Kwana goma kenan da komawar Luba gasakole, fadar Irin tashin hnkli da iyayenta suke ciki bata Lokaci ne, babu Wanda bai zubda hawaye ba, sede Tunda Taxo gidan babu wani sako Daga 'yan dutse, mahaifinta duk ya damu Yana ganin ya cuci marainiyar Yarinya gashi outcome din Auren wuri da yayi mata to amma shima ba laifinsa bane mahaifiyarsa ta tursasa akan se ya aurar da ita.A bangaren Luba dukda halin da take ciki amma damuwar ta ta ragu sosae on 1-10 scale 3 ya ragu saboda bata fita ko ina Innarta kullum tana kwantar mata da hankali tare da supporting dinta. A haka wata kanwar mahaifinta Anty balaraba dake aure a Jahun cikin jihar jigawa Taxo ta ga halin da ake ciki, cike da damuwa bayan sun kebe da Malam Mamuda tace
Mamuda yanxu Abinda ya samu Luba kenan
Shima da damuwa yace
Gata nan mijin ya dawo Mana da ita babu wata magana daga bangarensa
Tagumi tayi tace
To wanne hunkumci ka yanke?
Ni kaina bansani ba, amma me kike gani? Shiyasa Tun farko naki aurennan amma Baba magajiya ta daka tsalle akan se anyi yanxu waye cikin matsala?
Mamuda idan ana tuna baya rai baci zai nayi, wannan ya wuce yanxu mu maida hankalinmu akan yadda Zamu nema mata lapiya
Kanshi yayi nodding yace
Ina jinki
Kasan ina raba Kati a asibitin Jahun, to anan akwai mata da yawa masu matsala Irin tata ana kiranta yoyon fitsari, komai kyauta ake yiwa masu cutar kuma cikin hukuncin Allah suna warkewa Sede suna dadewa a asibiti.
Anty balaraba ta fada, Cikeda murna ya sanar da Inna da Baba magajiya wadda abin duniya ya isheta tunda gani take duk ita taja komai. Babu bata Lokaci suka nufi Jahun bangaren MSF da yake organisation ne na turawa suka zo don tallafawa mata akan ireiren matsalolin ciki, haihuwa da goyon yaro.
Cikin examination room likitan wanda yake tsaye dogo ne me chocolate skin colour, fuskarsa oval ce Cikeda kasimba, Daga gefensa wata matsakaiciyar mace ce cikin fararen kaya wanda zai tabbatar maka nurse ce, Amma kuma midwife ce, hannunta rikeda tray tace da Luba da shigowar ta kenan tace
Kece Marar lapiyar?
Eh nice
Luba ta fada Tana kwanciya saman examination bed da likitan yaa nuna mata, gloves suka saka a hannunsu da face mask, matar ta bude mata kafafunta tare da lankwasar dasu sannan ta mikawa likitan wani karfe, zura Mata yayi Yana ta fada akan Yarinya karama ace anyi mata aure, itakam midwife din ce masa tayi
Zaka gaji indai akan Wannan case din zaka bata ranka, laifin ai na iyayensu wannan karamar yarinyar da batafi js2 ba ace wai tayi aure ai jahilci ne
Luba tana kuka saboda zafi haka aka cusa karfen Don aga yadda Ciwon yake, wani katon syringe midwife din ta mika masa Cikeda ruwa ,amsa yayi Yana durawa cikin jikinta har Seda ya kare sannan suka matsa, midwife din tace Yi numfashi ai kuwa Sega wannan ruwan ya fara fitowa, zarowa sukai suna magana cikin medical jagons dinsu da Luba bata fahimci komai ba, rubuce rubuce sukai kafin suka ce taje waje.
Likitan ne ya fito Yana duban inda su Malam Mamuda suke hannunsa rike da file dinta yace
Ku jira yanxu xaa Bata gado,
Daga haka ya wuce, suna nan Zaune wata nurse tazo ta tafi da ita aka bata gado sannan ta saka mata robar fitsari.
Malam Mamuda da iyalansa suna xaune gaban nurse din dake dakin da aka kwantar da Luba, Tana musu bayani akan matsalar da luba ta samu
Ku kwantar da hankalinku, yarinyar ku ba Itace mutum ta farko da ta samu matsala Irin wannan ba, Duk wadda kuka gani cikin dakin nan itama Irin wannan matsalar gareta ta yoyon fitsari wadda muke kira vesico vaginal fistula, cuta ce da ta dade kuma har yanxu take nan saboda mutanenmu sunki su daina yiwa kanan yara aure, ko kuma Kin Zuwa Asibiti a haihu shi ne makasudun hakan......
Seda suka gane abinda take nufi sannan ta sanar dasu aiki xaayiwa Luba Don rufe wannan kofar dake zubda fitsarin.
