ta kaina baki bi kinfi sonta a kaina ko, toh yarki na nan lafia mun danyi tafiane" dadi ta dan ji a ranta dan yanxu ta tabbatar jikan nata ya fara jin wani abu gameda matar nasa "toh ka tabbata ka dawo mun da ita gobe goben nan" daria yayi yace "kai Hajjo inda muka je da dan nisa fa ke dai sin kin gammu kawai, kin ma sa na manta dalilin kirarki da nayi, yawwa Hajjo dan Allah lokacin da kika fara son dan tsohon kakan nawa ta ya kika gane kina sonsa" salati Hajjo ta shiga yi "Iye Ababakari rashin kunyar taka ta kai haka, toh ba dani za a yi wannan hirar ba" daria sosai yayi yana cewa "Haba Hajjona in bnyi da ke ba da wa zanyi wannan hirar, ko dayake ma ai taku soyayyar da ce bazai zo daya da na yanxu ba" tabe baki tayi tace "wannan kuwa kai ka sani, kasan ta da ince ka kirani ka katse mun barci" ajiyar zucia yayi yana "hoho Hajjo da ni fa dan gatanki ne amma akan yarinyar nan gaba daya kin canza mun, yanxu toh ki mun gata daya ki turomun number wancan abun nasan a wajenta zan samu amsar da zai gamsar da ni" "ban gane wancan abun ba? Cewar Hajjo, dan tsaki yayi yace "Hajjo wancan abun da ta zauna a wajenki mana wanda ta koma gidansu kwanan nan, Zali ko meh take da suna" "Allah dai ya shiryeka Ababakari, Zalince kake cewa wancan abun, wulakanci dai bashida kyau kuma ban turowa" tana gama fadin hakan ta kashe wayarta, tsaki yayi ya nufi dakin, daidai bakin kofar text message ya shigo ya duba yaga Hajjo ce, murmushi yayi ya dada shigewa ya bari a kan cewa sai washe gari zai kirata.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now