Babi Na Tara

3.1K 185 3
                                    

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

      *PRINCE SADIQ*

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

*Na Billy Ladan*

*19-20*

_Wannan shafin nakine sister HumyLuv ke da members inki na Matan Arewa, Mata masu Mutunci da Karamci, a gaskiya naji dadin hira daku,Allah ya kara daukakaku, ina yinki tawan irin sosai innan_

12 daidai suka sauka garin *Salsar* bakin wani babban gida yayi horn aka bude mai ya kutsa kai ya shiga, bin wajen ta shiga yi da ido, yanayin gininsu kamar na masarautarsu Sadiq, parking yayi ya sauko ya bude boot ya ciro yar jakar tata ya nufi ciki, ganin bata sauko ba ya shi cewa "inzo in sauko dake ko" a hankali ta bude motar ta bi bayansa suka shiga ratsa bayin da ke ta hidima, duk inda suka ketara sai an mai gaisuwa ta ban girma wanda hakan ya nuna wata masarautar suka zo, badai bauta ya kawota ba khairatee ta fada cikin ranta. Tafia mai dan nisa sukayi har suka iso bakin wani daki, sallama yayi tareda dage labulen ya shige, tsohuwar dake zaune falon ta dago tareda amsa sallamar, tana yin tozali da fuskar Sadiq ta saki wani murmushi tana cewa "Ababakari kaine tafe, maraba maraba da mijin da yaki matarsa" daria yayi yana sosa keya tareda cewa "kai Hajjo yaushene rabona da nan in" harara ta bishi da shi sannan tace "bar ganin na tsufa ina sane da komai, yau shekara daya kenan cur rabonka da Salsar" daga kai yayi alamar tunani sannan ya juyo yace "haka fa lalle yar tsohuwar nan kwakwalwarki na ja, bata buga ba tukun" pillow da ke gefenta ta dauka ta wurga mai ya kauce yana dariya, harara ta mai tana cewa "jimin yaro toh sai taka ta buga kan nawa ya buga" saukowa yayi suka shiga gaisawa tareda tambayarsa mutanen gida, dagowa yayi ya kalli kofar ya hango inuwarta jikin labulen, tsaki yayi a zuciyansa yana cewa "wato ita yarinyar nan in bata sani magana ba bata jin dadi" gyaran murya yayi sannan yace "in bazaki shigo ba sai ki koma kin wani tsaya wa mutane cirko cirko a bakin kofa sai kace wanda ta hadiyi tabarya, na fahimci ke komai sai an gaya miki toh bazance ki shigo ba in kinga dama ki shekara a gun" a hankali ta dago labulen tana sallama, amsa mata Hajjo tayi yayinda take kallon Sadiq "amma Ababakari anyi ja'irin yaro, yanxu dama da bakuwa kake sai ka barta awaje, karaso yan mata" cikin sanyin Jiki khairatee ta karasa ta zauna tareda gaida Hajjo, fuska a sake ta amsa mata sannan ta juyo ga Sadiq tace "Ababakari ina ka samu yarinya karama haka ince dai ba wani abun bane ya faru" mikewa yayi a kan 3 seater da yake zaune a kai tareda lumshe ido sannan yace "kishiyarki ce Hajjo" murmushine ya bayyana a fuskarta riko hannun Khairatee tayi tana cewa "ah lale maraba da kishiyata, amma gaskia Marwanu bai kyauta ba, ace ayi auren dan gaban goshin nawa banda labari, kuma ai ya bari yarinyar ta kara girma ko dan naga yarinyace sosai" tabe baki yayi tareda cewa "Hajjo ke kam akwai iya bata suna meh kuma wani Marwanu, Marwan ake cewa, ni kuma ba Ababakari bane Ababakar ake cewa, in shima in zai baki wahala toh ki ce Sadiq, kuma da kike cewa yarinyar tayi karama ina ku kuka tasani da surutun inyi aure yanxu nayi kuma za a dauko wani abun surutun daban, gaskia tsoffin nan ba a iya muku" tsaki tayi tareda cewa "Kai dai baka da kunya toh Ababakari zanyi ta cewa ba Saduk ba" tashi yayi zaune yana cewa "kayya! Hajjo mu tsaya a Ababakarin kawai meh kuma wani Saduk dan Allah" tabe baki tayi tareda cewa "kai ka sani"
Gyaran murya yayi yace "Hajjo ba kowane a gidan naki yazo ya shigar da ita dan akwai maganar da nakeso muyi" gyaran murya tayi ta shiga kwalawa Zaliha kira, amsa mata tayi daga dakin da takw tareda fitowa, da bayan Sadiq ta fara tozali wanda ya sata komawa daki da gudu, gaban mirror ta nufa ta shafa powder da lip balm cikin hanzari sannan ta feshe jikinta da turare, gyalen da ke jikinta ta yasar akan gado ta fice tana wani taku daidai kamar wanda ke tsoron taka kasa, da sallamarta ta shigo falon suna hada ido da Sadiq ta sake mai wani murmushi tareda cewa "lah Ya Sadiq sannu da zuwa yaushe ka shigo" maimakon ya amsa mata yace "ai tunda yanxu kike ganina kenan yanxun nazo" bata damu da kwatsatan da yayi ta juya tayo kitchen tana cewa bari in kawo ma abun sha, kallon Khairatee yayi da tun zuwarsu kanta ke kasa tana was da fingers inta sam bata ma damu da halin ko in kula da Zaliha ta y mata ba

Prince SadiqWhere stories live. Discover now