01

5.3K 318 5
                                    


*KANO..... Farawa layout*

A hankali gate man ya nufo gate din Don jin horn din megidansa, cikin hanzari ya karaso don ya tabbatar Uban gidansa ne, bude gate din yayi inda Barr. Nasir ya danno motarsa ciki, gate man din da shekarunsa zasu Kai wajen hamsin ya dinga daga masa hannu, tare da fadin

Barka da isowa ranka ya dade

Murmushi kawai Barrister yayi wanda Yafi Kama da na dole Don iyakarsa lebensa, yayi parking motarsa kusa da wata black Benz, ya Dan jima cikin motar kafin ya bude motar ya fito, dogo ne a wajen tsayi baya da kiba can kuma ba a rame yake ba, fatar jikinsa Fara ce tas gata fresh wadda zai tabbatar maka Hutu ya hadu da gayu, fuskarsa doguwa ce me matsakaitan halitta, saje ne me kyau Wanda ya hadu da gyara yasa barrister kamar wani dan 20s amma a zahiri he's 35years. Briefcase dinsa ya dauka hade da Leda ya nufi inda kofar da zata kaika parlon gidan yake, Hannunsa yasa ya murda kofar take ta bude tare da bayyana katon parlour wanda yasha gyara ga haddadun sofas peach da fari masu tsananin kyau, ko ina neat se kamshi dake tashi. Cikin zuciyarsa yace

Latifa badai tsafta ba

Bakinsa dauke da sallama ya shigo Yana maida kofar ya rufe babu Wanda ya amsa kasancewar a cikiciki yayi kuma ma babu kowa cikin parlon, se lokacin ya fara jiyo hayaniyar yaran daga play room dinsu, cikin nitsuwa ya nufi staircase ba tareda ya nemi kowa ba, nanma komai neat yake kamar ka yadda abinci kaci, parlon baki da fari ne na setters haddadu suma, bai tsaya parlon ba ya nufi dakinshi da yasha gyara. Kayansa ya cire ya nufi toilet don watsa ruwa.

Latifa tana cikin toilet taji bude gate hakan ya tabbatar mata barrister is home, wani farin ciki ya mamaye zuciyarta, dukda sanin halin barrister da tayi amma hakan bai hanata jin dadin dawowarsa ba haba two weeks baya gida yaje wani presentation akwa Ibom. A gagauce ta fito Daga toilet ta Fara goge jikinta sannan tayi shafe shafenta, tasan barrister ya hayo sama yanzu, Tana da tabbacin ko zata Kai isha'i bata fito ba bazai neme ta ba, hakan yasa ta gaggauta shirinta cikin A-shaped gown ta jar shadda da taji aiki, dauri tayi cikin kwarewa sannan ta feshe jikinta da turarruka, tayi kyau sosae kamar ka saceta. Latifa average height gareta kuma she's chubby, skin color dinta dark ne amma kuma tana da kyau me sanyi wanda kullum ka zauna da ita Seka sake ganinshi, mutum ce me tsafta, tarairaya da iya girki amma Batayi sa'ar miji ba Don Nasir Nada baudadden Hali.

Dakinshi ta Fara shiga har lokancin yana toilet bai fito ba, kayan da ya cire ta jefa cikin laundry bin sannan ta sauka kasa, play room dinsu taje taga duka basu nan hakan yasa ta nufi bedroom dinsu suna xaune su uku da plate din cake a gabansu, Tana shigowa duka suka sakar mata murmushi, Amal tace

Momma kizo Kici cake din kema

Kallonsu tayi tace

A'a kuci, daddynku ya dawo kun ganshi?

Gaba daya murmushin dake fuskarsu ya dauke hakan na damun latifa yara kwatakwata basu Saba da mahaifinsu ba,

Nana ce ta girgixa Kai tace

Muna play room mukaji yayi parking amma bamu fito ba.

Take latifa ta hade rai

Saboda me? Ba nace Kuna jin horn din motarsa kuje ku taro shi ba? Ba kwajin magana ta ko?

Dukkansu shiru sukai har Mimi wadda ba wani gane Abinda Momman Tasu Ke fadi ba, ta dai ga yan uwanta sunyi shiru hakan yasa itama tayi shiru ta daina cin cake din.

Ba zaku tashi kuje ku mishi sannu da zuwa ba? Se na daddake ku

Dukansu suka Mike kowanne bakinsa a gaba kamar zasu bige ginin, Seda taji hawansu sama sannan ta dafe kanta, itakam ya zatayi da halayen barrister duk wata hanya da take ganin is simple kuma zata bi Don shawo kansa amma Abu yaki, ganin zaman bazai kaita ko ina ba yasa ta nufi kitchen, karamar Yarinya da shekarunta bazasu Gaza goma Sha hudu ba ta iske tana jera plates Kan dish rack, kallonta tayi tace

Fa'iza taya ni Kai kayan nan sama

Tohm Anty

Tare suka Kai kayan abincin sama, su Amal na Zaune har lokancin barrister bai fito ba, Seda ta gama sannan ta sallami Fa'iza ta koma saman. Tana zama aka fara kiran sallar maghrib daidai fitowar barrister,

Daddy sannu da zuwa, ya hanya?

