15

1.4K 167 1
                                    


Gefen A'isha Muhammad ya zauna tareda kamo hannunta yace

Baby what's it?

Hannunta tasa ta rungume shi, tare da sake sakin wani kukan shikam gabaki daya he's confused kukan me takeyi ne? Shidai ya barta tana ta walwala yanxu kuma tana kuka kamar wadda Ke da bipolar disorder, bai sake fadin komai ba se patting bayanta da yake da hannunsa, a hankali kukan nata ya fara raguwa se kuma ta ware hannayenta daga jikinsa ta nufi sink din dake dining space ta wanko fuskarta sannan ta dawo cikin parlour, kallonta yayi yace

Baby yunwa nake ji, muje ki bani abinci

Bata son magana Don gani take da zarar ta bude Baki zata sake breaking, hakan yasa kawai ta mike shi kuma yabi bayanta, ita abincin ma kadan take ci shi ne dai ya ware cikinsa Yana kwasar lazi Saboda da gaske yunwar yake ji, ya lura da yadda take cin abincin, hakan yasa Yana cinye nashi ya janyo Nata wanda yasa ta dago idonta Wanda suka fara haske Daga jan da sukai ta aje cikin nashi, wani reaction ne yayi taking place, wasu Irin molecules ne suke fitowa daga idanun Muhammad suke shiga na A'isha, enjoying kallon suke har Seda wayan Muhammad dake cikin parlour tayi ringing hakan ya katse musu abinda suke, janyota jikinshi yayi gaba dayansu suke sauke numfashi saboda yadda wani sudden feelings ya mamaye su, basu so daina kallon kallon da suke ba, it was an intense, lovely gaze ya karanci abubuwa da yawa cikin wannan hazel eyes din nata, itama anata bangaren hakan take, what will life be without Muhammad by her side? Useless and worthless haka take ji, Muhammad is her other and better half, ita kanta batasan iya dimbin son da take masa ba, Allah kadai yasan hakan. Wayar ce ta sake katse musu tunani wanda yasa Muhammad Jan tsaki tare da sake rungume beloved dinsa kamar wani zai kwace ta haka yake ji.

Lemme bring your phone, ana kiranka

A'isha ta fada tana cire hannayenta daga jikinsa, shima zare nashi yayi jikinsa Duk ya mutu kamar Wanda aka daka, jikin screen din ta kalla Big Sister taga ansa hakan ya fadar mata da gaba Don tasan Anty Mariya ce, Mika masa wayar tayi saboda Tunda ta tafi idonsa na kanta har ta dawo, Tana bashi ta juya da niyyar tafiya amma ya riko hannunta tareda Kara wayar a kunnensa Bayan ya mata masauki kan cinyarsa wanda ya bata damar jin dukkan abinda Anty Mariya take fada

Ya zancen Zuwan naka yobe gobe, ko 'yar lelen taka ta hanaka?

Haba yaya, sau nawa zamui maganar nan dake nace muku zanje, sannan Dan Allah Anty ki daina saka A'isha cikin wannan maganar she knows nothing

Kallonshi A'isha tayi tana pleading da idonta Don shi baisan hakan da yayi kara mata bakin jini yake gurinsu ba akan wanda take dashi, Yi yayi kamar bai gane abinda take nufi ba ya cigaba da sauraron bambamin Anty mariya

...nidai na fada maka, duk fushin ka da Kare matarka da Kake Rufaida kamar ta shigo ta gama, muma mu fara jin kukan jarirai ba, ba ka shigo gida kamas babu 'ya'ya ba

Tabbas Anty Mariya taci darajar zamanta yayarsa amma Wallahi da wata ce se ya nuna mata iyakarta, bai ce mata komai ba ya kashe wayar tare da jefar da ita saman table din gabansu sannan ya dafe kansa jin yadda yake Sara masa tareda barazanar tsagewa, shi baya fada amma idan Yana son Abu baya son mutane suna kushe shi tun yana yaro yake da wannan dabo'ar sunsha fada da yaya Nuzla akan ta kushe Abinda yake so a times se hajja ta shiga maganar yake hakura, to me A'isha tayi musu suke mata wannan kin? Haihuwa shi zata haifawa to baya so why are they criticizing?

