Babi na Shahudu

4K 149 3
                                    

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*31-32*

_I want to use dis medium to tank ol dos who congratulated, celebrated with me tru calls,messages and been dia with me during my induction/oath taking into the noble profession of nursing, i tank u ol, especially members ina na Billy Ladan novels and Billy Ladan fans forum i say a big tank u to u ol, Allah ya barmu tare_

Zaune ya samu Farhana a parlor tana kallo, kallo daya tayi masa ta dauke kai ta cigaba da kallonta, shima bai bi ta kanta ba yayi wucewarsa daki yana mamakin halin nata.
Yana kokarin shiga toilet ta shigo dakin, gabansa ta sha ta tare kofar toilet in tana wani kada jiki, cike da masifa ta dubesa ta ce "wlh Prince abunda kake mun a gidannan ya fara isata, wannan wani irin bakin haline, ka sa kafa ka fice a gidannan kusan kwana biyu batareda ka ko gayamun koh meh ba sannan ka dawo koh sannu bara ka cemun ba,toh wallahi gaskia ni nagaji, kuma wallahi sai ka gayamun daga inda kake" wani banzan kallo ya mata tareda cewa "daga inda kika aikeni nake, mara kunya kawai" Gaisheta yayi ta amsa mai sannan tace "wato dan ta gaya ma gaskia shine sai ka kamata kayi ta jibga koh, ai tana da hakkin sanin inda kaje kuma ba ita kadai ba harni nan ka tada mun hankali kuma na fahimci hakan na son ya zame ma jiki, komai fa zai iya faruwa Sadiq, ba wai ana fatan hakan ba, kamata yayi duk inda zaka ka sanar da mu musamman ma ita ko dan samun kwanciyar hankalinmu amma bawai ka sa kafa ka fice haka kawai ba ka dawo kuma daga tambayar ba'asi ka hau kanta da duka" batareda ya dago ba yace "kuyi hakuri umma ban so saku cikin yanayi na tashin hankali ba kuma insha Allah gaba zan kiyaye, kuma batun cewa na daketa marinta kawai nayi umma kuma itama tasan meh tayi har nayi hakan wanda na tabbata bata fada miki ba" caraf Farhana ta karbe tace "wlh umma ni ba abunda na mai kawai daga tambayarsa ya hau jibgata" ajiyar zuciya umma tayi tareda cewa "toh ya isa, koma menene dai banson makamancin hakan ya sake faruwa, duk sanda wani tafiyar ya tashi sai ka sanar damu, kai kuma Sadiq na sha gayama karage wannan zafin naka, dukan mace ba abu bane mai kyau balle kuma a fuska, addini ya koyar da dabarun horar mace in tayi laifi wanda na tabbata ka san dasu so ka kiyaye" kansa ya kada tareda cewa "za a kiyaye insha Allah, amma umma itama ki ja mata kunne dan sam bata girmamani ko sa'a nake da ita albarka, shigowana koh sannu da zuwa ban samu ba balle a bani wani tarba na musamman sai ma tsareni da rashin kunyar tata da tayi" shiru Hajja Zinatu tayi dan ita kanta yanxu ta san dan nata baiyi dacen mata ba dan akwai lokacin da taje side nasu tajiyo hayaniyarsu, yanda Farha ke yabawa Sadiq magana ya sata juyawa batareda ta shige ba, kallon Farhana tayi tareda cewa "toh Farhana kema sai ki kiyaye, ki bi mijinki sau da kafa, ki girmamasa, kina amfani da kyawawan lafuza cike da ladabi wajen yin magana da shi dan samun zaman lafia da zama mai daurewa a tsakaninku, kinji ko 'yata" kai kawai ta daga, sake hadasu tayi ta musu fada sosai sannan ta dubi Sadiq tace "koh zamu iya jin inda kaje yanzu" murmushi yayi tareda cewa "Salsar naje, su Hajjo ma na gaisheku" murmushi tayi tareda cewa "ai hakan na da kyau amma nan gaba sai kana fada, kuma ai da kaje da ita Farhanan itama ta samu ladan ziyara" "wani zuwan naje da ita umma" ya mayar mata "toh Allah ya nuna mana, ku tashi kuje" a tare suka tashi suka fice, ko ta kanta bai bi ya wuce fada dan zuwa gaida mai martaba.

~~~~~~~~~~~

Zaune take a dakinta duk tunani ya bi ya isheta, tashi tayi ta nufi wardrobe inta dan ciro wayar da Sadiq ya bar mata, idonta ne ya sauka kan ledar da ya aje rannan, kamar bazata dubaba ta sa hannu ta jawosa taga takaddu ne ciki, bakin gadonta ta koma ta zauna tareda zazzage content in cikin ledar, murmushi ta sake ganin novels ne masu yawa, bazasu tayi dan ta zabi na karanta wa yau, wani small card ta hango tsakiyar takaddun ta dago tareda karanta abunda ke ciki _"l knw i wunt always b dia for u but i hope dis kip u company"_ murmushi tayi tareda rungume papern a kirjinta, atleast he cares about her tunda har yasan da cewa tana son karanta novels, wayarta ta ja ta kunna ta shiga contacts, number biyu kawai ta gani daya ansa Nani daya kuma ba ayi saving ba, cike da murnanta tayi dialing na Nani, sunyi kusan hour daya suna hira dasu ummartata sannan sukayi sallama. Cike da jin dadin hirar tasu da su ummarta ta yi dialing dayar numbar sai dai har sau biyu tana kira ba a daga ba, har kamar bazata sake kira ba amma kuma zuciyarta na son jin ko ya isa lafia dan haka ta sake dialing, Farhana da karar buzzing in wayar ya isheta dan tana vibration ne ta tashi ta shiga neman wayar, har ta kusa katsewa ta daga kallon wayar tayi dan bata san Sadiq da shi ba sannan ta kalli sunar jikin wayar *BB* tabe baki tayi tareda picking "Hello wayene? Khairatee saurin katse wayar tayi jin muryan Farhana, ko ba a fada ba tasan matarsa ce, bata ankara ba taji hawaye na bin kuncinta.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now