10

1.5K 179 1
                                    

Iska ce ke kadawa a hankali cikin garin na Kano kuma sassan Farawa layout, tun asuba Latifa da ta tashi bata koma bacci ba saboda yau ne ranar entrance examination na Gateway academy, Amal ce ta fara wanka sannan Nana kafin Latifa tayi itada Mimi cikin dakinta, Seda ta hadawa barrister abincinsa tsaf sannan ta dafa masa white rice saboda rana.

Tsaf ta kammalla komai karfe bakwai, Don Tara na safe Za'a Fara test din shi yasa take Son su tafi da wuri, dakin barrister taje, Yana zaune kan gado hannunsa rike da wayarsa yana danne danne, sallama tayi masa wanda yasa ya dago idonsa ya zube kanta cikin voile lace take milk da coffee dinkin plain zani da riga, fuskarta powder ce kawai se lip balm Amma Duk da haka tayi kyau, zama tayi bayan ta aje tray din dake hannunta Kan bedside drawer tace

Ashe ka tashi, ina Kwana

Ajiye wayar yayi yace

Lapiya lau, kun gama shiryawa

Kanta ta gyada tace

Eh, tafiya Zamuyi

Mikewa yayi ya dakko kudi as usual ya kama hannunta yace

Allah ya kiyaye, drive carefully?

A'a rakiya kuma fa?

Amma Kinsan I've something to do, ko katsewa zanyi na rakaku kamar baki

Haba barrister am very sure munfi abinda kake yi muhimmanci , I hate it when you give some silly abubuwa full attention dinka amma mu ko a jikinka

Latifa ni kike addressing haka? Daily trust ce silly

What about daily trust? Compared to me they're silly of no use

Raini ya shiga tsakani na dake kenan? Yaushe muka Fara yar wasa dake?

No yaya Nasir babu zancen raini, ni matar ka ce idan baka sakar min fuska kayi wasa damu ba dawa zakai? We're your family nasha tambayarka idan laifi nayi maka kayi hakuri amma ko daya kaki canzawa am tired, I want this to work, ka canxa kamar normal mutane
   Bai ce mata komai Illa ci gaba da ayyukansa dayayi, sosae halayen barrister ke bata mamaki, handbag dinta ta dauka ta fice ba tareda ta dauki kudin da ya aje mata ba. A parlor ta samu su Amal suna jiranta, kallonsu tayi ta kirkiro murmushi Don taga dukkansu sun tsare ta da ido tace

Let's go

Tare suka Mike suka bi bayanta, Seda tayi addu'a kafin ta tada motar Mai gadi ya bude musu gate suka Kama hanya.  Awa biyu  suka isa cikin dutse, ta shuwarin tabi cikin Abubakar Rimi housing estate anan Gateway take. Mutane ne da yawa ana ta screening thank God ba'a fara Don tayi tunanin se sun makara at least tayi beating time. Karfe goma suka shiga venue din exams din, Latifa Seda ta karba number wata invigilator wadda ta tabbatar staff ce a school din saboda wani tag dake makale jikin abayar ta.

A kofar gidan A'isha dake G9 quarters Latifa tayi parking Bayan ta tabbatar Tana nan daga gurin gate man dinsu. A'isha na bedroom dinta cikin shigarta ta kullum wato Abaya sea green da jajayen stones , kanta jan karamin veil ne ta daura, kitson kanta sun zubo bayanta se medical glasses dake idonta, dukda babu komai fuskarta tayi kyau sede ta rame, idanunta sunyi xuruxuru kamar wadda tayi diarrhea gaba daya ta lalace saboda yadda tasa zancen auren Muhammad a ranta, Shiyasa kana kallonta kasan bata cikin nitsuwanta kuma akwai damuwa a tattare da ita. Gabanta system dinta ce wadda ta zame mata kawa kuma abokiyar hira saboda Muhammad baya zama kuma Koda Yana nan tana jinsa kamar wani stranger shi yasa ta maida dakinta gurin zamanta.