A hankali ta cire hannayensa daya dafe kansa, dago idonshi yayi da suka Fara canza launi ya sauke kanta, murmushi take masa wanda yake burgeshi har Seda hakorin makanta dake right side cikin jerin hakoranta ya samu lekowa

Sweetie, nasan these days things are hard for you am so sorry idan ina kara maka wata pressure din, inason duk Abinda su Anty sukace kayi to kayi indai be Saba shari'a ba Koda hakan zai bata mini rai, bin bayana da Kake da nuna musu ni wata ce a gurinka Shiyasa suke Kara tsana ta....

Me kike so ayi?  Na kyallesu suna wulakanta abinda nake so? Shatuuu I can't stand any person da baya sonki other than hajiya

Ai kuwa bazasu taba daina tsangwamma ta ba matsawar Xaka nuna bacin rai idan sun min ko sun fadi Abu a kaina.

Baice komai ba ya janyo abincin dake cikin plate ya debo a spoon ya kai mata, kin bude bakinta tayi hakan yasa yace

Kina son Nayi miki dure?

Kanta ta girgixa, hakan yasa yace

Open up

Bude bakin tayi ya shiga feeding dinta har ta koshi sannan suka danyi kallo a arewa24 kafin suka tafi suka kwanta.

Da asuba tare sukai sallar isha'i, bacci Muhammad yakeji saboda Daren jiya was awesome and perfect A'ishansa is beyond yayi bayanin ta, Shiyasa ba suyi bacci da wuri ba

Me za kayi haka?

A'isha ta fada astonished

Baby bacci nake ji, Dan Allah allow me

Muhammad ya fada Yana jan bargo tareda rufe jikinsa, Hawa gadon tayi tace tana yaye bargon

No way! Sakko Kaje kayi wanka kaida zakayi tafiya ina kaga idon bacci

Shiru yayi mata yana runtse idonshi dukda yasan karya yake yace zaiyi bacci, ganin abinda yake yasa A'isha fara mishi cakulkulu, bude idonshi yayi Yana dariya tare da fadin

OK Kinyi winning bari Naje Nayi wankan se Inyi baccin ko

Tana dariya ta harareshi tare da dage kafadarta Irin ko a jikina, murmushi yayi ya wuce toilet Yana jin sonta da kimarta na nunkuwa a zuciyarshi, ita kam banda ambaton Allah babu Abinda take saboda yadda take jin zuciyarta na azalzalarta, haka ta gyara gadon ta fito masa da short da vest sannan ta wuce kitchen inda ta Fara soya Banana pancake din data kwaba Tun dazu, Tana Yi tana sauraren wani wa'azi na favourite scholar dinta Mufti menk akan marriage, tanayi tana azhkar din safe hakan ya saukar mata wata nutsuwa har taji zuciyarta ta Daidaita, ji tayi an rungumo ta ta baya, tasan Muhammad ne hakan yasa ta kwantar da kanta tana lumshe idonta tana jin daddadan kamshin turaren sa,

Zai kone

Haka taji Muhammad ya fada, hakan yasa ta bude idonta tare da saurin cire abin Daga frying pan din, kashe gas din tayi ta jera cikin foil paper tare da zuba chocolate akai da skittles akai, soup din kaza ta zuba musu cikin bowl tace

Muje muci Karka makara

Suna gamawa suka nufi daki inda ta fito masa da light brown kufta me coffee royal embroidery design dinnan, tare suka saka kayan ta dakko wani Arabian turare ta feshe mishi jikinsa dashi, ta kawo coffee hula ta zanna bukar ta kafa masa akai tare da daura masa agogo me coffee fata take yayi wani kyau na mussaman Wanda ya haifar mata da wani Irin kishi daya taso mata, amma take ta fara ambaton sunan Allah, wayarta kirar infinix hot6 ta dakko ta haska habibinta, tare suka fito Yana waya da Salis dake masa korafin zasu iya makara, hakuri ya bashi akan Yana hanya.

Wannan pancakes din ta bashi tace

Kaci a hanya Kada ka barmin kanka da yunwa

Fuskanta ya shafo tareda pecking forehead dinta yace

I love you

Love you more

A haka ya isa bakin motar ta don Dama yace da ita zai tafi, ta bude masa ya shiga sannan ta rufo masa kofar tareda Fara karanto masa adduar matafiyi shi kuma yana maimaitawa har suka gama sannan tayi kissing hannunshi dake cikin nata tace

Allah ya tsare, no careless driving less overtaking OK?

Kanshi yayi nodding yace

As you said darling

Sakin hannunshi tayi tace

Ka gaida *RUFAIDA*

Shatuuu ♥️

GIDAJEN MU Where stories live. Discover now