28

1.4K 190 2
                                    


Innnalillahil wa Inna ilahil rajiun! Youth muna ganin kamar tsofaffi ne suke mutuwa Wallahi muma muna mutuwa, on Saturday anyi rasuwa wadda ta girgixa ni, I was devastated, shattered su biyar they were friends and they died in a car accident. Fear Allah wherever you find yourself death await each and everyone of us, we will surely leave this sweet dunya one day , so let's strive hard and do something good that will make us be part of jannah one day. I love you guys ♥️


Bayan watanni biyar

Wata matashiyar budurwa ce cikin uniform na Boko wanda suka sha wanki kuma sike a goge tas se kari a jikinsu, dukda yanayin rana da ake a garin saboda hadarin dake kwance sararin samaniya sede bai Kai ga tasowa ba, cikin gajiya Lubabatu take tahowa zuwa gida daga makaranta, fuskarnan cike take da anuri, Tunda aka sallameta wata daya da suka wuce ta komo gida cikeda nasarar aikin da akayi ta ke jinta tamkar sabuwar halitta, Tana jin kamar sake ta akai batada wata damuwa, karatunta take babu bata Lokaci ko wasa so takeyi ta zama wata saboda Watarana ta bada labarin kanta.

Da sallama ta shiga cikin gidan inda Innarta Ke ta kai kawo daga daki zuwa inda aka tanada Dan yin girki, da fara'a take fadin

Inna barka da gida

Itama Inna da murmushi tace

Sannunki da Zuwa, ya makarantar?

Yatsina fuska tayi tace

Lapiya lau, su idris sun tafi makaranta ne
.kanta ta gyada hakan yasa itama ta wuce Don cire kayanta, ruwa ta hada ta shiga bayi tayi wanka Dama ita ba wai tana dadewa bane, cikin Mintina ta fito ta fara shirinta. Cikin wani yadi wanda Yadan Fara kodewa kuma yayi mata cif jikinta saboda kivar da tadan sakeyi, Inna dake zaune ta kalleta murna da godiyar Allah kullum saboda yadda rayuwar ta ta gyaru baki daya wannan tashin hnkli da bakin ciki da tazo dashi yanxu babu, Allah yasa Rayuwarta ta iganta, sunanan zaune har Bayan La'asar se hira suke abinsu, sunayi Luba ta tashi ta dora tuwan dare, tanayi cikin kwanciyar hankali se jin sallama sukai daga zaure, tare suka amsa Luba tace

Shigo mana

Aikuwa sega sister Farida cikin shiga ta alfarma, tayi kyau kana ganinta kaga wadda Hutu da jin dadi suka samu gurin zama, wani tsalle Luba ta buga ta nufeta tana fadin

Anty oyoyo

Rungume juna sukai yayinda Inna ta shiga ciki ta dakko tabarma ta shimfida tareda fadin

Ke Lubabatu sake ta Taxo ta zauna

Dariya sister Farida tayi ta kamo hannun Luba suka zauna, gaisawa suka fara yi nan Luba ta leka aka siyo mata pure water wani shago gefen gidan mota ta gani da wani azababben guy zaune saman motar hannunsa rike da waya Yana danne danne, gayen ya hadu babu lie, take ta kauda wannan tunanin daga zuciyar ta don Tana ganin babu wata alaka DA ta rage tsakaninta da 'da namiji, bawai ta tsane su bane a'a tasan basuda adalci, Abinda sani yayi mata shi ne last thing da take expecting daga gurinshi, ciki ta koma ko kafin ta zauna sega Malam Mamuda ya shigo da sallama ganin Farida Zaune yasa ya kara fadada murmushin shi tareda fadin

Ikon Allah likita ce yau a GIDANMU? Sannunku da zuwa

Yawwa Malam, ya me jiki?

Jiki yayi Sauqi har ta koma makaranta, ko Kece kika xo da bako a kofar gida

Kanta ta gyada tace

Yaron guri nane Ja'afar, dama gurinka naxo

Bari na shigo dashi Se muyi maganar

Bai jira cewarta ba yayi waje inda ya shigo da Ja'afar yace

Bari na Kira Baba

Fita yayi yayinda Ja'afar ya gaida Inna sannan Luba dake zaune ta gaesheshi, idonshi ya tsura mata Don yana son tuna inda ya santa, confirm ya taba ganinta wani gurin but he can't recall, haka nan ya amsa tareda maida kansa kan wayar shi, a haka kakar Luba Taxo suka gaisa cikin mutunta juna tana ta zolayar Ja'afar dayake shima dan hau ne ya biyeta, seda suka gama kafin sister Farida tace

GIDAJEN MU Onde histórias criam vida. Descubra agora