Lapiya lau little babies, Naje massallaci

Bai jira abinda zasu fada ba ya sauka kasa, suma sallar sukai sannan Amal da Nana suka dakko quranai suka Fara tilawa, Seda aka Yi sallar ishai sannan barrister ya shigo, cikin parlour ya xauna yana daukar remote sanin abinda zaiyi yasa Nana fadin

Daddy please Ka bar mana yanzu Za'a Fara Dora the explorer fa,

Ko kallonta baiyi ba, Mimi kuka ta Fara yi daidai shigowar latifa wadda ta sake gyara fuskarta se kamshi take, kallonsu tayi taga duk sunyi kicinkicin da rai tasan akan kallo ne hakan yasa tace

Amal kuje downstairs ku kalla cartoon din nan daddy network news zai kalla.

Gaba daya mikewa sukai yayinda ta dawo kusa dashi fuskarta fal murmushi tace

Honey ya hanya? I missed you sosae

Dan kallonta yayi yace

Alhamdulillah, gani na dawo ai

Dan yake tayi tace

Kace kayi missing dina mana

Ta fada a shagwabe, dukda tayi affecting dinsa amma se yace

Latifa ki kyaleni please, this is not the right time

Fuskarta Cikeda embarrassments tace

Haba barrister me yasa kake haka? At least mu family dinka ne idan baka sakar mana fuska ba wa zaka yiwa, ka dawo Daga tafiya ka zauna damu kaji yadda muke lokacinda baka nan Amma se ya zama problem kullum TV da newspaper ne abokanka? Haba barrister

Tunda ta Fara magana yake kallonta har ta gama, memokan yace wani abu se yace

Ki bani abinci idan kin gama complain din, Tunda Ke Bakyason ganin zuciyarki ta huta.

Idonta taf da hawaye ta Fara serving dinsa, inda sabo yaci ace latifa ta Saba da halayen Nasir amma kamar da wahala.

*'YAN DUTSE*

Wash! Wash! Wash Allah na ku kiramin innata mutuwa zanyi

Wannan ya kasance furucin Lubabatu Kwana biu da suka wuce, yau Kwananta uku tana labor amma mirsisi uwar mijinta taki yadda akai ta Asibiti, da an kawo zancen se ta hau sababi

Babu me kaita gurin wayancan mutanen da basu ganin kimar manya, haihuwata Sha uku baki daya tala unguzoma Ke karba, se ita raguwa Za'a ce se taje Asibiti to baa gidannan ba.

Wannan ya zama kamar common saying na Baba, fur taki yadda akai yar mutane Asibiti wai bazaa yarda alada ba. Shima Sani baya gida da yake driver ne na manyan mota da take zuwa can Lagos da sauran gurare. Duk wanda ake tunanin Baba zata ji magamarsa a banza taki yarda, gashi ita iyayenta baa gari suke ba.

Cikin hukuncin Allah Matar me gari ta samu labari, tayi fada kamar ta ari Baki Seda me girma kamar yadda take kiranshi yazo sannan ta sanar dashi halin da ake ciki

Kwana biu tana nakuda a gida?

Wallahi me girma, nima dazu asabe Ke fada min.

To zaman me kikeyi ki tashi muje Tunda ishaq yazo ya mika mu Asibiti.

Tare suka fito, inda ishaq babban Dan me gari dake aure a gumel yaxo kuma yana da mota, a kofar gidan me gari ya tsaya ita kuma ta shiga, lokacin da kyar Lubabatu ke numfashi, yarinyar da Dakyar idan tayi shekarun Sha biyar a duniya, Ta fita hayyacinta ta galabaita, shi kanshi dakin da take babu ventilation se zufa take daga ita har unguzomar wadda ta tsufa tukuf, kana kallon scenario din kasan zalunci ne da jahilci.

Matar me gari Bata jira hansai dake ta ihun ina Za'a kaita, Ta rirriko ta zuwa mota, kamar mataciyya haka Lubabatu take, da gudu hansai ta biyo su tana fadin

Tunda kin nuna min isa akan Abinda yake nawa, Luba ko ta haihu kar ta dawo gidannan.

Babu Wanda ya kulata se Jan motar da ishaq yayi zuciyarsa fal tausayin Luba bashi kadai ba hatta me gari abin ya taba zuciyar sa.

Shatuuu

GIDAJEN MU Where stories live. Discover now