Akwai amare da yawa cikin duniyarnan, kowacce mace da yadda take ranar bikinta, bangaren Rufaida kam opposite din sauran ce, Tunda aka fara hada Hadar biki take kuka, kuka kuwa ba na wasa ba gashi taki cewa uffan idan kana mata magana sede ta dinga binka da ido kamar taga aliens, mahaifiyarta ta shiga tsananin damuwa yayinda Alhaji Aliyu ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa, cewa yayi ko gawarta ce se yakai gidan Muhammad daga baya ayi jana'ixa. 'yan uwan Mamanta kadai ke bin bayanta a haka dai aka gama biki babu wani armashi, ana daura aure aka taho da ita Dutse wanda take jin tamkar kabarinta Za'a kaita, da wanne idon zata kalli Anty A'isha?Acan dutse rigima sosae akayi da Muhammad da yaya Maryam akan sabon gidan da ya gina, gidan kasa da sama ne kuma Muhammad da sunan A'isha yayi upstairs Don yace shi bazai iya barin A'isha a kasa ba, Maryam kuwa tayi tsalle ta dire Tace Se an kwashe kayan A'isha don already an gama saka komai. Shi kuma Muhammad yace Allah ya kasheshi idan Rufaida ta zauna a sama, haka aka dinga Yi har hajja gana taji maganar, wannan karan Bayan Muhammad tabi Tace
Ke Maryam ki fita a idona na rufe Bana son shiga ahinda babu ruwanka, matarki ce ko tashi ko kuma zaki tsara masa yadda zai tafiyar da rayuwar shi da gidanshi?
Ai kuwa ran Maryam ya baci sosae, amma kuma an samawa Muhammad lapiya, ita Nuzla Tunda Taxo gidan A'isha ta sauka ta dinga kwantar mata da hankali, ga Latifa itama tazo ta yini sanann ta koma Don ta cewa A'isha Kar tayi wani taro saboda mutane gulma kawai zasu zo yi.
Se yamma su Rufaida suka iso dutse itada danginta, ganin yamma tayi sosae yasa aka barta Zuwa Washegari a rakota, dukda A'isha tare da Muhammad suka Kwana Amma Kwana tayi hankalinta a tashe, bacci barawo ne ya dauke ta.
Washegari bayan sunyi breakfast, Muhammad ya dubi A'isha yace
Baby
Dago idonta tayi ta sauke Kan Fuskarshi wadda ya tsura mata ido, hannunshi ya bude mata alamun tazo gareshi, babu musu ta fada jikinshi, kanta ya shafa yace
A'isha Kiyi hkri, nasan Kinyi amma inason ki Kara akan wanda kikeyi da, da zamanmu muke lapiya a sirrance Amma yanzu mun samu third party kinga idon kowa ya dawo kanmu kenan, inason kim kwantar da hankalinki ki nutsu hakan zaisa nayi adalci a tsakaninku, wasu abubuwan dole zasu canza amma inason Wannan fahimtar da kike min kullum ki Kara min ita, ki sani no matter what happened, what life be no matter the problems we face, the hardships and thorns Muhammad Yana sonki ke kadai saboda ban taba mafarkin akwai ranar da zan miki kishiya ba to babu yadda zanyi rabo ya riga ya rantse. Idan kikayi min haka A'isha kin gama min komai
Ko ka fada ko kayi shiru sweetie nasan kana sona, Inshaaa Allah I'll never let you down nima ina sonka
A'isha ta fada tana kuka, sosae ya sake rungumeta tare da fadin
Shhhhhh, you've cried enough kinji, ki zama jaruma ki jajirce kar ki Kara kuka, Da zarar mun nutsu Zamu tafi asibiti and am so sorry da tuntuni bamu je check up ba, saboda banyi tunanin haka abin zai zama ba, Allah knows best.
Haka yayi ta lallashinta har ta daina kukan sannan yace
Da La'asar zasu zo Bari Naje mu gaisa
Kanta ta gyada ta dakko masa shadda milk me aikin coffee wadda da kanta ta danka masa, har bakin mota ta rakashi sannan ta dawo Don daura abinci Tunda ya Nuzla tace ta danyi abinci ko yaya ne, yaran mamu ne suka taya ta aikin, basu tafi ba seda suka gyara ko ina sannan suka sakko kasa, anan sukaci Karo da 'yan uwan Rufaida wanda zasu koma yobe sunzo ganin gida, Anty Mariya tace
Ke koma kira Matar gidan, ai da ganagan ya bata key se kace nata
Hamida ce ta juya ta kira A'isha, hijabi ta saka ta sakko kasa, gaba dayansu kallonta suke, gaishesu tayi sannan Mariya tace
Tsayawar me kike? Dallah wuce ki kawo mana key, juya kawai
.idan da sabo A'isha ta Saba, juyawa tayi tana jin wata tana fadin
Mariya Meye haka, ta hana kanta haihuwa ne? Idan....