Ringing din wayarta taji hakan yasa ta Mike Ba tareda ta damu da goge hawayen da yake bin kuncinta ba, ita barrister ya mara? Mari se ta lumshe idonta Don har lokancin taki daena jin zugin da gurin keyi mata, wayar ta dauka ganin sunan Mama Nafi yasa ta daidaita muryarta sannan ta dauka , suna gaisawa Mama tace
Latifa lapiya kike kuwa? Naji kamar kuka kike
Kanta ta girgixa cikin karfin Hali Tace
A'a Mama kaina ne yake yimin ciwo se zazzabi
Assha, sannu kinji, Bari na aiko Haidar ya karbi kayan su Amal Kema ki huta, Asiya tace suna gidanta a dakko su daga can.
Latifa taji dadi tace
Eh daxu suka tafi, To Mama Bari na hada kafin yazo
Sallama sukai ta dakko trolley ta hada musu duk abinda tasan zasu bukata sannan ta shiga bayi ta Fara sabon wanka, tana fitowa ta shirya cikin mint green Abaya, hijabi ta zura Don Haidar yace yana kofar gida.
Barrister Tunda latifa ta fita ya kasa ko kwakwaran motsi, se hannun hagunsa yake kallo wanda dashi ne yayi Marin, gaba daya haushin kansa yake ji, Donme zai mare ta saboda tayi maka masifa zuciyarshi ta bashi amsa, tsaki yayi don yasan bai kyauta ba kwatakwata ko sau daya, mikewa yayi ya zura farar jallabiya ya dauki system din ya dawo parlour Don yin aikinshi. Yana nan Zaune Yana aiki ya Mike Yaje ya bude wata kofa da zata hadaka da balcony gidan, gurin yayi kyau wasu thatched woven kujeru ne guda hudu se glass table a tsakiya, bai zauna ba se ya kama silver handle din da ya kawata balcony ya rike Yana kallon roofing din gidajen unguwar da kuma yadda motoci ke Dan wucewa. Kamar ance ya kalli kasa sega Fa'iza janye da katon trolley bayanta Latifa ce Sanye da katon hijabi waya kare a kunnenta, wata Irin muguwar faduwar gaba yaji Kada Latifa tayi yaji fa, har ya bude baki se kuma yace Bari yaga gudun ruwanta, Yana tsaye yaga ta gaisa da Baba megadi sannan ta bude gate ta fita, baya ganin abinda yake faruwa hakan yasa ya rasa yadda zaiyi, wajen Mintina goma se gata ta shigo sannan ta nufo cikin gidan. Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke Yana godewa Allah, parlour ya dawo ya zauna Yana bin system da takaddun dake zube ido, janyowa yayi Yana dudduba su, shiru shiru baiji Latifa ta hayo ba har aka Kira sallar laasar, sauka yayi yaje masjid sannan ya dawo bayan an Idar.
Bayan sallar ishai yana nan Zaune a parlour da lemu gabanshi wanda tun dazu shi yake ta kwankwada saboda yau ma ko breakfast baiyi ba kuma har lokancin baiga Latifa ba. Kallon agogo yayi dake manne jikin bangon parlour Tara Harda 'yan Mintina, tsaki yayi jin wani sound na fitowa daga cikinsa alamun yunwa yake ji, wayarsa ya janyo ya fara kiran Latifa Amma har ta katse bata dauka ba, sake Kira yayi for the second time amma shima shiru, mikewa yayi ya nufi bedroom dinta, har ya manta Yaushe ne last ya shigo dakin nan, komai neat se kamshi dake tashi, amma bata ciki Dayan ma haka, sauka kasa yayi don duba parlonta na kasa ga mamakinsa wutar a kashe take, kunnawa yayi yaga babu kowa, girgixa Kai yayi ya nufi kitchen, babu alamar anyi girki a gidan komai a wanke yake cooker babu komai, hakan ya dada haifar masa da faduwar gaba saboda yunwa yake ji sosae. Can idonshi ya hango plate an rufe da foil paper, janyowa yayi Yana budewa yaga Red meat ne anyi grilling anyi garnishing sosae yayi kyau a ido Balle kuma idan ya shiga baka take barrister ya fara salivating, fork ya janyo har ya caka yaji an riqe fork din, ko baa fada ba yasan Latifa ce saboda ga wannan yatsun nata da suka sha lalle sunyi kyau, bin yatsun yayi har zuwa fuskarta, wadda babu murmushi ko daya, idonta sun Dan kumbura wanda ya tabbatar masa kuka take har yanxu. janye plate din tayi ta fice daga kitchen din batareda ta furta komai ba, haishinsa take ji ko da wasa bata taba tunanin Nasir zai iya marinta ba Koda kudi aka bashi se gashi yayi a sadaka.
Shiru yayi saboda yadda Latifa ta bashi mamaki, Yana nan Zaune kusan na 5 minutes sannan ya hango samosa janyowa yayi har yasa hannu se ya samu kanshi da kulle kitchen Don Kada ta dawo, seda yaci kusan Tara sannan ya maida ya fito ya nufi dakinsa Don kwanciya dama yunwa ce tasa yake nemanta to he's full yanxu.
Shatuuu ♥️
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️