👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*PRINCE SADIQ*
👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑
*Na Billy Ladan*
*15-16*
_wannan shafin nakune yan group ina Billy Ladan Novels & Billy Ladan fans forum,Allah ya barni da ku dearies😘_
Hanya dayace da za a bi dan tserar da ita daga shiga wannan dajin kuma itace hanyar auratayya, idan har an samu wani da zai yadda ya aureta kafun zuwa dare toh dole mai gari ya hakura ya barta. Shiru Sadiq yayi na yan wasu dakikai sannan ya tashi ya nufi inda abban khairi da liman ke tsaye, hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro kudin da ke jikinsa ya kamo hannun Abba ya sa mai su a ciki tareda cewa "wannan sadakin yarka ce da kuma dokina daya dake waje, in har ka amince a shirye nake da a daura mana aure yanxun nan" kallon juna liman da abbanta sukayi sannan yace "liman sai muje masallaci ai a daura ko" gyada kai kawai yayi sannan suka fice suka nufi masallacin
Bayan kaman minti talatin Abban khairi suka shigo shida Sadiq, inda suka bar Nanna nan suka sameta, gyaran murya Abban khairi yayi tareda cewa "Nanna sai a shiryata ai dan yau zasu wuce nidai Allah ya ji kaina ya rabani da alakakai dan haka ta gaggauta barin mun gida" kai Nanna ta gyada cike da takaici sannan ta tashi ta nufi dakin Khairatee. Zama Sadiq yayi yana mamakin hali irin na abban Khairi tareda tunanin yanda zasuje su kare da ummarsa da maimartaba, wannan shine an gudu ba a tsira ba, yayi gudun auren Farhana gashi yazo ya kare da auren yar kauye wanda da ace yayi auren wuri da ya aje irinta, ajiyar zucia yayi yana hango bala'in da zaije ya tarar a gida, amma koma menene aikin gama ya gama dia was no way zai bar wanda ta cece rayuwarsa ta shiga wannan dajin da ake kira duhun daji, dole taci darajar ceton rayuwarsa da tayi. Fitowar abba ne ya katse mai tunani ya dubesa yace "wai basu fito da ita bane" Sadiq yi yayi kamar bai jisa ba dan haka kawai mutumin ke basa haushi, ace ka haifi yaro amma ka daura mai karan tsana, tur! da irin wayannan iyayen. Ganin Sadiq ba amsa mishi zaiyi ba yasa shi wucewa dakin, a zaune ya taddasu sunata lallashin Khairatee da ke ta kuka, cikin kuka tace "Nanna yanxu wannan mai kama da larabawan aka aura mun, gaskia ni bazan bishi ba gwara in shiga dajin, halan ma aljanine dan kyawunsa ya wuce misali, idan ba aljani bane shi baza a rasa wani mugun abu a tattare da shi ba, nidai ba inda zani na zabi shiga dajin nan dan in mutu kowa ya hutu" a harzuke ya karasa shiga dakin yana cewa "toh dan ubanki ko dan shan jini ne sai kin bisa, shegiya, tsinanniya, baki ma gode Allah ya ceci rayuwarki ba toh wlh kuyi maza ku gama shiryata dan bazata kara kwana mun gida ba, daga zuwanmu jiya har Muhsin ya fara zazzabi toh wlh duk maitarki da uwarki kinyi kadan, baku isa ku cinye mun yaro ba, shegiya mai bakar mugunta toh ta Allah ba taku ba, minti biyu na baku a fitar mun da wannan annobar daga gidana" yana gama fadin hakan ya juya ya fice yana wani huci.
