06

1.7K 221 5
                                    

Da sallama Bilal ya shigo cikin parlour, Fatima bata ciki se yaranta dake zaune duka fuskokinsu babu walwala, ko ina kacakaca wannan ya tabbatar masa Batayi Shara ba, yaran na jin muryarsa suka taho a guje suna fadin

Oyoyo Abhi

Shima fuskarsa da walwala ya dauki juwaira ya cilla sama, ai kuwa ta saki dariya, aje ta yayi Yana shafa kansu jawad yana fadin

My boys ya akai?

Jalal ne yace

Abhi yunwa muke ji, Umma bata bamu abinci ba Tunda muka dawo Daga school

Take yaji ranshi ya baci ya rasa dalilin da yasa Fatima take mishi haka,

Ku zauna, ina Umman taku?

Jawad yace

Tana bedroom dinta

Baice komai ba ya nufi kofar dakinta, a hankali ya tura kofar ya shiga, Tana zaune kan gado can karshe , dakin wani Irin karni yake na mop din da bai samun kulawa, kofofin wardrobe din duka a bude suke ga kaya sun turo kansu suna jiran a tabasu su zubo.

Zama yayi gefen gadon Yana kallonta, fuskarta ta kumbura wanda ya tabbatar masa kuka tayi, jikinta bakar abaya ce me multi colored stones, ko wanne Hali Fatima take ciki bazaka taba ganinta babu wanka ko kwaliyya ba amma gidanta, yaranta will tell you who she is.

Tee

Bilal ya kira sunanta a sanyaye saboda ganin kumburin da fuskarta yayi yake ganin bai kyauta ba, amma he can't help he wants her change ko yaya ne,

Tee magana nake miki

Na jika ai, zaka iya fadar abinda Ke tafe da kai

Kansa ya girgixa yace

Tee you shouting on me?

Harara ta watsa masa tace

Kadan ka gani matsawar bakayi gaggawar janye batun aurenka ba.

Murmushi yayi wanda ya sake hasala ta yace

Haba Tee da girmana ince na fasa, a'a kinga yara baki basu abinci ba....

Ban dafa ba, kuma ba zanyi ba wadda kakeson aura tazo ta dafa musu.

Baice komai ba ya mike ya fice yana jin kukanta, dakinsa Yaje ya watsa ruwa ya nufi kitchen ya hadawa yaran cereals, suna ta murna suka sha yasan bazasu koshi ba hakan yasa ya daukesu sukaje wani eatery sukaci.

Karba wannan jawad ka kaiwa Ummanku

Karbar takeaway din yayi ya nufi dakin Fatima, Tana kan sallaya da dukkan alamu sallar ishai ta Idar

Umma gashi inji Abhi

Fita ka mayar masa duk wanda ya Kara shigo min daki se naci ubansa

Ko kafin ta karasa jawad ya fice saboda azabar tsoronta da suke, Fatima babu sauki babu wasa.

Abhi Tace na dawo maka da abincin

Dago kansa yayi Daga system din da yake aiki dashi yace

Jeka ka aje cikin fridge, sannan kuje ku kwanta

Jawad yaje yakai sannan suka tafi Dakinsu shi da jalal bayan Bilal ya sake jadadda musu Kan yin Alwala da addu'a kafin su kwanta.

Wayarsa na rike a hannunsa yaji an fisge wayar, dago idanunsa yayi ya aje Kan fuskarta, Tana tsaye ta zuba mishi ido, dauke kanshi yayi ya cigaba da Abinda yake saboda bashida lokacin ta.

Washegari ko kofar bedroom dinta bata leko bata leko ba, yaran sukai wanka ya dimama musu abincin da taki ci sukaci sannan suka tafi school, dakinta ya kai mata kudin cefane ya dauki wayarsa dake Kan bedside drawer dinta ya fice yana sake ganin wautar Fatima.

GIDAJEN MU Where stories live. Discover now