Babi na Sha biyu

3.3K 139 2
                                    

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO 🦅*

*25-26*

*Wanna shafin na baki shi kyauta Feedohm dear, u r such an amazing person, bazan taba gajia da gode miki ba, tnk u so much for d amazing birthday story da kikayi musamman dan tayani murnar zagayowar ranar haihuwata, i so much appreciate, Allah ya kara daukakaki dear*
*Rabbi ya jibanci lamuranki*
*Allah ya karo baseera da zakin hannu*
❤😘

_Wato yau sai da na gama typing ya goge, kuka ne kawai banyi ba wlh😭, da kyar na lallaba na sake muku wannan_

Tun kan ya iso yake jin hucin zuwar kibiyar, ya tattara dukkan hankalinsa ya mika shi zuwa inda yake jiyo karar,  hannunsa ya daga yana jiran zuwarta, caraf kake ji ya riko kibiyar da hannunsa sannan ya dago ya kalli inda ta fito, duk da darene hakan bai hanashi hango wannan bakin mugun ba da ke zaune kan bishiya, kan kace meh duk wajen ya hargitse an fara gudun ceton rai, tashi Sadiq yayi dan yau koma wanene wannan mugun toh sai yaga bayansa bayan yaji ko waye ya aikosa, sai dai tun kan ya karasa Mahmoud da ke biye da shi ya sa hannu ya karbi kwari a hannun bayin da ke tsaye tareda karbar kibiyar da ke hannun Sadiq sai gashi jikin wannan mugun ya fadi kasa mataccce, cikin bacin rai Sadiq ya karasa inda gawar yake ya dan sunkuya tareda cire kibiyar nan, cikin abinda bai wuce second biyar ba jikin wannan mugun yayi wani irin bushewa ya dawo bakikirin, cire kibiyar yayi sannan yayi hannu wa bayin alamar suzo, suna karasowa yace "dayanku yayi maza ya taho mun da Mallam Aminu yanxun nan sauran kuma ku dauki gawar nan kuje ku jirani da shi a bakin ofishinsa, cikin zafin nama suka shiga aiwatar da umarnin  da aka basu, ko da ya dago baiga Mahmoud tsaye ba, karasawa yayi inda su Hajjo ke tsaye tsoro karara a fuskarsu, dafata yayi tareda cewa "Zali rike hannun umma da Hajjo kuyi ciki dan tsayuwarku anan da hatsari dan ba mamaki masu farautar rayuwan nawa basu kare ba" kai kawai ta gyada mai dan itama a ruden take, rike hannunsu tayi ta shiga jansu suka bar wajen, sai sannan ya juyo ya nufi Farhana da tun faruwan abun take zaune a inda ya barta tana ta kuka kamar ranta zai fita, zama yayi a gefenta tareda jawota jikinsa ya shiga rarrashinta dan sosai ta basa tausayi, ko ba komai tana sonsa, sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya tayar da ita ya sa bayinta su rakata ciki.

Cike da fargabar abunda zai tarar ya nufi ofishin mal Aminu wanda yake matsayin Dr a masarautar, bude ya samj ofishin wanda hakan ya tabbatar mai da cewa mal Aminu ya iso, yana shiga ya sallami kowa sannan ya rufi kofar ya isa gun mal Aminu da ke tsaye gefen gawar, gaisawa sukayi sannan Mal Aminu ya ja kujera ya zauna dan bazai iya tsayuwar ba sabida shekaru sun kawo mai, gyaran murya Sadiq yayi tareda cewa "Baba Aminu meh zaka iya cewa gameda wannan gawar? Shiru yayi na yan wasu dakikai sannan yace " wato Yarima a gaskia abunda zai sa mutum yayi irin wannan canzawar cikin kankanin lokaci ba karamin abu bane, gubar da akayi amfani da ita meh karfice kuma ko ma waye ya aikosa baya sonka a raye dan kaga yanda ya sauyashi" kada kai yayi tareda sa hannu a aljihunsa ya ciro kibiyar ya mikawa mal Aminu yace "Baba Aminu da wannan kibiyar aka so kasheni, ina so ka dubata da kyau ko zaki iya samo wani abu jikinta" glass insa ya ja ya sa ya shiga jujjuya kibiyar, wani mark da ya gani ya sa yanayin fuskarsa canzawa, Sadiq da ke lura da yanayinsa ya matso yana cewa "Baba Aminu wani abun ka samo" kujera ya nuna mai alamar ya zauna dan maganar ba ta tsaye bace, ba musu ya jawo kujerar ya zauna, tura mai kibiyar yayi zuwa gabansa yace "duba kasar kibiyar nan ka gaya mun meh ka gani" dagawa yayi ya shiga dubawa sai dai bai ga komai ba sai wani tambarin tsuntsu, dagowa yayi yace "tambarice ta tsuntsu Baba Aminu" murmushi yayi tareda cewa "wannan tambari da kake gani itace tambarin wannan masarautar a zamanin kakanka sarki Jibril, kuma wannan kibiya da kake gani tasa ce, bana taba mantawa wani zamani da zashi yaki ya sa aka kera masa ita, ko ina zaka je bazaka taba samun irinta ba dan shi kadai ya mallaketa, bayan rasuwarsa wannan kibiya ta shiga gado aka rabasa tsakanin mahaifinka da wansa, mutane biyu kawai ke da ikon mallakar wannan kibiyar, iyalan wan mahaifinka wato Haj Maryama da d'an' uwanka Mahmoud sai kuma kai da iyayenka" ba karamin sanyi jikin Sadiq yayi ba jin wannan bayanai na mal Aminu, dan dama already yanada suspect sai kuma gashi ya mai confirming, sai yanxu yake gane dalilin saurin Mahmoud wajen kashe wannan mugun dan tabbas ya san da ya rayu toh dole ya tona asirinsu, ajiyar zucia yayi sannan ya dago yace "Baba Aminu kasan iyayena bazasu taba salwantar da rayuwana ba sabida haka zargin yanxu akan mutum biyu yake, inaso wannan magana ya zamto sirri tsakanina da kai koh mai martaba bana so ya sani, ni nasan yanda zan bullowa al'amarin, yanxu zan wuce ciki sai gobe idan Allah ya kaimu zan sake juyowa, nagode sosai Baba Aminu, Allah ya kara lafia da tsawon rai" ya karashe tareda rungumar dan tsohon, "bakomai yarima, Allah dai ya dada tsarewa" mal Aminu ya mayar mai, "amin baba Aminu, mu kwana lafia" yana gama fadin hakan ya fice yayinda baba Aminu ya bisa da ido

Prince SadiqWhere stories live. Discover now