Babi na biyar

2.8K 130 7
                                        

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

      *PRINCE SADIQ*

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

*Na Billy Ladan*

*10-12*

Sha biyu daidai Sadiq ya fito sanye da wasu kodaddun kaya na bayi, amintaccen bawansa Shehu da ke jiransa yana ganin fitowarsa ya karaso tareda cewa "ran Yarima Sadiq ya dade, komai a shirye yake kai kawai nake jira" ajiyar zucia yayi tareda cewa "ai sai muje koh" inda ya aje musu dokin suka nufa, sai da ya tabbatar Sadiq ya haye nasa sannan shima ya hau nasa, ta kofar baya suka fice suka bar fadar batareda kowa ya kallesu ba. Suna cikin tafia Shehu yaga Sadiq ya tsaya, saukowa yayi daga kan dokinsa yanufosa tareda tambayar ko lafia, shiru Sadiq yayi tareda bin inda suke da kallo, ajiyar zucia yayi sannan ya kalli Shehu yace "ji nake kamar ana biyomu ne" a take Shehu ya zaro wukar da ke jikinsa yace "ranka shi dade bara na dan duba, kai ka dakata a nan" dokinsa ya hau ya koma baya sai dai ba abunda ya gani, sam bai lura da muguyen kartin da aka aikosu dan kashe Sadiq ba, yana barin wurin suka fito daga inda suka rakube, harara babban ya watsawa dayan yana cewa "kai dakikin ina ne da kake cewa mu kashesa tun a nan, ko ka manta har yanxu a cikin masarautar muke, kai dai ka bi yanda nace kawai ko kuma kaima in badda kai, zabi ya rage naka" yana gams fadin haka ya ja dokinsa ya bi bayan su Prince Sadiq dan kar su bace musu, shima fito da dokinsa yayi yabi bayan ogan nasa.

👑👑👑👑

Wani azabebben ciwon kaine ya tadata wanda ba komai ya jawo mata hakan ba sai kusan kwana da tayi tana kuka, tashi tayi ta fada toilet ta yi wanka, light make up tayi sannan ta dauki wani english gown ta sa, tana shirin fita Ma ta turo kofar dakin, tsayawa tayi tana kallonta dan ba karamin kyau ta mata ba, gaisheta da khairatee tayi ya sata dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, karasa shigewa dakin tayi tareda zama gefenta, fuskarta ta shafa tareda murmushi "u luk beautiful Khairi" murrmushi itama tayi tareda cewa "tanx mum"sosai ta ji dadin compliment in duk da ta san bayan Ma da Nanna ba wanda ke ganin kyawunta, tashi Ma tayi tareda cewa "ki fito Shamawilu na jiranki a waje" take murmushin da ke fuskarta ya gushe, dan turo baki tayi tareda cewa "Ma ki ce mai bacci nake" harara ta watso mata tareda cewa "sabida na zamo yar aikenki ko, kin wuce koh sai na saba miki" tana yar guna guni ta fita

Zaune a kan dakalin da ke kofar gidansu ta hangosa, fuskar nan a murtuke ta karaso tareda mai sallama, kafeta yayi da ido yayinda ya kasa amsa sallamarta, tunani yake a zuciyarsa dama haka yarinyar nan takeda kyau, toh mesa take kulle kanta a shigar maza, ji yayi bazai iya aiwatar da abunda yazo yi ba, khairatee da ta gaji da tsayuwane ta yi gyaran murya tareda cewa "kaga malam idan baka da abunyi yi ni inada, ka taso ni kuma nazo ka kafeni da idanu sai kace yau ka fara ganina" murmushi yayi tareda cewa "Allah huci ran gimbiya, ai kamar yau na fara ganin kin dan ban san sirrin kyau gareki haka ba, Allah ne yasa zan ganki hakan dan kar in yiwa kaina asara" baki bude take kallonsa dan gani take ya ma raina mata hankali, gajeriyar dariya tayi sannan tace "kaga Shamawilu ni ba irin yan matan naka bane da zaka yaudara da dadin baki, wlh nafi karfin haka kuma nafi karfin wulakanci, kuma inaso in ja ma kunne daga yau kar ka sake tunkarar kofar gidanmu da sunan kazo wajena dan kamar yanda kake ikrarin baka sona nima ba sonka nake ba dan ko maza sun kare bazan aureka ba" daria yayi tareda cewa "ai kin makaro yarinya, wlh aurenki kamar nayi kuma ba mahalukin da ya isa ya hanani aurenki" cikin bacin rai ta juya tayi gida yayinda shamawilu ya bita da kallo yana "kanbu ashe fa yarinyar nan ta hade, amma na so na kwari kaina, wannan ai in ta dan kara shekaru ba karamar mace za a yi anan ba. Cike da wannan tunani ya bar kofar gidan nasu.

