Tunda Muhammad ya turo kofar parlour gidan ya fara jiyo Sautin qura'ani kira'ar maher mu'aqilee cikin suratul Isra (I knew many will say shatuuu kullum maher, guys ina sonshi ne, I want to meet him face to face, I wants to hear him giving me that advice on how to carry myself to jannah, pray for me lemme meet him it's my ambition) Ke tashi, wannan ya zama sabonta Tunda yayi mata zancen aurenshi kullum tana cikin jin karatun qurani.Bata cikin parlour sede hancinsa ya fara jiyo masa wani Irin aroma na girki, A'isha Issa cook, Tana son girki hatta leisure time dinta idan bata girki a kitchen to she's reading on new recipes, abincinta always taste different, ta iya girki ne kamar duka energy dinta akanshi yake karewa.
Kitchen din ya nufa, Tana tsaye cikin beige color gown me stones, kanta hula ce wadda ta bawa jelar kitson ta damar Lekowa, fuskarta babu wata walwala kamar yadda yanxu ya zama sabonta, it's been long yaga dariyarta, ya manta last da tayi masa simple murmushi, gidan duk babu dadi dukkansu sun rame saboda yadda A'isha ke azabtar da zuciyoyinsu, wannan smiles din duka babu ta mayar da gidan massallaci saboda yadda ta maida jin karatun qurani komai nata ko hira basui, abinci kadai suke ci tare shima shiru se Jefijefi sukanyi magana
Sannu da zuwa
A'isha ta fada Tana juye abinci cikin warmers
Yawwa baby, ya office da lecture
Aje wukar hannunta tayi cikin sink tace
It was fine Alhmdllh, why not go for a quick shower kafin maghrib tayi?
Cikin jin dadi yace
Whatever the princess wishes that will be my command
Yana fadin haka ya fice Zuwa daki, kanta ta dafe tana jin wani Irin kunci cikin zuciyarta, Allah kadai yasan yadda take Kwana cikin kowanne dare idan ta tuna her man is about to take a new wife, hawayen dake bin kuncinta ta goge, tun tana karama tasan ita mutum ce me tsananin kishi, Tana da kishi ko cikin sisters dinta bata son a fifita su akanta, amma dayake she's d reserved type bazaka gane ba. A'isha na da passion sosae akan girki kullum cikin trying sabon abu take saboda tana ganin girki shi ne priority a gidan aure, hakan yasa ta zama expert baa girki kawai ba hatta wasu abubuwan A'isha ba tada damuwa Akansu. Ita yanzu matsalarta daya ce Auren da Muhammad zaiyi, wa zai aura? What if idan tazo ta haihu shi kenan ta tabbata barren kamar yadda yan uwansa suke kiranta.
Shiru babu Abinda Ke tashi se karar spoons dinsu, kowa zuciyarsa babu dadi har suka kammalla cin abincin, kwashe kayan tayi ta Kai kitchen daga can ta wuce bedroom dinta ta zauna kan sofa dake facing gadonta, system dinta ta janyo ta Fara typing da alama lecture note take hadawa, turo kofar taji anyi dukda tasan Muhammad ne amma seda ta dago, har ya canza kaya zuwa nighties dinsa farare masu layi layin Brown, hannunsa rike da mug wanda ta tabbatar coffee ne ko kuma madara, dauke kanta tayi tana jin wani son sa na sake tsirga mata amma haushin shi take ji. Gefen gadon ya zauna tareda switching TV din dake dakin bai ce mata uffan ba, sun fi awa zaune sannan ta mike ta rufe system din ta shiga toilet ba jimawa ta fito daure da towel wanda ya tabbatar masa wanka tayi, bai fita ba se binta da ido da yake, riga ta samu iya gwiwarta ta saka sannan ta daura hula kanta tare da feshe jikinta da turare, kan gadon ta kwanta ta Fara addu'a ganin haka yasa Muhammad ficewa da cup din, bayan kamar 7minutes ya dawo, wutar ya kashe sannan ya zauna tareda jinginar da bayansa kan pillow din dake gadon, hannunsa yasa ya janyo A'isha jikinsa, ture hannun tayi ta matsa gefe idonta a runtse,
It will over a darennan
Ya fada cikin ransa tare da sake kamo ta zuwa jikinsa, sake tureshi tayi amma ya riga da yasa mata karfi, bugunshi ta dinga Yi tun karfinta tare da sakin kuka hannunsa yasa ya kama hannayenta yace
Come on A'isha stop this, me kike nufi da rayuwarmu ne? Kin dena min magana kulkum cikin kunci kike ya kike so Nayi, kin sani aurennan da zanyi baa son raina ba kawai babu yadda zanyi ne, understand me mana.
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️