Babi Na Shida

2.9K 130 3
                                    

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

      *PRINCE SADIQ*

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

*Na Billy Ladan*

*13-14*

Kan ya kai ga aikata mugun nufinsa ya ji saukar kibiya a kafarsa, wani kara ya saka tareda ihun neman agaji a wajen dan uwan nasa sai dai shima kan ya karaso ya samu rabonsa a kafa shima ya shiga birjima akasa yana ihu, ga dukkan alamu kibiyar akwai dafi dan azabar da yake ji bai taba jin makamacinta ba tunda yazo dunia. Sai da Khairatee ta tabbatar duk ya samesu sannan ta fito daga wajen buyan nata, a hankali ta fara takowa tana zuwa wajen Sadiq, shi kuwa jin shirun ya sashi bude idonsa ya gansu zube a kasa, cikin zafin nama ya nufi inda wukar shehu yake ya zarota daga cikin gidanta ya juyo yana kallon khairatee da mask in fuskarta ya hanashi ganin fuskarta, ganin yana nufota da wukarsa mai sheki ya sa numfashinta daukewa dan duk a zatonta kasheta zaiyi, a hankali ta fara sulalelewa tayi kasa sumammiya

Baki bude ya bita da kallo a zuciyarsa yana cewa toh wannan bawan Allah mai ya sashi suma, karasawa yayi daidai inda ta fadi ya duba yaga lalle suma tayi, juyowa yayi dan yaje ya dauko ruwa yaga mugayen nan har sun samu damar tashi suna kokarin afka mai, nan ya shiga fada da su, yanayi yana godewa mahaifiyarsa da trainer insa dan yau yaga amfanin koyar fadan. Duk da sun samu sunyi mai rauni sai da ya yi galaba a kansu.

Da kyar ya iya jawo kafansa ya dawo inda khairatee ke kwance a sume haryanxu, hannunshi ya sa ya fara kokarin cire mask in dake fuskarta a zuciyarsa yana cewa "koh me ya fito da karamin yaro haka a cikin daren nan" bayan ya cire ya aje gefe sannan ya fara kokarin cire kayan da ke jikinta, wani abu kaman lemon tsami da ya taba hannunsa ya sa shi jin wani shock, saurin janye hannunsa yayi tareda ciro wayarsa daga aljihunsa, torch ya kunna sannan yabi fuskarta da kallo,hannunsa ya sa ya cire hular da ke kanta dan ya tabbatar da zarginsa, ganin gashin kanta mai tsawo ya gama fitar da surarta na mace, bin fuskarta yayi da kallo, karamin jan lips inta ya kurawa ido, ya yi kusan five seconds yana kare mata kallo, jawo bottle in ruwan yayi ya shafa mata a fuskarta, wani ajiyar zucia tayi sannan ta tashi a razane tana kalle kalle har idonta ya sauka akan kyakkyawar fuskar Sadiq, juyawa tayi ta kalli gawawakin da ke zube kanta ne taji yafara juyawa ganin yanda jini ke kwarara, baya tayi tayi luuu zata sake sumewa, rikota Sadiq yayi tareda jawota suna fuskantar juna, nunota yayi da yatsarsa yace "kika kara sume mun sai na mareki sannan in barki a duhun dajin nan, na tabbata kuma masu farautar rayuwan nawa basu kareba in sunxo sa sameki so ki nutsu, zaro gwalagwalan idanunta tayi ta gyada mai kai cikin tsoro, juyawa yayi ya fara tafiya jin bata biyosa ya sashi juyowa yana kallonta " sai sunzo sun sameki a can ko" jiki na rawa ta tashi ta dauki kayanta da suka tarwatse a wajen ta bi bayansa. Dardumarsu da kayan abincin ya tattare ya maida kan dokinsa, gawar Shehu ya daura a dayan dokin sannan ya ma Khairatee umarni ta hau nata dokin

Sai da suka fara tafia ya juyo yace "ina ne garinku? Cikin dar dar tace "daga kauyen shika nake kuma inaga na bata dan bansan nayi nisa haka ba, amma idan gari ya waye zan iya gane hanya"
"Toh zamuyi gaba kadan mu yada zango kafun safe muje kauyen naku" kanta kawai ta gyada mai sannan suka cigaba da tafia. Bayan wani dutse suka samu gefen wani rafi suka yada zango, dardumar ya shimfida musu suka zauna akai, ragowar abincin nasu ya miko mata, ta so kin karba amma kukar da cikinta yayi ya fallasa sirrin yunwar da take ji, hannu ta sa ta karba ta fara ci a hankali. Can karshen dardumar yaje ya kwanta tareda juya mata baya.

Tana gamawa ta wanke hannunta tareda yin hamdala, gashin kanta tayi parking sannan ta maida hularta ta kwanta itama can karshen dardumar tareda barin katon space tsakaninsu.

Minti biyar ya wuce amma bacci yaki daukarta sai juye juye take, Sadiq kuwa duk motsinta ya hanashi bacci, abun da ya ishesa ya tashi ya juyo cikin bacin rai yace "wai tsutsace ke da bazaki nutsu ki bacci ba sai juye juye kike ma mutane kin hanani bacci, meh ma ya fito da karamar yarinya irinki cikin wannan dare" ganin yanda ta wani zazzaro ido jiki na rawa ya sashi sake fuskanshi, ya lura duk a tsorace take, tausayintane ya kamashi, ko ba komai yau ta ceci rayuwarsa, da ba dun ita ba yau ya tabbata mutuwa zaiyi, cikin sanyin murya yace "ki daure kiyi bacci ki daina juye juye hakan zai hanani bacci,kinji ko? Kai kawai ta gyada tareda gyara kwanciyarta.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now