Tana Shiga ta tarar da Ma da Nanna a zaune Ma na sharar kwalla, karasawa tayi ta dafa kafadar Ma tana tambayarta koh lafia, murmushi ta mata tareda cewa "ba komai Ummul Khairi, ki tashi kije ciki akwai kaya na aje miki akan katifarki ki sa ki zo kitchen ki tayani shirya table" tana gama fadin haka ta tashi ta wuce kicin. Kallon Nanna Khairatee tayi alamar tambaya, murmushi Nanna ta mata tareda cewa "kiyi yanda ummarki tace kawai Khairatee" cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi dakinta, wani sabon English gown ta gani da wani yar mayafi da ya shiga dashi, na jikinta ta cire ta zura sabo da Ma ta aje mata, gashinta mai shegen tsawo ta gyara tareda barking sannan tayi daurin channel O da gyalen ta fito sai kamshi take, daga Ma har Nanna zuba mata ido sukayi wanda har ya sa taji kunya, karasawa tayi ta tayasu gama shirya dining in sannan suka dawo parlor. Suna jin tsayuwar mota Ma ta tashi ta sako hijabinta sannan ta dubi Khairatee tace "duk abunda zaki gani bani so kice komai kuma bnda rashin kunya duk da nasan ba halinki bane, ki tashi kije ki taya su Abbanki shigo da kaya" ba karamin sanyi jikinta yayi ba jin kalaman Ma gashi kuma taga hawaye kwance a idonta, tabbas akwai wani abun a kasa. Cikin sanyin jiki ta tashi ta fice, a hankali ta fara takowa zuwa inda motar yake, numfashinta ne ya kusa daukewa ganin abbanta rungume da wata mata a cikin motar, daskarewa tayi ta kasa koda daga kafarta daga inda take, tana tsaye a wajen Abbanta ya fito bai ko damu ya kalleta ba ya zagaya daya gefen ya bude wa matar nan kofa ta fito hannunta rike da yaro da bazai wuce 2 years ba, hannunsu makale da na juna har suka karaso inda take, muryarta na rawa ta karbi jakar da ke hannunsa tareda musu sannu da zuwa, murna fal rubuce fuskarsa ya amsa sannan ya dubi matar da suke tare yace "my love meet my first daughter Ummul Khairi n u Khairatee meet ur step mum n step bro Muhsin" murmushi kawai matar ta mata sannan suka wuce suka barta tsaye a wajen. Minti kusan biyar ta dauka maganganun abban nata na yawo a kanta, da kyar ta ja kafarta ta shige inda har sun zazzauna a kan table suna cin abinci. Aje jakar tayi ta zo ta ja kujera itama ta zauna. Ma ce ta fito daga kitchen ta fara serving insu, tashi khairatee tayi dan tayata amma ta mata alama da ido akan ta zauna. Sai da ta gama serving in kowa sannan ta ja kujerarta ta zauna, in ka dauke abbanta da matarsa bawanda ke walwala cikinsu dan kowa da abunde ke yawo a kwakwalwarsa, minti minti Khairatee ke dagowa taga yanda Abbanta ke tarairayar matarsa da dan nasu ba ko kunya, wani kishi da tsanarsu ne ya dirar mata dan tunda take bata taba tuna lokacin da abbanta ya nuna mata irin wannan so ba amma gashi har abinci yake bawa Muhsin a baki, wani gajiyar tsaki taja tareda aje spoon da ke hannunta ta fara kokarin tashi, Ma ce ta mata ido alamar ta koma ta zauna, kallon side na abbanta tayi dan ganin koh ya lura da abunda ya faru taga shi sam hankalinsa ma ba a gunsu yake ba, cike da bakin ciki ta cigaba da jujjuya abincin dan ita gaba daya ya fita ranta. Muryar amaryar abban nata taji tace "honey what do we have for desert? Murmushi yayi tareda cewa "kar ki damu my luv nasan Ma wil surprise u, i told u my wife is born to cook so dnt worry" ya karashe yana daria, wasu hawayene suka taru a idon Khairatee yayinda take jin wani tausayin ummar nata na ratsata, tashi Ma tayi batareda ta karasa cin abincin nata ba ta nufi kitchen. Bayan kaman five minutes Khairatee ta bi bayanta, Ma na jin motsinta tayi saurin share hawayenta, cike da damuwa ta karaso gun Ma, kallo daya tayi mata ta gane kuka take, rungumeta tayi ta hau kuka a hankali, shafa kanta Ma ta shiga yi har sai da taji ta bar kukan, cikin dasashiyar murya Khairatee tace "Ma pls ki daukeni mu gudu, he dsnt deserve u, bai cancanci ki masa duk hidimar da kike mai ba, pls lets leave" dago fuskarta Ma tayi tana share mata hawayenta, murmushi ta sake mata tareda cewa "Khairatee har yanxu ke yarinyace bazaki taba ganewa ba, do u tink i dnt want to liv him, av tot of dat many times since wen u wia so little but i couldn't,I chuz to stay with him for ol d tins he has done right and not to live him for d small tins he has done wrong
I chuz to stay bcs i understand why tins had to happen dis way, I understand his reason for causing me pain, he may hav bn hurtn our feelings but ur father is a good man"