Knocking taji jikin kofar hakan yasa ta Mike Don tasan Muhammad ne, lock din ta cire, shi ne kua cikin jallabiya baka me gajeren hannu shima ya rame kamar A'isha Sede shi yayi baki, kallon fuskarta yayi yace

Kinyi baki a parlour

Bai kuma cewa komai ba ya nufi dakinsa, ba tare da ta koma dakin ba ta nufi parlour, ganin Latifa Zaune da yaranta yasa ta tafi da sauri ta rungume Latifa tana fadin

Lateey ashe zaki zo

Itama cikin murna tace

Gani dai na cika alkawari nazo dutse

Sakinta tayi ta rungume su Mimi tana amsa gaisuwar su tare da shafa kansu, kitchen taje ta kawo musu abin tabawa, kafin kuma suka Fara hira har Muhammad ya fito shima ya zauna akai hirar dashi dukda faking kawai suke. Wajen 12pm A'isha ta shiga kitchen ya rage daga Latifa se Muhammad, Wanda so yake yayi maganar da Latifa amma ya rasa ta inda zai fara, ana haka wannan malamar ta kira ta akan an kammalla exams din, mikewa tayi ta dauki key tana fadin

Bari na dakko Amal sun gama exams din

A'a ki Bari Naje na dakko ta kawae, bani digits din malamar

Muhammad ya fada, take ta bashi number sannan ya fada mawa A'isha dake kitchen ya fice daga gidan. Bayan sun gama cin abinci Muhammad ya dauki yaran suka tafi yawo Don bawa su A'isha space Don yasan magana zasui.

    Latifa ce ta Fara fadin

A'isha me yake damunku ne? Daga ke har Muhammad din gaba daya kun rame

Dan murmushi A'isha tayi tace

Lateey, Muhammad aure zaiyi

Aure?

Latifa ta fada sounding amaze da idanuwa a warwaje

Da gaske nake Lateey, abinda Ke damun mu kenan, Lateey ni na daurawa kaina rashin haihuwa, idan asan raina ne zan ki haihuwa ne? Lateey they're putting pressure, Tun hajiyanshi na Zuwa tayi min wulakanci itada yan uwanshi har kuma Taxo Tace wai yayi aure

Shiru Latifa tayi tana sauraren A'isha, Seda ta gama tace

A'isha kun taba Zuwa Asibiti kuwa?

Kanta ta girgixa tace

Engineer yaki yarda yace wai shiga gonar Allah ne, to ya zanyi dashi

A'a babu wannan maganar, dole kuje Asibiti what if infection ne yake cinku Baku sani ba,

To ya zanyi Lateey? Bansan yadda zanyi ba

Ki Bari yanxu Tunda zancen aurenan ya kankama to mu bari se yayi tukun zanzo mui magana dashi, amma A'isha yanzu Abinda nake so dake nasan Ke kadai kika san halin da kike ciki, to Amma a wannan stage din hakuri shi ne komai, Kiyi hkri ki rungumi mijinki saboda nasan babu fashi a aurenann,

Hawayen dake bin kuncinta ta goge tace

Lateey thank you, amma Wallahi bana son ganin Muhammad yanxu ashe akwai ranar da zai iya sake aure

Dan murmushi Latifa tayi tace

Shedan ne, Kiyi hkri ki kwantar da hankalinki ki rike mijinki, Ke Kinyi Saar miji kuma Kinsan kin gina kanki none will ever take your place a gurinshi, Bayan Kinsan auren ma hadi ne Meye xaki damu kanki.

Haka suka dinga taba hira mostly Kan matsalar A'isha, duka shawarwarin daya dace shi Latifa ta fada mata. Bayan La'asar Muhammad ya dawo da yaran haka suka nufi Kano Cikeda kewar juna.

Muhammad na daki A'isha ta shigo ta sake wani wankan cikin purple abaya light da golden ado, golden veil ta saka sannan ta dan shafa powder da lips dinta maroon wanda ya haska ta, Yana kwance da wayarsa a hannu da alama browsing wani abin yake, kamshin turaren ta ne ya fara dokar hancinsa wanda yasa shi juyowa tare da sakin wani lallausan murmushi, itama murmushin ta sakar masa tace tana zama gefenshi

Sweerie

Baby, Kiyi hkri

No lemme apologize, am sorry engineer

Janyota yayi yace

No baby Karki damu, Kinsan bana son aurennan hajiya insisted akan se nayi amma Nayi miki alkawarin bazan taba juya miki baya ba no matter d hardship.

Wannan ranar was beyond words a gurin Muhammad da A'isha yau kam sun sasanta kansu, dukda A'isha tana jin uneasiness idan ta tuna Auren Muhammad, amma tuna maganganun Latifa se ya fado mata hakan yasa take jin babu komai kawai.

Shatuuu






Am very sorry for the late update, many things came that are inevitable, but always bear in mind that Aeeeysha loves you much ♥️♥️♥️

GIDAJEN MU Where stories live. Discover now