babi na goma

3.1K 157 5
                                    

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

      *PRINCE SADIQ*

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

*Na Billy Ladan*

*21-22*

🎂🍾🎁🎊🎉🎂
_Alhamdulillah am a year older_
_Ya Allah, thank u. Thank u for another year of life that u gave to me, I’m so greatfull for all the things that u’ve been givin me. Thank u for my family who never fail to show some love & care to me. Thank u to all my friends, who never forget me & always understood me. Thank u for all the people who remembered me today by sending messages & good wishes via watsapp, sms, facebook & of course greeting me personally, i really appreciate u ol_
🎂🎉🎊🎁🍾🎂

Sanye take da towel fitowarta kenan daga wanka ta zauna a bakin gadon tana shafa mai, jawo ledan kayan da sukayi siyayya tayi ta fara dubawa dan sam jiya bata bi ta kansu ba, jera kayan kwalliyan tayi a gaban yar dressing mirror inta na sawanta kuma ta sasu cikin wardrobe na dakin, jawo sauran leda biyun tayi taga dayan kayan kwalamane ciki, ajesa tayi a gefe tareda duba ko meh dayan ya kunsa, kananun brezia ne a ciki sai pants da kayan shan iska sai kuma pad, wani kunya ne ya kamata, ita bata ma san yaushe ya siya mata su ba dan tare sukayi siyayyan, dago wani pink tayi tana kare mai kallo sannan ta aje gefe, pink pant ta dauka shima ta aje sannan ta tashi ta sa sauran a wardrobe, tana shirin kunce towel inta kenan taji an turo kofar tareda sallama, a kidime ta juyo tana kakkare jikinta ta ma kasa amsa sallamar tasa, da ido ta fara neman inda hijabinta yake ta hangosa can karshen dakin, runtse idonta tayi tareda cizan lips inta na kasa a zuciyarta tana cewa "shikenan yau zai kare mun kallo" dan already she can feel his eyes on her, takowa ya fara a hankali har ya karaso inda take, dago fuskarta yayi ya kurawa red lips inta ido, hannu yasa ya cire lips inta da ta danne da hakwaranta ya shiga shafawa a hankali, koh me ya tuna oho dan gani nayi ya janye hannunsa cikin sauri yayi waje, ajiyar zucia Khairatee tayi sannan ta shiga shiryawa da wuri gudun kar ya sake shigo mata.

Shigar english wear riga da skirt tayi sannan tayi parking gashinta ya zubo ta gefe sannan ta daura black veil a kanta, feshe jikinta tayi da turare sannan ta fito dan rabonta da palon tun jiya da suka dawo daga siyayya, abinci ma sai da Hajjo ta sa akai mata shi a daki.

Shi kadai ta samu zaune a falon ta nemi waje dan nesa da shi ta zauna, dago kansa yayi ya kalleta sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa dan cigaba da abunda yakeyi, bata jima da zama ba Zali ta fito itama ta caba kwalliya bakin nan ya sha mai kaman injin na tatan man gyada, kujerar da Sadiq ke kai ta zauna tareda gaishesa, batareda ya dago ba ya amsa mata, jansa ta shiga yi da hira wasu ya amsa wasu kuma yayi kamar bai ji ba. Khairatee da zaman ya isheta ta tashi dan komawa daki dan dama ita dan Hajjo ta fito ganin bata nan kuma baza ta zauna tayita kallon abunda ke kona mata rai ba, koh taku biyu bata yi taji yace "koma ki zauna" dagowa tayi taga haryanxu wayarsa yake kallo hakan ya sa ta cigaba da tafiyarta sai dai ko step daya bata ida ba ya sake cewa "bakiji ba kenan" dauke kanta tayi tareda cewa "abu zan dauko ne" ganin bai ce komai ba ya sata cigaba da tafiyarta, tana shiga dakinta ta nufi inda novels inta ke aje akan bed stand inta ta dauki favorite inta *The Australian na Babra Delinsky*, inda ta barsu nan ta samesu, mazauninta na da ta je ta zauna tareda bude novel in, da yake ta jima bata karanta shi ba ji tayi kamar yau ta fara karantashi, sosai takaddan ya tafi da hankalinta shi yasa sam bata ji shigowar Hajjo ba sai da taji tace "Khairi meh kika samu ne haka? Rufe takaddar tayi tareda cewa "sannu da fitowa Hajjo" cikin sakin fuska Hajjo ta amsa mata tana cewa "ke zanwa sannu ai Khairi amaryar daki, tun jiya kinki fitowa sai yanxu" murmushi tayi tareda sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, kallon Sadiq Hajjo tayi tareda cewa "Ababakari baka tafin ba? Jefa wayarsa yayi a aljihu yana cewa "aw korata ma kikeyi, infa na tafi bazaki sake ganina ba" tabe baki tayi tareda cewa "ai kuwa dolene ma kazo tunda yanxu akwai dalili" wayarta ne ya shiga kara ta jawo glass inta ta sa tana kallon mai kiran, kallon da ta ma Sadiq ya sa shi gane ummarsa ce ke kiran

Prince SadiqWhere stories live. Discover now