Idanu cike da hawaye Khairatee ke kallonta, janye jikinta tayi daga na ummanta tareda cewa "bazan taba ganewa ba, n if u aint living i wil liv wtout u" riko hannunta Ma tayi tana hawaye sannan tace "Khairatee pls dnt do dat, dis is marriage we r talking about, aure ya gaji hakan, wataran a ji dadi wataran kuma kishiyar hakan, amma hakan ba yana nufin zamar ya kare ba, u sit and try to understand ur differences and make tins ryt, soon kema zaki tsinci kanki a gidan miji,den u wil understand my reasons" share hawayenta tayi tareda karban chocolate cake da ke hannun Ma tayi waje da shi. Yayyankawa tayi ta sawa kowa a karamar plate ta aje mai, taje aje na dad inta Muhsin da ke cinyarsa ya rinka wurgo mata hannu, lokaci daya taji yaron ya shiga ranta hannu tasa tana kokarin dagasa taji abbanta ya rikesa gam, batareda ya kalleta ba yace "barshi tukun ban gama feeding insa ba" cikin sanyin jiki ta koma ta zauna ta fara cin cake nata a hankali, kamar daga sama taji muryar abban nata na cewa "Yaron nan Shamawilu zasu kawo sadakin yarinyar nan sai ku shirya" kai kawai Ma ta gyada, da karfi Khairatee ta buga fork da ke hannunta akan plate dake gabanta wanda ya sa kowa dagowa, hawayen da take ta dannewa suka fara zarya a kumatunta, bata san lokacinda ta budi baki ta fara magana ba "was hating me not enuf, do u have to humiliate me by forcing someone to marry me" rike hannunta Ma tayi alamar tayi shiru amma ina sai ma fincike hannunta da tayi ta cigaba "wani irin tsana kake mun haka abba, meh na ma da ka tsaneni haka, ace sadaki na sai kaine zaka biya dan kawai ka gaji da kallona a cikin gidanka, u culd have just told me to liv n save me d humiliation, but i just want u to knw bazan taba yadda da wannan auren ba, i wil never marry him" cike da bacin rai abbanta yace "yes u will"
"I wont" ta fada cikin daga murya, saukar marine ta samu daga gun Ma da itama take hawayen, rike da kuncinta ta juya ta bar falon tayi dakinta ta kulle. Rigar jikinta ta cire tana hawaye ta maida asalin shigar ta da take na maza. Almakashi ta dauko ta zauna gaban mirror, tattaro gashinta tayi da niyyar askewa, ko me ta tuna sai naga ta ajiye, safar fuskarta da take sawa ta rufe fuskarta dashi sannan ta dauki kwari da bakarta, ta windown dakinta ta fice ta haura kan dokinta, duk da garin ya fara duhu bataji tsoron shigewa dajin ba.

👑👑👑👑👑

Tafia sosai sukayi amma basuga alamun mutane ba, ganin garin ya fara duhu ya sa Sadiq cewa su dan tsaya su huta, daure dawakansu sukayi sannan suka yada zango. Abincin da suka taho da shi suka zauna suna ci suna yar hirarsu. Basu ankara ba kawai sukaga kartin mutane su biyu a kansu, cikin zafin nama Shehu ya nufi inda wukarsa yake amma kan ya karasa dayan ya fille masa wuya sai ga kansa a kasa, runtse idanunsa Sadiq yayi yana ta karanto addu'o'i a ransa, shahada ya shiga yi dan yau kam ya san tasa ta kare
Cikin zafin nama wannan bakin mugun ya daga wukar sama ya...........................


Billy Ladan🖊

Prince SadiqWhere stories live. Discover now