Babi Na Takwas

3K 187 5
                                        

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

      *PRINCE SADIQ*

👑🤴🏼🤴🏼🤴🏼👑

*Na Billy Ladan*

*17-18*

Wani irin kallo Hajja zinatu ta bisa da shi sannan tace "Sadiq hankalinka daya kuwa, ka san meh kake fada kuwa, da alama wannan ciwon da ke kannaka ya tabama kwakwalwa" wani irin bata rai yayi tareda cewa "hankalina daya umma kuma kamar yanda na fada matatace kuma babu inda zata" salati ta fara tana tafa hannu sannan ta sake kallon Khairatee da ke ta rarraba idanu tace "Sadiq wannan mai zubin aljanun kake kira matarka, hala dai gamo kayi da aljanu suka hadaka da ita, toh wlh koh sarkin aljanuce ke sai kin sake mun dana, dan ubanki zuki fice daga nan" ta karashe tana nuna mata hanya, kokarin janye hannayenta ta shiga yi yayinda hawaye ya gama wanke mata fuska, sake damke hannayen nata Sadiq yayi  ganin hakan ya sa Hajja Zinatu karasowa ciki ta shiga kokarin raba hannayen nasu amma ko kusa ta kasa, kamo gashin khairatee tayi ta shiga janta tana "wlh sai kin sake mun dana dan yafi karfinku" ji tayi Sadiq ya riko hannun nata, dagawo tayi cike da mamaki tana kallonsa, gani tayi idonsa yayi ja yanayin fuskarsa ya nuna ransa a bace yake, cikin sanyin jiki ta sake mata gashin, kujera taje ta zauna ta shiga sharo kwalla, "yanxu Sadiq akan wannan aljanar har zaka daga mun hannu, wayyoni Zinatu na shiga uku sun shanye mun d'a dan na tabbata ba a hayyacinka kake ba, dan da hankalinka nasan bazaka auri wannan mummunar ba"  ba tareda ya dago ko ya kalleta ba yace "umma a hayyacina nake kuma da sanina na aureta, mutum ce ita sabida haka kar ki sake aibata mun mata, ace d'an da kika haifa ya bace na yan kwanaki kuma ya dawo da rauni amma ki nuna halin ko in kula, sumtimes i wonder if kece kika haifeni, anya ba tsintata kika yi ko kuma dai a gidan marayu kika daukoni, dan duk uwar da zata kalli danta a halin da na dawo masarautar nan toh baza ta zamto cikin kwanciyar hankali ba amma ni tawa uwar bata damu ba sai ma wani damuwar ta daban da ta daurawa kanta" takowa tayi tana zuwa gabansa ta daga hannayenta ta sharara mai mari tareda nunosa da yatsa "na sha gaya ma ka daina mun magana kamar wanda ya samu sa'arshi, duk son da nake ma duk damuwa da dawainiya da nake a kanka har zaka dubeni kace anya ni na haifeka, ni uwarka Sadiq kake fadawa hakan, nayi rainon cikinka for gud nine months na sha kashinka da fitsarinka amma kullum kuntata mun kake, duk abunda kaga ina yi dan kai nakeyi kuma son da nake ma ya sa hakan, ban san yaushe zaka fahimci son da nake ma ba, watakil sai ranar da ka wayi gari kaga babu ni a dunia by then it wil b too late"

Kawar da kansa yayi yace "Umma u dnt luv any1 but urself kuma ol u care abt is d damn throne, shine kadai abunda yake gabanki, baki kaunata koh abbana, u dnt even knw d first tin abt luv, u knw notin, in haka ake nunawa da so toh da yara dayawa sun tagayyara dan ni yanda nakeji da ni da maraya bamu da maraba" kukane ya kufce wa Hajja Zinatu ta yi sauri ta fice daga dakin, zama yayi a bakin gadon tareda dafe kansa da hannayensa, a hankali khairatee ta tako ta zauna a gabansa, haryanxu hawaye bai daina fita a idanunta ba, dagowa yayi ya kalleta da jajayen idanunsa, tabe baki yayi yace "wai da wanne zanji ne, yanxu meh aka miki da zaki tasani a gaba kina kuka" ai kaman ya ce ta kara dan kuka mai sauti ta sake, tsaki yayi tareda dagata ya zaunar da ita a gefensa, shi dai bai iya rarrashi ba ga shi ya tsani kuka dan ba karamin daga mai hankali yake ba balle nata da yake jinsa har cikin ransa ya kuma kasa gane dalilin hakan, cikin muryarsa mai sanyi yace "ya isa haka, dan naga ke kukan bata miki wuya ko dadinsa kike ji oho" share hawayenta ta shiga yi sannan ta dago ta kallesa "kaje ka bawa ummarka hakuri" kallonta ya tsaya yi sannan yace "akan meh zan bata hakuri? "kuka fa take da ta bar nan kuma kai ka sanyata kukan, sam baka kyauta ba, mahaifiyarka ce fa, kalaman da kayi amfani dasu wajen mata magana sam bai dace ba, kuma kar ka manta aljannarka tana karkashin kafarta, sai ta daga ma zaka shige, kana tunanin yanda kake mu'amala da ita zaka samu rahamar ubangiji, shawarace nake baka bawai umarni ba dan ban kai ba, kayi kokarin gyara mu'amalarka da mahaifiyarka, duk yanda ta kai ga musguna maka mahaifiyarka ce kuma dole sai kana hakuri da ita, sabida haka nake baka shawaran kaje gareta ka bata hakuri koh ka kwana da fushin ubangiji" tashi yayi bai ce da ita komai ba ya fice.

Prince SadiqWhere stories live. Discover now