Kukan Khairatee ne ya tsananta, tashi Ma tayi ta ciro mata wani kayanta wanda shine dan dama dama a cikin kayayyakin nata, rigace da skirt sai hijabin da ya shiga da shi, powder da man baki ta shafa manta sannan ta riko hannunta suka fice, har sun kai palo ta sake komowa daki da gudu, takaddunta masu debe mata kewa ta tattaro a hannunta sai dan kur'aninta, falo ta dawo ta zauna gefen Nanna haryanxu idanunta basu bar *Zubar Hawaye* ba, nasiha sosai Ma da Nanna suka mata sannan Ma tace ta tashi ta tafi, kasa tashi tayi har sai da Abbanta ya fito ya daka mata tsawa amma duk da hakan bata tashi ba sai ma kara kankame Ma da tayi, ganin Abbanta ya yo kanta ya sa Sadiq saurin tashi ya rigasa isa wajenta, hannayensa ya sa ya riko kafadarta tareda tayar da ita, a hankali ya fara janta suka nufi kofa, ganin dagaske tafia zaiyi da ita ya sata kara sautin kukan nata tana "wayyo abba ka tausayamun kar ka rabani da Ma, Nanna ki bashi hakuri ya barni in zauna da ku, Abba ka ji kaina bazan sake ba wallahi na tuba" wani uban tsawa ya daka mata tareda cewa "yau duk maitarki bazaki kwana mun a gida ba, sabida haka ki sawa zuciyarki hakuri ki bi mijinki"
Ma kasa zama tayi a wajen ta tashi ta wuce dakinta yayinda hawaye keta tsere a fuskarta, Nanna ma hawayen take ta kasa cewa komai, duk da tana tirje tirje sai da ya fita da ita daga gidan, suna fita ta durkushe a wajen tana kuka kamar ranta zai fita, tausayinta ne ya kama Sadiq ya durkuso ya rike kafadarta "Khairi" yanda ya kira sunan nata ya sata dagowa ta kallesa, dauke kansa yayi tareda cewa "nasan abunda kike tunani amma ki sani da inada niyyar cutar dake da ban kawoki garinku ba da tun a daji zan aikatar da duk abunda kike tunanin zan miki, bazan hanaki kuka ba dan abunda ya sameki ya ma cancanci a tayaki kuka, rabuwa da iyaye abune mai zafi barinma baki san inda zaki ba, inaso ki yarda dani, ban aureki dan wata manufa ta daban ba, na aurekine dan tserar da rayuwarki kuma na miki alkawari muddun komai ya lafa zan sauwake miki in dawo dake wajen iyayenki" dagowa ta sakeyi ta kallesa dan zancensa na karshe ya daki zuciyarta, shi sam bai ma lura da kallonsa da take ba ya cigaba da cewa "yanxu dole mu tafi, ko kinfi son shiga dajin ko kuma kinfi so kiyi ta zama ki cigaba da fuskantar tsana da tsangwama daga mahaifinki da yan kauyen naku dan a kwana daya har na gama fuskantar abunda yake faruwa" ya karashe yana kallonta, kai ta gyada mai alamar "a'a", dagata yayi yana kade mata jikinta sannan ya jata suka nufi inda dokin nasa yake, dan jakar nata da takuddun ya karba ya zuba a jakar da ke rataye jikin dokin sannan ya rike ya ce ta hau, ganin sai juye juye take ya sashi dagata cak ya daurata sannan shima ya haye, har zasu fara tafia ya hango Nanna ta fito daga cikin gidan, a hankali ta karaso wajensu, wata yar roba ta miko musu tace "ga wannan in kunji yunwa kuci, sannan kai kuma bawan Allah wannan yarinya da aka aura ma amana ce a wajenka idan ka ci amana Allah na nan zai kuma saka mata, ina hadaka da Allah da ka rike mana ita amana, ka mun alkawarin cewa zaka kula mana da ita, ka mun alkawarin cewa bazaka bari tayi maraicin mu ba, kai kawai ya gyada tareda cewa nayi alkawari Kaka, murmushi ta mai tareda riko hannun Khairatee "Allah ya kareku, ya kaiku inda zaku lafia, ki riki addu'a Khairatee dan ba abunda yafi hakan, sannan banso kiyi tunanin dawowa kauyen nan anan kusa, idan ko mai ya lafa na tabbata mijinki zai kawo mana ke" ta karashe tana kallon fuskar Sadiq, murmushi kawai ya mata, tana tsaye a wajen suka fara tafia har sai da ta daina ganinsu sannan ta shige gida.

YOU ARE READING
Prince Sadiq
Fiksi PenggemarUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...