sha shida

3.6K 137 3
                                    

*PRINCE SADIQ*

*Na Billy Ladan*

*37*

_Wannan Shafin naku ne Manyan Mata, Mata masu Fasaha,Karamci, da kuma Hangen Nesa,ko ina na leka ku nake gani😍, ko ina na leka hirarku ake,ina bala'in ji da ku ina kuma alfahari da ku my_ *ASSO* wato *IDON MIKIYA WRITER'S*🦅
_Allah ya kara daukakaku_
*Ana tare*
*Ana manne*
*Ana like*🤝😄

*Song: Let Me Love You by glee cast*

_Baby u should let me love u_
_let me be the one to give u everything u want and need_
_Baby good love and protection, make me ur selection, show the way love is suppose to be_
_Let me love you......._

Wakar da ke tashi cikin motar kenan yayin da Sadiq ke ta zuba uban gudu kamar zasu tashi sama, kallon Khairatee yayi ta gefen ido yaga sai wani cin magani take, kara volume yayi ya shiga bin wakar a hankali yayinda from tym to tym yake satan kallon Khairatee da ta maida hankalinta a kan hanya, sake kawar da kanta tayi ta runtsesu yayinda take sauraron wakar a bakin Sadiq dan sai taji ya ma fisu dadin murya, a haka bacci mai dadi yayi awon gaba da ita.

A hankali ta bude idonta ta fara bin inda take da ido, zumbur ta mike ta fara bin dakin da kallo, idonta ta murza dan tabbatar da abunda take gani, shin dagaske a dakinta na Shika suke, duk da yan canji da dakin ya samu bazata taba manta da room inta ba, juyowan da zatayi taga Sadiq zaune kan sallaya ya kafeta da kallon nasa da yake mata kamar zai cinyeta, sauko da kafafunta tayi tareda maida kallonta kasa, gyarar murya tayi tace "ina muke? Tashi yayi ya nade sallayar ya aje sannan ya dubeta yace "am sure kin san inda muka zo but if u r still doubting sai ki fito ki gani" shiru tayi for some seconds sannan ta ce "did u put me to bed?" Jin bai amsa ba yasata dagowa taga ita yake kallo, gira ya daga mata alamar eh, take idanunta ya kawo ruwa, ajiyar zucia yayi a ransa yace "toh queen of tears ta fara" gefenta ya zo ya zauna yace "yanxu kuma meh aka miki da zaki hau kukan,wai ni y do u enjoy crying ne, is it dat its ur hobby or what" kawar da kanta tayi tana mai zumburo yar karamin red lips inta, cikin yanayi na shagwaba tace "akan meh baka tasheni na shigo da kaina ba zaka wani daukoni sai kace wata jaririya, kila ma yan kauyen nan duk sun gama ganina suna can sunata zagina n d worst is maybe a gaban su Nanna ma ka daukeni" ta karashe tana kuka a hankali, sosai ta basa daria amma ya gimtse yace "toh dan na daukoki kina bacci laifine balle ki tsaya kina kuka dan an ganki, matatace ke fa" sake turo baki tayi tace "ai akwai kunya koh, yanxu ni duk kasa bazan iya fita bama duk da son ganinsu da nake" daria ya shiga yi a hankali ta dago tana kallonsa, wani kyau ya mata ganinsa a hakan, zata iya cewa dis  d first tym ta gansa haka n he luks so handsome wen he laughs, bata san ta saki baki tana kallonsa ba sai da yayi waving hannunsa a gaban fuskarta sannan ta dawo daga duniyar da ta tafi, cikin jin kunya ta kawar da kanta tareda tashi dan zuwa ta dauro alwala, riko hannunta yayi ta juyo amma bata yadda sun hada ido ba, dago fuskarta yayi yace "BB yanxu akan na daukoki shine kike ta wani bata rai wai ke gaki na saki kunya koh, toh inaga in kinyi cikifa?" dago kansa yayi alamar tunani yace "gashi zakiyi kyau da ciki kuwa irin mai fitowa sosai innan yana gaba kina biyosa a baya lokacin sai in kawoki gida wajen su Nanna inga karshen kunya tunda kowa zai san meh kikayi kika kunso cikin" yana gama fadin hakan ya juya yana cewa "yi sallah ki fito" ko da ya fita lekota yayi yana daria ganin yanda ta kasa shiga toilet in ta zube wajen tana kuka, sai da ta gaji dan kanta ta tashi ta shige toilet ta yi wanka tareda dauro alwala.
Light kaya ta sa sannan ta daura hijabi a kai ta fito, tun daga corridor take jiyo hirar Sadiq da Ma, yanda suke hira zakace sun jima da sanin juna ne, ita dai a kullum kara bata mamaki yake yanda yake wani abun kamar mai multiple personality or sumone who is bipolar
Cikin jin kunya ta zo ta zauna gefen Ma tareda kwanciya a jikinta ta shiga kuka a hankali, shafa kanta Ma tayi tace "toh kuma meh na kuka Khairina" tashi tayi tana goge hawayenta taga Sadiq sai harara yake watso mata, itama hararar ta mai ta juyo ga Ma tareda riko hannunta tace "Ma nayi kewarku sosai, hop kina lafia ba abunda yake damunki, ina Nanna i miss her too, kuma ina fatan ba mai takura mun ku cos zanyi fada da duk wanda ya tabamun ku" daria Ma tayi tace "oh Khairina duk wannan uban tambayan" shafa fuskarta tayi tareda cewa "muna nan lau Ummul Khairi, Nanna kuwa tana dakinta ki tashi kuje ku gaidata" a tare suka tashi tana gaba yana biye da ita, sai da suka kusa shiga dakin ya riko hannunta tareda juyo da ita, dagowa tayi suka hada ido ta sake mai harara, hancinta ya kama yaja tareda cewa "ki cigiba da hararata sai na cire wannan huge eyes in naki, kuma kika sake kika mana kuka in mun shiga toh sai na baki abunda zai saki kuka truout d nyt" kwace hannunta tayi tareda bude kofar ta shige.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now