Daga nan ta daina juyo muryar su, seda ta dakko sannan ta kawo musu, suna tayi mata sannu ta wuce, ruwa da abinci ta kawo musu nanma Mariya cewa tayi
To uwar makairai sunce yunwa suke ji
Wadda tayi magana dazu wadda Itace yayar hajiyan Muhammad ta kuma fadin
Mun gode A'isha Allah yayi miki albarka ya hada kanku, ke kuma Mariya Bana son haka ina laifin wanda ya kula ku shashasha kawai
Daga nan Mariya Bata kuma cewa komai ba har suka tafi, Dab da La'asar ta sake wanka tayi kwaliyya daidai misali Bayan ta kure karatun qurani Don zuciyar ta ta lafa Daga gobarar da ake, wani lace ta dakko fari tas me kyau Wanda Mamanta ta kawo mata lokacinda taje Dubai, amma bata taba amfani dashi ba se shekaranjiya aka kawo shi daga dinki, jajayen accessories ta saka tayi kyau kamar ba gobe, gashi idan ka kalleta she's fit bazaka ce Tana da damuwa ba, turaren wuta tasa Sega cousins dinta biyu da yaya Nuzla, su suka gyara gidan tareda Kara gyara A'isha sannan suka zauna jiran zuwan su Rufaida.
Dammm taji gabanta ya fadi jin guda da ake yi babu kakautawa, manyan ne kawai suka hayo sama da Rufaida gurin A'isha, Tana lullube cikin lafaya me kyau da tsada, kalar army green da flowers lemon green a jiki, suna shigowa parlour ta kwace hannunta ta nufi A'isha da gudunta ta fada jikinta tare da sakin wani sabon kukan, rungumeta A'isha tayi a take taji komai ya wuce, sede tausayin Rufaida daya sake kamata, bubbuga bayanta tadinga yi, kowa shiru yayi Yana kallonsu, Mariya kamar tayi me amma babu dama Nuzla ta kalleta tayi murmushi batace komai ba, wadda ake fada akanta itama ta bada Kai.
Anty Kinyi fushi ko, walahil azim takura ni sukai, Kinsan bazan iya miki haka ba
Shafa kanta tayi tana jin kamar itama tayi kukan tace
Shhhhhh, ya isa banyi fushi ba, tashi ki zauna,.
Zama tayi yayinda wasu suka birgesu su Maryam se turo baki suke daga karshe suka koma part din Amarya. Nasiha akai musu Amma mirsisi taki barin A'isha lokacinda da Za'a maidata part dinta, se A'isha ce ta rakata.
Karfe takwas babu kowa se su biyu kacal cikin gidan kowacce a part dinta, har lokancin Rufaida kuka take, yayinda A'isha take hada questions cikin system dinta. Cikin farin yadi me kyau Muhammad ya shigo, sama ya fara hayowa ya samu A'isha a Zaune da system gabanta ga tumbler Cikeda watermelon smoothie se gwangwanin pringles da take ci, sallama yayi, Da mamaki ta dago don Batayi tunanin ganin shi a wannan lokacin, ba tareda ta amsa ba tace
Sweetie me kakeyi?
Zama yayi gefenta yace
Yunwa nake ji Tun breakfast din safe
Ko kulashi ba tayi ba tace
Ka tashi ka tafi engineer Karka jawo min magana
Baby am hungry fa nace miki
Whatever, zan kawo muku abinci yanxu amma ka tafi
Kiss yayi mata sannan ya fice, kasalalen murmushi tayi tace
I love you sweetheart
Kitchen taje ta sakko da wasu maroon da silver warmers inda ta Adana abincin da tayi bayan maghrib, a parlor kasa ta aje sannan ta kira Muhammad akan ta kawo abincin, tare suka fito da rufaida wadda har lokancin kukan take, Dakyar ya samu tadan daina Amma ta rame ga fuskarta tayi ja, zama sukayi kan 3 seater ya saka su tsakiya yayi musu nasiha sannan ya raba Kwana da duk wani abu daya kamata sannan suka ci abinci wanda A'isha ta tursasa Rufaida taci, suna gamawa tayi musu sallama zuciyar ta a cunkushe ga mugun race da zuciyar ta keyi, daki ta shiga ta kulle Bayan ta kashe wutar parlon da duk inda ya dace, karatun qurani ta kunna sannan ta shiga wanka, Tana fitowa ta zura kayan bacci ta hau gado, juyi ta dinga yi bata san bacci ya dauketa ba se asuba ta farka ta kashe wayar da karatun qurani ya Kwana yana yi.
Bangaren Amarya da Ango kuwa sunyi nafila rakaa biyu sannan kowa ya nufi dakinsa, Muhammad bacci yayi sosae dukda tunannin A'isha da yake, itakam Rufaida tana kwanciya bacci yayi gaba da ita. Acan gidan hajiya, Mariya tace ayi breakfast akai hajiya tace a'a Don tasan A'isha zata basu abinci kuma hakan ce ta kasance a gurinta sukai breakfast sannan ya bar gidan yayinda A'isha da Rufaida Ke hira suna kallon wani movie cikin MBC max.
Shatuuu ♥️
YOU ARE READING
GIDAJEN MU
General FictionGIDAJEN MU novel ne dazai yi duba akan problems din da muke fuskanta a gidajen mu cikin society dinmu, akan aure, cuttutuka and zamantakewar mu ta yau da kullum. Shatuuu♥️