*PRINCE SADIQ*
*Na Billy Ladan*
*35-36*
Yana kokarin shiga motarsa ya ga taya biyu sunyi paci, buga tayar yayi da kafarsa yana tsaki, gashi sauran keys in motocin gidan na gun Hajja Zinatu yasan kuma warhaka tayi bacci, cike da takaici ya komo daki ya kwanta, ya jima idonsa biyu sannan bacci ya daukesa. Kirar Sallar farko ya tashi ya shige toilet yayi wanka sannan ya dauro alwala. Shiryawa yayi cikin shigar jamfa sannan ya shiga tada Farhana, ganin in ya tsaya zata bata mai lokaci ya jawo wayarta ya sa alarm sannan ya sa daidai kunnenta ya fice.
Sashin Hajja Zinatu ya nufa, fitowarta daga alwala kenan ta gansa zaune kan kujera, cike da mamaki tace "a'a Sadiq lafia na ganka da sanyin asuban nan kuma cikin shiri?" saukowa yayi daga kan kujerar ya gaidata ta amsa mai sannan ta tsaresa da ido dan son jin ko lafia, sosa keyarsa yayi sannan yace "umma wlh dama wani project nake a Salsar, so jiya aka kirani da suna bukatar inje shine nake so da nayi Sallah inje in wuce dan inaso na dawo da wuri dan bazan kwana ba" "wani aiki kenan haka Sadiq, kuma ai ka jira gari ya dan waye ko, kaga sai ku tafi ma da iyalin naka"
"Masallaci da islamia nake ginawa a can anguwar bigira dan naga suna da bukatar hakan, abunda yasa bazanje da ita Farhana ba kuma dan a yau zan juyo, da kyar ma in karasa cikin salsar in" shiru Hajja Zinatu tayi sannan tace "toh shikenan, Allah ya kiyaye hanya" "amin" ya amsa mata sannan ya nufi inda keys yake ya dauki daya ya fice, ajiyar zucia ya sauke da ya fito yana mai godia wa Allah da bata hadasa da Farhana ba, ya daiyi karyar bazai isa Salsar ba alhalin inda zasa kenan dan aikinsa na bigira koh tunanin farata ma baiyi ba amma yana gab da farata dan ya ma samu wanda zai bawa contract in aikin. Sai da ya tsaya masallaci yayi sallah sannan ya dauki hanyar Salsar.Tunda ta tashi da asuba bata sake komawa ba, bayan tayi tilawa ta karanta azkar inta ta tashi ta nufi kitchen ta hada musu breakfast, wajen seven ta gama komai ta juye a flask sannan ta koma dakinta tayi wanka ta shirya cikin dogon riga sannan ta dauko babban mayafi ta yafa ta fito parlor. Ganin har takwas Hajjo bata fito ba ya sata tashi dan zuwa dubata, bata ida fita a parlorn ba tajiyo muryarta tana waya hakan ya sa ta dawo ta zauna ta jirata har ta shigo, gaisheta tayi tareda cewa "ai Hajjo har na tashi zani dubaki sai na jiyo muryarki" murmushi tayi tareda cewa "ke dai 'yan nan bari kawai wani program mai dadi na samu ban san har lokaci ya tafi haka ba sai da naji cikina ta fara kukan yunwa" daria Khairi tayi tace "toh bari na kawo mana abinci Hajjo" eating mat ta dauko ta shimfida musu a palon sannan ta dauko flasks na abincin, yam balls in ta zuba musu a plate daya sannan ta ja cups biyu ta zuba musu kunun madaran da tayi suka fara ci, suna cikin karyawa Mahmoud ya shigo da sallamarsa, a tare suka amsa mai ya karaso ya zauna a dan gefe da su tareda gaida Hajjo, cikin sakin fuska ta amsa mai sannan Khairi ma ta gaishesa tareda tambayarsa abunda zata zuba mai, hannu ya daga mata yace "barshi matarmu zan ma zuba da kaina" jawo flask in yayi shima ya zuba abunda suke ci, sosai ya ci abincin dan ba karamin dadi ya mai ba, kallon Hajjo yayi yace "Hajjo wa yayi abincin nan? Dariya tayi tareda nuno Khairatee, cike da mamaki yace "gaskia matarmu na baki A1 ai dole Sadiq ya boyeki a nan, gaskia am impressed, ur mum brought u up well" "sosai fa" cewar Hajjo "ai ni ranar da zan ganta sai na jinjina mata dan gaskia tayi kokari sosai, ba kowace yarinya bane zaka samu da wannan kwazon at her age, sam batada kiwuyan aiki"
A haka suna yar hirarsu har suka gama karyawa Khairatee ta tattara kayan ta kai kitchen ta dawo, kallon Mahmoud tayi tace "Ya Mahmoud alkawarinmu" daria yayi tareda cewa "matarmu ashe baki manta ba" "ina fa zan manta" ta mayar mai, tashi yayi tareda cewa "toh bara naje in kimtsa sai in zo mu wuce koh" kai kawai ta gyada mai. Bai jima da fita ba ya dawo cikin kananan kaya suka ma Hajjo Sallama sannan suka fice.Fitarsu da kaman 30 minutes sai ga Sadiq ya shigo ba ko sallama ya wuce dakin Khairi, binsa Hajjo tayi da ido tana tabe baki, gani tayi ya fito yazo ya zauna tareda cire wayarsa ya shiga dialing wata number ganin baya shiga ya sashi jan wani tsaki tareda aje wayar, dagowa yayi ya kalli Hajjo yace "Hajjo ina kwana? tabe baki tayi tareda cewa "aww ca nake baka ganni ba ai tunda har ka iya zuwa wuceni ba ko sallama balle ka gaidani" kawar da kansa gefe yayi tareda yin tsaki mara sauti sannan yace "Hajjo ban ganki bane" bawai ta yarda ba tace "in ma baka ganni ba sallamar fa" "kayya Hajjo nafayi sallama sai dai in kece bakiji ba, ni ba ta wannan ma nake ba, ina kishiyar taki" tabe baki tayi tareda cewa "sai da kaga bata nan shine zaka san da ni,toh ban san inda take ba"
YOU ARE READING
Prince Sadiq
FanficUmmul Khairi (Khairatee) yarinyace da take fuskantar tsantsar tsana da tsangwama daga mahaifinta da yan kauyensu saboda ta kasance baka kuma mummuna wanda hakan yasa suke gani ita annobace, tsautsayi ya hada ta da Yarima Sadiq wanda ya kaiga aure ts...